← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 34

Sashe 24

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
53&54
Intisar zama tayi kofar gidan su inaya tana zubar da hawaye akan abinda tae wa inaya cikin kuka ta furta wai me yasa na tsane ta haka ne bayan da can bani da wata kawa sama da ita meyasa kuma lokaci guda kawai naji tsanarta inalillahi wa inna ilaihi rajiun ta ambata tare da sunkuyar da kanta tana ci gaba da kukanta akalla ta kai 20mint sannan ta tashi daga kofar gidan bakin titi ta tsaya tana tsaye a cikin wannan ranar wata mota ce ta faka kusa da ita, ko kallon motar batayi ba tana ji yana mata magana amma tai iskar kare da shi dai dai lokacin mai nafef ne yazo hucewa tsayar dashi tayi ta shiga tana gaya masa unguwar da zai kaita a zuciyar ta tana furta haba ni yau ina zan saka kaina ne.....
In'am ce tace allah sarki inaya na tausaya mata yaya amma mai zai hana a nemo wadda tayi mata hakan yaya ikram ne yace ina kokari in'am akan hakan amma na bari sai mun dawo sai munje gidan nasu tare ku gyasa ko in'am daga kanta tayi tace ea wallahi yaya domin ta bani tausayi matuka yaya wayarsa ya kalla dauka yayi tare da dialling number da ya bawa inaya sim din, inaya na zaune akan tabarma tana zubar da kwallah a zuciyar ta tana furta lallae talaka shi wato bashi da wani alfanu amma intisar ta bani mamaki yadda na dauke ta ba haka ta dauke ni ba jin karar waya ne yasata juyawa ganin wayar da aka bata ne jiya yasata dagawa tare da yin sallama ikram ne ya amsa yace mata sannu ko nasan baki gane mai magana ba ko eaa kawai ta bashi amsa dan murmushi yayi yana kallon hanyar daya ke driving yace ikram ne, inaya ce tace auu ya hakuri da rashin gane muryarka yallabai ikram ne yace ba komai ai yagida ya innar taki inaya ce tace lafiya lau fatan dai komai lafiya a haka dai suka ci gaba da wayar dik da inaya daga ea sai a'a sai da ya tabbatar da cewa ba wata matsala sannan yace zasu gaisa da wata kanwarsa in'am ce ta karba suka gaisa da ita sannan ya katse wayar....
Inaya ce tace ahab dama nafada ba abinda zaiyi dani zuciya ta ce kawai take rayamin cewa sona yake ashe ma yana da budurwa dan daga jin sautin muryar macen nan kasan ai budurwarsa ce kawai dama nasan tausayi na yake shisa ma har ya bani waya da kayan sutura da wannan tinanin ta kwanta akan tabarmar ta janyo wayar kusa da ita tai shiru tana tinani....
Hajiya indo ce zaune a falonta ita kadai tayi shiru tana tina maganar boka sai kuma ta kalli television din ta tare da sauke ajiyar zuciya lalle ya kamata kuwa na hakura da sallah ko dan nasamu na cika burina akan wadan nan yaran domin ni hajiya indo na tsani talaka, me ake da talaka idan ba ita ba intisar taya zatayi min kawance da inaya ai ni da farko na dauka abin nasu iya yara ne ashe har girmansu to ina bazai yiwu ba wallahi da sake yanzu dai abinda boka ya gayamin dashi zanyi amfani domin ganin na raba intisar da inaya.....Sallamar intisar ce ya dawo da ita daga duniyar tinani amsawa tayi tana kallon diyar ta ta da gaba dayanta sukuku,hajiya indo ce ta kalleta tace daga ina kike amsa kawai ta bata daga gidan su hafsat zata wuce ne indo tace mata haba intisar ya kamata fa kici abinci kinji ina zuwa bara na kawo miki zauna kinji shalele intisar ce ta zauna akan kujera tana tina yadda suka kare da inaya tabbas nayi kuskure tana cikin tinanin ne indo ta shigo ta dafata firgigit ta dago tace to maza kici kinji amsa tayi kawai tana ci....
Ikram sun sauka a gidan mahaifiyar su wato nafisa mutanen wannan gida sun yi farincikin ganinsu domin sun dade rabon da suga wani da daga cikin zuriar nafisa ba ko a lokacin da nafisa ta rasu sunyi sunyi akan a basu in'am amma aliyu ya hana su,tarba kuwa sun shata daga yan uwa...Zaune suke a wani daki aka saukesu wata dattijuwar mata ce ta shigo dauke da kofin roba a hannunta,ikram ne ya tashi ya karbi kofin sai kuma ya koma ya zuba wa in'am ruwan shima ya zuba sha sukayi sannan aka fara gaishe gaishe da hirar yaushe gamo yan uwa nata mamakin in'am yadda ta girma haka ita kuwa mutuniyar sai dariya take kasa kasa....
