← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 34

Sashe 34

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shigarta asibitin ne yasata fara dube dube amma bataga kowa ba dakun nan ta fara shiga ba kowa a dakin, wani daki ta hango dan karami dan gaka lekawa tayi nan idanunta suka sauka akan innarta tana cin abinci kai da gani dole akai mata, shiga dakin tayi batare da tayi sallama ba sai hawayen da yake bin fuskarta,ikram ne idanunsa suka sauka akan inaya kasa rike kansa yayi yace inaya ce fa wannan, take kowa ya juyo yana kallonta cike da mamaki da gudu inaya ta matso ta rungume mahaifiyar ta tana sa kuka,dikansu kuka suke ba wanda yayi kokarin hanasu, inna ce ta saketa tace inaya kalli yadda kikayi baki kalleki kara kankameta tayi kamar zata mai da ta ciki, bayan wasu mintuna inaya ce a zaune yayin da zubair,ikram,inam kowa hankalinsa na kanta, in'am ce ta tashi ta bude cooler ta debo mata abinci, tin kan ta bata inaya take binta da kallao tana hadiyar yawu,tana mikomata ta fara ci da sauri sauri kamar zata cinye har kwanon,kallonta ikram yayi ya goge hawayen dake fuskarsa, tashi yayi ya fita in'am ce ta bi bayansa, kallonsa tayi tace sai kabar kukan ko yayana dama nace maka zata dawo, juyowa yayi kawai ya rungume in'am cike da farin ciki, sai kuma suka koma dakin a lokacin har ta cinye tana ta lasar kwanon, inna ce tace ko a karo miki, in'am ba tare da tahi amsar ba ta karo mata abincin,ci tayi ta koshi ta fara kallon dakin, inna dai sai gashi ta warware tana ta surutu ganin haka ne yasa zubair sallamarta, dikansu suna zaune ana hira yayin da inaya gaba daya hankalinta na kan intisar da abin da tayi mata,jin sallama ne yasa su dagowa banda inaya,jin muryar da bazata taba mantawa bane yasata dagowa tana kallonta cike da mamaki, zubair ne ya nuna musu wani gado zama sukayi, alhaji sammani ne ya fara magana tare da gaisawa da mutanen wajen, inaya ce ta fara gaishe da su kowannen su amma inaua kau da kanta tayi.

Alhaji sammani ne ya dauko bayani sai kuma ya barwa intisar ta karasa dik da tanayi tana hawaye a fuskarta gaba daya dakin shiru kowa yayi yana mamakin hali na indo, inaya kam kuka kawai take kamar an aikota, intisar sai da ta gama basu labarin dik abinda ta sani a sannan ne kuma tace a yanzu haka mahaifiyata allah yayi mata rasuwa sakamakon bin bokayen da takeyi, inaya wata zabura tayi tace umma ta rasu intisar,inalillahi wa inna ilaihi rajiun gaba daya dakin suka furta, intisar sakkowa tayi ta tsugguna ta na bawa inaya hakuri, inaya dai ta hakura.haka aka tashi kowa na mamakin halin indo akan kawance kawai,a na sukayi wa mahaifin intisar da intisar gaisuwa. zubair ne bayan kowa ya watse ya kalleta yace intisar to yanzu kina sona ne ko kuwa, rufe fuskanta kawai tayi tabi sawun mahaifinta tana daga masa hannu...

Bayan kwana 10
Inaya ce zaune a kan kujera tana ta faman inna da surutu, tana bata labari inna ce tace inaya me yasa zakiwa intisar haka kin manta da ita din kawar kice, kallon gefe tayi tace nasan kawata ce amma kuma inna banason kawancen saboda irin abinda tayi min, amma kuma wulakanci bashi da dadi fa inaya, jiya da tazo ko kallonta bakiyi ba, sallama da akayi ce ta katse su,ikram ne ya shigo da in'am inna ce ta mike tare da cewa lale yau kace manyan baki nayi dariya dikansu sukayi suna masu shiga dakin,

Intisar ce ta shiga gidan su hafsat a tsaye ta ganta ta kunna famfo, tana jira ruwa ya isheta ta wanke kwanikan, kallonta hafsat tayi da murmushi tace aa intisar ce kuma yau a gidan namu kenan, ki shigo to aa kawai tace anan dai itama ta nemi yafiyarta tare da fada mata ansa ranar bikinta nan da sati biyu,hafsat tayi mamaki matuka da jin wannan labarin amma sai ta share..wayar tace tai kara ganin sunan mahaifinta yasa ta dagawa ta kara a kunne shikenan dad bara nazo, sallama tayiwa hafsat kawai ta wuce,..KAWANCEN MU
Writing and Story
Waleedah Muhammad

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
89&90
Khalifa ya fito sanye da manyan kaya shadda ce sabuwa kar, dining ya nufa ya zauna tare da ajiye jakarsa a dayar kujerar da ke gefensa,sai da ya fara gaishe da iyayen nasa sannan suka fara break ana ta hira, kallon kannan nasa yayi yace maza ku zo mu tafi na ajiye ku a makaran ta yau ina da meeting, tashi sukai suna wa mahaifiyar su da mahaifinsu bye suka wuce,hajiya ce ta kalli alhaji tace allah nagode maka da ka shiryamin shi alhamdulillah, murmushi dikansu sukayi..

