← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 34

Sashe 33

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsat ce ta shigo asibitin dai dai office din zubair ta tsaya, knocking tai ji tayi kawai ance come shiga tayi, a zaune ta tarar da shi da fara'a ya kalleta yace aa yau kice kawar masoyiya tace tazo, dan murmushi kawai tayi tare da gaishe sa amsawa yayi da fara'a, ya jikin innar inaya da sauki yace mata tare da fadin ai jikin nata ma kwanan nan ya fara sauki tinda alhamdulillah yanzu tana gane wanda yake amma kuma bata magana sosai, kullun cikin tinanin inaya, murmushi hafsat tayi tace amma fa ya kamata ka tambayi intisar kallonta yayai yace amma kuma me yasa, saboda tabbas nasan intisar tasan wani abu akan abinda ya faru,kai dai kawai ka tambaye ta amma shawara na baka, karka manta da irin abinda taiwa intisar a can baya, zubair shiru yayi yana nazari, can kuma ya kalleta, to ni zan tafi sai anjima fitowar ta tayi taja masa kofa, tana murmushin samun nasara...

Khalifa zaune yake akan sallah ba laifi yayi fari amma ba can ba, dan gaskia sai yanzu ya zama mutum, jin an bude dakin ne yasa shi kallon kofar, mahaifiyar sa ya gani dauke da tray dan murmushi yayi kawai yace aa mom ke ce, da shawa'a ta kalli dan nata ganin yanzu ya zama mutum mai hankali, ajiye tray din tayi tana murmushi gaisawa sukai, sai ya kalleta yace mommy har yanzu haka zan zauna a kulle dan allah ki fada wa dad na daina shaye shaye, bana sha'awar yi wallahi, kallonsa tayi tace nan ba da jimawa ba yarona kaci gaba da addua kaji, tashi kawai tayi tabar dakin..

Cikin hanzari ta fito daga ita sai veils da karamar jaka,motar tai wa key ta fita daga cikin gidan,wani mahaukacin gudu take sai da fita daga garin malumfashi sannan ta dau hanyar wani karamin kauye, dai dai bakin hanya tai parkinga ta karasa da kafarta,wani dan daki kawai naga ta shiga tare da zama, kallon ta bokan yayi yace mai kuma ya kawoki wajena yanzu hanifa, boka na kasance kwanakin nan ina yawan mafarkai akan na karya asirin da indo tai wa 'yar ta amma kuma amma me bokan ya katseta, ai karya asirin nan shi ne jin dadinki idan ba haka ba, bazaki taba cika burinki ba hanifa dan haka zan baki shawara, tin wuri ki karya sa ko ya zama shamaki tsakanin ki da burinki, hanifa gumi daya ke tsattsafo mata ne ta goge ta kalli boka tace, to dan allah ka karya sa wasu makudan kudade ta ajiye masa, tare da tashi tabar wajen, jikin mota na hangota ta rike kanta ta dan dade sai kuma naga taja tsaki ta shige motarta, yayin da boka ya babbake da dariya ya kuma kalli hanyar da ta nufa..tin a hanya hanifa take ganin wani irin duhu duhu ga wata mahaukaciyar dariya da take ji, badai ta tsaya ba ta ci gaba da tukin ta,can kuma sai taji kamar an daga motar ta ta sama tana lekawa take idanunta suka sarkafe da wami mahaukacin dodo, daya zaro baki ji tayi an saki motar ta fado gwajab, amma bata daina tukin ba ga wani hayaki da da take gani a hanyar ta ta, cikin gudun ne ta hango wani katon dutse mai tsini kasa tsayar da motar tayi, sai ji kake kattt motar ta bugu da dutsen, take motar ta kama da wuta yayin da hanifa take ihu tare da kira wadan su irin sunaye(allah ya kiyashe mu da aikin halaka) a haka har wutar ta cinye ta tsabb....bangare daya kuma indo na zaune akan kujera tana kallon jin dakin na girgiza yasa ta tsayawa kallon dik wani abu a dakin sai dai kaji tarrrr ya fashe har indai ya danganci glass,da gudu intisar ta fito tana ihu tare da rike indo, cikk suka tsaya ganin gidan yayi wani duhu intisar ji tayi bata ji indo ba dan haka tafiya take tana kiran umma sai ji kake kitt an bige ta ta fadi, indo a daki na hangota ana tambari da ita tare da fadin ke har kin isa, mu zaki karyawa asiri muna tsaka da yi miki aiki, to ki sani sai mun cire miki kafafu, tinda baki da mutunci, dama ance dan adam butulu ne, dan haka ki karbi hukunci shiru najiya biyo baya...KAWANCEN MU
Writing and Story
Waleedah Muhammad
AUNTYNNMU