Intisar sai da yaci taci abincin tayi nakk sannan ta tashi daga falon zuwa dakinta indo ta kalleta tace intisar ina kuma zakije, bata ba ta amsa ba kawai ta wuce tana kallon hanyar datake bi domin gaba daya ta kasance haushin kowa take ji, shigewa tayi indo ce ta kalleta tace kyayi kya gama indai ni ce intisar ai nadau aniyar sai na rabaki da inaya wallahi da karfin kafin ta karasa ne hafsat ta shigo tare da sallama, sai da ta gaishe da umma sannan take tambayar ta intisar, umma ce tace tashi ki shiga tana ciki yanzun nan ta shiga tashi hafsat tayi ta nufi dakin....KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
55&56
Inaya ce zaune idanun nan kyar akan wayarta ji take dama ya kara kiranta ko sau daya ne wata zuciyar ce tace idan kinkirasa ki basa me kuma tsaki taja dai dai nan ikilima tai sallama inaya ce ta juyo ta amsa tare da fadin aa ikilima Bismillah zauna wadda aka kira ce da ikilimar ce ta zauna akan tabarmar inaya ce ta tashi ta kawo mata ruwa zama sukayi ikilima ce tace inaya allah ya shiryeki har yanzu kinki shigowa gidan mu ko inaya data rasa abinda zatace ne yasata fadin aa wallahi ikilima kinga da yanzu nai niyyar shigowa amma kuma inna bata nan wai da bari nai sai inna ta dawo sai na shigo mu gaisa ita dai ikilima murmushi tayi tace to dama ba wani abu bane nazo ne gayyatarki zuwa rabon chewing gum din bikina gobe zamu fara dan allah kizo kinji dariya inaya tayi amma ba har ranta tace shikenan nan zanzo insha allah ina kawarki in'am ikilima ce tace bata gari sun je unguwa amma nan da jibi zata dawo tashi ikilima tayi sai kuma inaya tace amma kuma ba anko ne dariya ikilima tayi tace akwai kedai kawai kizo murmushi tayi tace to zanzo sai anjima amarya dariya ikilima tayi tace wato harkin fara tsokanata ko inaya sallama sukai da haka ita kuma ta tafi abinta.....
Hafsat tana bude dakin intisar ta hango akan bed ta rungumi pillow sai hawayene ke zubowa daga kan fuskarta cike da rashin jin dadi hafsat ta rufe kofar tabi bayanta zama tayi kusa da ita ta dafata dagowa tayi tare da kama hannun hafsat,hafsat ce tai kokarin tambayar ta da cewa ke intisar lafiyarki kuwa cikin kuka intisar ke magana yanzu ace hafsat haka zanci gaba kenan hafsat inaya ce ina sonta har yanzu amma kuma sai na rinka yi mata wasu abubuwa kamar bani ba hafsat ya zanyi, yanzu haka fa daga gidan su nake ke kinga wulakancin da nai mata hafsat narasa me ke damuna wani lokacin ni wani lokacin bani ba hafsat yazanyi ita dai hafsat lallashinta kawai take da kyar ta samu ta hakura, hafsat ce tace yanzu tashi kije ki wanka kinga har 3 ta kusa kuma kince zamuje na rakaki siyayya zaki fara zuwa school ko daga mata kai kawai intisar tayi tare da tashi......
Ikram ne kwance a dakin da aka basa daga katifa sai zanen gado sai hasken gwan da yake da wuta kwance yake yayi luff abinsa cikin zuciyar sa sai sake sake yake cikin zuciyar sa ne ke furta dama ace ummana ta dawo allah sarki gashi ba abba sai mu kadai a duniyar nan nayi nayi da kawu muje dangin mahaifin mu amma yakiya wai meye matsalar hakan ne amma insha allah zan saka shi yaje da wayo da dabara,ko da yaushe idan na dakko zancen muje sai yace sai samu lokaci sallamar da akayi ce ta katsesa daga tinanin da yake tashi yayi kallon mai sallamar yayi yace Attahir shigo mana attahir ne ya shigo ya zauna ya kallesa yace yaushe zaku tafi yaya ikram kallonsa yayi a tsanake yace sai jibi kwana 2 zamuyi attahir ne yace to yanzu ka tashi muje cikin gari ka ga gari mana ko dai ka gaji ne yaya ikram kasan rabanka da garin nan wallahi har na manta ikram ne yace ai bazaka gane ba bane attahir bana samun lokaci ne ko da yaushe a aiki nake attahir ne ya mike da murmushi a fuskarsa shikenan to idan ka shirya ina waje ina jiranka ko.......
Dik hirar da suke akan kunnen hajiya indo rike haba tayi tare da furta lalle intisar wai me yake damunta, kenan dik bin bokayen da nake yarinyar nan bata hakura da kawancen nan ba anya anya kuwa yarinyar nan haka ta barta kuwa, kai gaskia da sake amma wucewa hajiya indo tayi tabi ta wajen dakinta, tana shiga ta doko kyauren tana cewa ahh dole, dole mana boka yace min nayi sake kai wannan tsinanniyar yarinyar wai me taiwa yarinya ta ne wayarta ta dauka wata number naga tai dialling ansaka hajiya Hanifa.....bugu daya aka daga hajiya indo ce ta furta hanifa da matsala fa, hanifa ce tace lafiya indo ce tace ina fa lafiya hanifa yarinyar nan dik irin magungunan bokan da nake bata amma taki daina san yarinyar nan wai ace ta kama har kuka take mata hanifa ce tace what kinga hajiya indo bari kawai ki gama dura mata magungunan zuwa nan da kwana 3 idan kingama abin baiyi ba sai mu chanja boka kawai ok hajiya indo ta furta ta kashe wayar kittt tare da zama tana dafa goshi....KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU
Chapter 24 · 0% Book details