← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 34

Sashe 7

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Page 13&14
Bude gidan inaya tayi suka shiga madaidaicin gidane mai dakuna 2 sai kitchen da toilet gaba daya gidan a malale yake da siminti sai rijiyar datake a gefe inaya tana kuwa tabarmar da suka dakko ne ta shimfidawa inna a inuwar gidan tana mata sannu yawwa inaya innar ta bata amsa ruwa ta samu ta kawo mata tasha sannan inaya ta zauna kukan dayaci karfinta ne yasa inna yiwa inaya magana inaya lafiya dai ko inaya ce tace inna bakomai kawai innarce ta kalleta tace haba inaya bai kamata ki boye min wani abu ba murmushi inaya tayi inna shikenan zan fada miki amma yanzu bara naje na siyo mana abinci da wannan chanjin udan nadawo zan fada miki meya faru shikenan inaya sai kin dawo cewar inna....
Inaya tana fita ganin unguwar tayi shiru itama bata damu da hakan ba ta nufi bakin titi inda ake saida abincin tafiya take tana tinanin abinda kuma intisar ke niyyar aikata mata allah ya gani bata da niyyar cutar da intisar sabida ta zagi mahaifiyar ta ne yasa ta mareta ba wai dan wani abu ba order da ake mata yasata zumbur dawowa daga tinanin dagowa tayi dikda bataga kowa ba acikin motar kasancewar motar mai bakin glass ce hakuri ta basa sannan ta wuce...
Hafsatce da intisar zaune akan kujarar palourn su intisar sai hira suke suna tafawa abinsu hajiya indo ce ta fito ta kallesu sai kuma ta kalli intisar taja tsaki ke intisar meye haka wacece kuma wannan intiar ce ta ce umma yar gidan alhaji aminu ce fa sakin fuska hajiya indo tayi auuh aa kace yar wajen binta ce murmushi hafsat tayi eaa wallahi umma hajiya indo ce ta kalle ta ai nadauka 'yar matsiyatar kika kara zuwa ki dakko min yayan talakawa marasa mutunci hafsat ce tai murmushi wallahi nima umma na tsani wannan inayar umma nadauka fa zataje wajen police hajiya indo ce ta zauna to in banda abinki hafsat ina zata iya uwarwa gareta da zai tsaya mata ita wai awa ma zata kai mu wajen 'yan sandan bayan ni naje na siye bakunan yan sandan tayaya intisar ce tace wallahi nima mom na tsaneta wai ni zata mara dan zagi tsohuwar uwarnan ta ta tada dade a duniya...
Inaya shigarta gida kenan aka kira sallar la'asar innarta taga bata nan kwala mata kira ta farayi can taji motsinta abandaki shimfidar inna ta tashi ita ta zauna akai tana kallon kwanon abinci sai kuma ta tashi ta dauro alwala dai dai nan innar ta fito sallah inayar ta tayar inna ma tazo ta tada sallar....
Dr Zubair tin bayan fitarsa daga gidan daya sa su inayar kiram ikram yayi akan su hadu ikram ne yaxe shikenan amma kuma fa ni ina gida sai dai kazo gidan nawa shikenan gani nan zuwa cewar dr Zubair.....
Intisar ce tai shiru hajiya indo tace intisar lafiya kuwa kallonta intisar tayi umma karfa ace daddy ya sani akan wannan batun kinsan dai baya nan ko hajiya indo ce tai murmushi wai ke intisar angaya miki ban shirya bane akan wannan abin daya faru ne intisar na shirya komai kowa da nasani zai bani matsala tini na biyasu ko kin manta yanzu kudi sune murmushi intisar din tayi gaskia dai umma shisa kike birgeni....
Inaya ce suke cin abincin da innarta innarce ta kalleta inaya innar ta ambaci sunanta naam ta amsa inna kifadamin meya faru wai inayarce ta tsayar da cin abincin inna zan fadamiki fa mugama cin abincin sai mu gyara dakin namu innarce tace shikenan inaya amma yanzu ya za ayi kinsan dai wannan yarinyar ta kone miki dakinki inayarce tace eaa wallahi inna ai intisar bazata gama da duniya lafiya ba innace tace kull inaya karna kara ji n wannan kalmar a bakinki inaya kiyi wa mutum fatan samun shiriya ba kidinga yi masa mugun baki ba ganin inna ta nuna bacin ranta yasa inaya tace ya hakuri inna nadaina bazan karaba shikenan tashi muje a gyara dakin musan abinyi inaya ce ta duba to amma inna sai mun ja ruwan sha dan ma munci sa'a da guga shikenan inaya...
Hafsat ce tace intisar to ni zan tafi naga magariba ta fara gabato shikenan hafsat bara nataka miki cewar intisar fitowa sukai yayin da suke a jere suna tafiya intisar ce tace hafsat nadai nafadamiki ki nemomin inda su inaya suka koma naji ancemin wani mai kankanba ne ya daukesu wallahi kowaye ubansa a garin nan sai yayi dana sanin daukarsu hafsat ce tace shikenan yanzu dai sai gobe idan zamuje bikin zeeyah zanzo miki da labari mai dadi shikenan hafsat dai dai bakin gate suka rabu yayin da intisar ta juyo tana fadin inaya inaya inaya ki shiga taitayinki fa....
Dr Zubair ne zaune akan karamar kujerar falon ya daga kansa sama shigowa ikram yayi ya zauna amma dr Zubair bai saniba ikram din ne ya dan tabasa take ya juyo yana kallon ikram din dr zubair ne yayi murmushi ashe ka fito ranka ya dade murmushi ikram yayi kawai sai kuma yace zubair naji kace akwai matsala wace irin matsala kenan...........👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
Chapter 7 · 0% Book details