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
85&86
Intisar tana farkawa taji kanta na sarawa a hankali ta fara kiran umma kinsan me ya faru ni na manta komai,jin bata amsa bane yasata mikewa a hankali amma wayam ba kowa,dakin ta ta shiga, a lokacin ne taja wata kara tana mai fitowa, anan ne sukai kicibis da zubair kallinta yayi yace ke kuma lafiya, umma ta ce, ita ce wuce ta yayi tare da shiga dakin ba abinda ya furta sai inalillahi wa inna ilaihi rajiun, ganin abin yayi kamar almara, dawowa kan kujera yayi ya zauna, kallonta yayi yace fadamin me ya faru, shiru tayi tace bazan iya tina komai ba dan yanzu na tashi daga bacci, waya ya dakko yayi dialing sai kuma yace bara naje na dawo to kawai tace tana ta share hawaye, wayar indo ta dauka ta fara dialing number dad yana dagawa yace matata ya akayi, jin shasshekar kukan inaya yasa shi tambayar ta lafiya, cikin kuka take furta dad umma ce ta mutu, what intisar da gaske kike ko da wasa, da gaske nake dad, ok gani nan yanzun nan kit ya kashe, intisar zama tayi tana tinanin halin data ga indo a ciki, kafafunta ne a zube sai kuma yankan da akayi mata a wuya, kuka take sai ga zubair ya dawo rasa abinda zai yi yayi yace intisar ya kike ganin za a yi domi tabbas, mahaifiyar ki ta rasu, ka jira dad dina haka kawai ta bashi amsa ya wuce yace to yanzu kije ki kira makota, idan yazo ki kirani saboda ana jira a asibiti zan yi theatre, wucewa yayi yayin da ta hada kai da gwiwa tana kuka..

Haka ta faru bayan kwana 3 ne a lokacin kowa ya watse, kasancewar indo ba wasu 'YAN uwa gareta ba, intisar na zaune tana tina nin taya akai mahaifiyar ta tai wannan mutuwar, ji kawai tayi tana son ganin sakonni wayar ta, whatsapp ta shiga ganin abin da ya tada mata hankali ne yasa ta kuka, a take ta tina da maganar inaya, wayarta ta ciro daga dakinta wadda sai da kyar da ganta, kira ta farayi sai tai kira 3 sannan aka daga cikin kuka tace kasaki inaya yanzu kaji, ok kawai yace sai kuma ta fashe da kuka, umma shikenan kin mutu ashe ba banza ba da kikai wannan mutuwar umma zan cci gaba da yi miki addua, amma ban san tsanar da kikewa inaya ba har takai haka, gashi har ansaki a hanyar bin bokaye kin mutu kuma akan hanyar su, inaya kiyi hakuri ki yafemin inaya, na tafaka babban kuskure, kuka ta fashe da shi sai kuma ta kara fadin tinda shi kikeso na aura zan aure shi umma dik wannan maganar da take dad na bayanta sai da tagama tsabb sai jin muryar tayi yace intisar fadamin me ya faru da sauri ta juyo,gyada mata kai kawai yayi ya zauna.

Zubair ne ya shigo ya kalli inna wani mugun tausayin ta yaji gaba daya ta rame, ta yi baki ga damuwa, ruwan dayake ya kare ya cire mata tare da mika mata abinci,banza tayi dashi sallamar ikram ce tasa ta dagowa cikin farin ciki ta kallesa tace ashe dai kunga inaya ta, fito min da ita mana tana ina, in'am ce ta karasa tare da rike ta tana kallonta, sai kuma tace inna kiyi hakuri amma zubair ne ya katseta yace inna kici abinci sai na kira miki inaya, murmushi tayi tace dan allah dagaske kake ko kasan banason karya ko, murmushi yayi da gani iya na saman lebe ne...

Inaya na kwance taga haske ya bayyana a wajen ganin wani mai dirkeken ciki tayi ya kalleta yace ke tashi ki tafi, cike da murna ta tashi sai kuma wata zuciyar ta raya mata kodai karya ne, watsar da wannan zancen tayi kawai taci gaba da murna da gudu ta fito a lokacin ana ta kiraye kirayen sallar la'asar, ganin unguwar tayi kamar bata taba zuwa ba, dan haka ganin wani mai nafef tayi take ta tsayar da shi ta shiga tana masa kwatance, a zuciyar ta tana godewa allah, kofar gidan su ta tsaya amma kuma taga a kulle, sai lokacin naga fuskanta baka kirin,da ita kamar gawayi ga wata rama da tayi, idanun nata sun shige loko,muje asibitin dake garin nan, bai ce mata komai ba kuwa ya wuce zuwa asibitin...

Hajiya ce ta kalli alhaji tace yakamata kuma ka fito da khalifa haka domin tabbas nasan yayi hankali kuma na tabbata bazai kara gigin shan wata kwaya ba ko wani abinda zai bugar dashi,alhaji ne ya kalleta yace nima dama nayi tinanin hakan, domin dik wasu abokansa sun gaji da kiran daga karshe kuma na karya sim din nasa hajiya ce tace kagani yanzu sai a bashi campany,mu fara ganin abinda kuma zai yi, shikenan alhaji ya fada tare da chanja zancen.KAWANCEN MU
Writing and Story
Waleedah Muhammad
AUNTYNNMU

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
87&88
Tabbas dad hakance ta faru,umma ta fara bin bokaye ita ta rabani da inaya ta sanya min tsanarta a cikin zuciyata,alhaji glass din fuskarsa ya cire ya goge hawayen da suka zubo masa, yace yanzu zaki iya kaini inda mahaifiyar inayar take, tinda nasan dik inda inaya take yanzu taje gida, gyada kai tayi yace mata to taso muje.
Chapter 33 · 0% Book details