← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 34

Sashe 26

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
59&60
Indo ce tsaye sai safa da marwa take a lokacin wata hamshakiyar hajiya tayi sallama juyowa tayi tana kallonta sai kuma ta zauna tare da furta hajiya Hanifa sai yanzu kenan, hajiya hanifa ce ta bata amsa eaa mana ai nayi kokari da nazo miki da sanyin safiya kalli fa agogo karfe 8 tashi indo tayi taja hannun hanifa zuwa can cikin dakinta...
Intisar ce a zaune tayi shiru sai kuma ta tashi tare da shiga bandaki bata dade ba ta fito..wasu riga da wando naga ta saka ash color daya daga cikin kayan data siyo, kallo daya zaka mata kasan tasha kyau dik da batai wani kwalliya ba powder kadai ta shafa abinta wani dan siririn mayafi ta dauka ta yana ta dauki jaka da takalmi..tana fitowa falon taji tsitt jin shirun ne yasa ta nufar falon indo, a zauna ta tarar da su cike da mamaki fall ranta ta furta wannan matar kuma mai take nufi zata zo wa mutane gida da sassafe umma ce ta kalleta tace yawwa intisar kinfito eaa.kawai ta bata amsa umma ce ta kara kallonta tace kuma kinga bakiyi break,banma yi abincin karin ba intisar ce ta kalleta tace nasani ai shisa idan na fita na ci kallon hanifa tayi tace ina kwana ko gama amsawa batayi ba ta juya tana jin haushin su har ta fito sai kuma ta dawo ta kalli indo tace umma bani aron mukullin motar ki,indo ta kalleta tace aa intisar baki kware ba fa karkije sai kuma tayi shiru intisar ce tace umma dan allah ki bani sauri nakeyi fa mika mata indo tayi ita kuma ta wuce fuu tana jan tsakin ganin hanifa....
Wani haddadden falo ne kai da gani komai yaji na alatu a cikin sa wasu yammata biyu na gani da gani kamarsu daya ba wani banbanci can sama na daga kaina na kalli wani katon bene wasu nagani na sakkowa dayan dattijo ne dan sanye yake da glass irin farin nan ya zuba wata shadda kai da gani taci naira sai matar kuma da gani matarsa ce ita kuma sanye da wani dakakken lace dinkin doguwar riga yasha dinkin zamani,sakkowarsu tai daidai da zamansu kusa da yaran nan daya ce ta kallesu tace good morning ma and pa amsawa tayi sukayi tare da fadin islaaam yau an tashi da wuri kenan ko dariya tayi dayar ce ta kallesu tare da ambatar abinda dayar ma ta fada amsawa dika sukayi suna murmushi...hajiya ce tace zaman me kuke baku fara break ba islam ce tace mom ku muke jira fa ko Haseenah ta kalli 'yar uwar ta ta tare da sakin murmushi alhajin ne ya kallesu yace ai kwa kun kyauta yarana tashi sukai suka nufi dining sai da suka zauna sannan mom tace,islam tashi kije ki kiramin yayanku kinji to kawai ta furta tare da tashi ta haye upstairs din benen..a kofar wani daki naga ta dakata kai tin daga waje zaka gane an kashe naira knocking take amma shiru kakeji har ta gaji zata tafi ne ta jiyo maganarsa tare da fadin waye amsawa tayi tare da fadin ni ce yaya budewa yayi nan idanuna suka gano min shi dauke da kwalbar giya sai rufe idanu yake yana rufewa tsaki taja ta kalli gefe sai kuma tace kazo zamuyi breakfast dan tsaki yaja cikin muryar maye yace ke haseena zan barar da ke ohhh..is.laam ko kije zanzo har ta juya ne yace islaaam zo nan tana zuwa yace kice sai ga amai kwaaaaa a jikinta fasa kara tayi tare da durkushewa a wajen kallonta yayi kawai yayi dariya yace ke dallah meye abin ihu shashasha kawai...haseena na jiyo ihunta yasa su tashi su dika sai ma'aikatan wajen suka nufi saman benan.....
Inaya ce zaune akan tabarma tana kirga kudi kallon inna tayi tace laa inna yau kinga ansiyar da wuri banyi tinanin zai kare yanzu ba inna ce ta kalleta tace ai kinsan kasuwa inaya wataran ya kare wataran kuma yayi saura,inaya ce ta kwanta a kan tabarmar dakin suna hira jefi jefi har bacci yayi awon gaba da ita..cikin baccin ne inna ke taba ta ke inaya tashi tayi tana ya kuna fuska tana juyawa idan ta ya sauka akan dr zubair janyo hijabinta tayi ta saka tare da zama,zubair ne ya kalleta yayi murmushi yace aa inaya yammata sai yanzu aka tashi kallonsa tayi tace ina kwana dr amsa ya bata da lafiya lau ya gida alhamdulillah kawai take binsa da ita sai kuma ta tashi tare da kawo mai sauran breakfast din da suka rage ita kuma ta fito ta shige bandaki domin wanka....
Hanifa ce ta kalleta tace ai ni indo kin bani mamaki wallahi yadda ake bin maganin dole ma zai yi aiki taya zakice mu tafi wajen wani bokan,lalle indo kina wasa wallahi da aikin boka badai ya baki kaidoji ba abinda ya rage miki shi ne amfani da magani yadda yace da kuma bin dokokinsa ke kanki sai kinyi mamakin maganin nan indo kallonta indo tayi tace to amma kuma ni so nake a raba tsakaninsu har abada fa amma dai ai zamu gani idan yayi...
Intisar sai da ta biya kudin admission sannan ta fito cike da mugun gudu kai akan motar ta hayo babban titi kai da ganin ran nan kasan a hade yake cikin gudun ne kawai ji kake casssssss karar karuwar motoci.....KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU
Chapter 26 · 0% Book details