Wani haddadden gida akai parking, karkuce wani gida ne aa gidan dai malam shehu ne amma kuma gida yayi matukar haduwa,alhaji sammani ne ya kalli intisar yace mata wanann gidan shine wanda kika ruguje,wato gidan su inaya da murna ta kankamesa tana mai zubar da hawayen farin ciki, tana ta zabga godiya daga nan suka wuce gida.

Inaya dai an tsayar da ranar aurenta da ikram yayin da in'am sai murna takeyi...hade bikin akayi da shi da na zubair rana daya aka mai da shi.i naya ce ta kalli inna tace inna wai yaushe zamuje dangin mahaifina, hawaye ne ya kawo wa inna sai kuma tace inaya yau zan fada miki gaskia, baki da wani dangi na mahaifinki ni kadai ce danginki kiyi hakuri shiru inaya tayi.

Alhaji sammani ne ya kalli inna tare da mika mata key yace wannan shine mukullin gidan ku amina sannan ina neman alfarma a wajen ki kallonsa tayi tace tame kuma dan allah zaki aureni shiru inna tayi jin maganar tasa wani iri,ganin tayi shiru ne yasashi fadin karki damu kinji kiyi tinani zan dawo,nan da jibi tashi yayi ya fice yayin da inna ta kalli mukullin..

Kofar gidan suka tsaya suna kallonsa inaya ce tace inna kalli yadda ya gyara mana gidan nan ya zama na 'YAN gayu ko dariya ina tayi tace allah ko budewa sukai tare da shiga 'YAN unguwa sai kallonsu suke suna tseguminsu,ciki suka shiga suna ta murna abinsu, inda ana inaya tai ta zubawa mahaifin intisar addua.

Intisar ce a dakin ita da hafsat a zaune inaya ce ta shigo ta kallesu ta ajiye masu ruwan, intisar ce tace inaya nagani har yanzu baki hakura, da idan kin hakura na tabbata bazaki na shareni ba, amma kinsan ba laifi na bane na baki hakuri amma inaya kinki hakura,hafsat tace inaya dan allah kiyi hakuri domon ni kaina shaida ce akan abinda ya faru da intisar,inaya ce tace nifa na hakura, kawai kawancen ne abarshi haka kinji intisar idan muka hadu ma gaisa kawai, hakan ma ya isa domin naga ishara a ta dalilin kawancen mu..

Rana bata karya a yaune aka daura auren ZUBAIR IBRAHIM DA KUMA INTISAR SAMMANI Abisa sadaki naira dubu 100 sai MUHAMMAD IKRAM MUHAMMAD DA INAYA MUKHTAR MUHAMMAD Bisa sadaki nai dubu 100,s ai dai fatan dorewar farin ciki....

A gefe daya kuma auren innar inaya aka daura da kuma mahaifin intisar cike da farin ciki suke,kowa fuskansa dauke da farin ciki,especially in'am da dama can take burin ganin yayanta yayi aure.

BAYAN SHEKARA 2
Shiga gidan ikram nai mai matukar daukar hankali kai da kaga gini kasan an kashe naira a zaune na tarar da iyalan 2 wato zubair da matarsa sai kuma inaya da ikram hira suke sosai,inaya ce ta dan kwabe fuska tare da furta papa juyowa ikram yayi yace ya dai, yausge zamuje Switzerland din nifa na matsu naga innata, da gudu aka shigo juyawa nai tare da kallon yaran mace ne da na miji, intisar ce ta kallesu tace wato ku indai kuka hadu bakwa ji ko,intisar ce ta karve zance kajita fa my cweet ni bance inason ganin dad ni ba sai ita,gaba dayan su dariya sukai,inaya ce tace ke iftihaj maza zo ku zauna wasan ya isa haka..

Dika dika anan na kawo karshe wannan littafin na KAwANCEN mu abinda na fada dai dai allah ya bani ladan abinda banyi dai dai allah ya yafemin nagode masoya na masu bibiya ta a koda yaushe,

Na sadaukar da shi a gareku iyayena ina alfahari da ku.😍💖

Bazan manta da kungiya ta ba ta king and queen writers association ina alfahari da ku..

Godiya ga Umar Atteh......

Alkalamin🖋️
Waleeda Muhammad
(Auntynmu ce😍)
Chapter 34 · 0% Book details