← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 34

Sashe 20

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
45&46
Inaya ce ta shiga cikin gidansu dauke da sallama a bakinta,inna ta tarar a bakin murhu tana hura wuta inna ce ta dagota kalleta tare da furta inaya daga ina kike,cikin inda inda inaya tace am am dama dam katse ta inna tayi tace dama mai idan zakiyi magana kifito kiyi banason shashancin banza ko,nasande ba daga makaranta ki keba,shiru inaya tayi tana kallon mahaifiyar ta ta,naira 100 ta wulla mata dauki kije ki sayomin gawayi aikin banza kawai,fitowa inaya tayi ta nufi gidan sayen gawayin da sallama ta shiga gidan,a harabar gidan ta tarar da wata budurwa inaya ce tace yawwa Iklima bani gawayi na dika dan murmushi wadda aka kira da ikilima tayi tace to inaya na nawa na dika ta bata amsa,a dai dai lokacin in'am ta fito daga dakin tana kwala kiran iklima,sai kuma ta tsaya kallon inaya,inaya ce tace sannunki yawwa in'am ta ce inaya ce tace ta tafi ta dakko min gawayi ne shisa bata amsa ba dan murmushi in'am ta yi tace ok,iklima ce ta fito rike da gawayin mika mata tayi sai kuma tace inaya bakyason zuwa ko,murmushi inaya tayi tace wallahi ba haka bane ikilima kawai dai sai kuma tayi shiru in'am ce ta tsoma baki tare da fadin ba wani inaya kedai kawai ta kawata ce bakyason shigowa ko shikenan ai,inaya ce ta kalleta tace aa nikam inason shigowa wallahi kawai dai bana samun time ne ikilima ce tace bawani inaya murmushi tayi tace to naji dai yanzu sai anjima inna na jirana tare da juya iklima ce tace to ki gaida gida sai anjima juyowa tayi ta kalli in'am tace mushiga dakin ko juyawa tayi...
Intisar dik da tana cikin cell bakinta bai mutu ba sai zage zage take kamar 'yar maguzawa,hajiya indo ce ta tashigo yayin da taga intisar karasawa wajen ta tayi intisar ce tace umma wallahi sai na dau fansa akan abinda yarinyar nan tayi min,nizata yiwa hakan ni wai tabbb,rufe mata baki umma tayi tace shhhi intisar ina zuwa yanzu zan fito office din dpo ta shiga ta kutsa kai ko sallama babu a zaune ta sameshi dagowa yayi ya kalleta yace zauna,zama tayi tana zare ido mika mata wata takarda tayi ta saka hannu sannan ta ajiye wasu kudi akan table kallon kudin yayi,tare da kiran sergent shigow tayi fada mata yayi akan ta fito da intisar cikin salon aikinta ta juya ta tafi hajiya indo ce take murmushi tare da zabga godiya banza da ita yayi ya juya....
A bakin police station din na hangesu suna kokarin shiga mota yayin da idanun intisar suka cika da hawaye kallon hajiya indo tayi tace umma wallahi sai na wa yarinyar nan abinda bata taba zato ba ni zatayi wa hakan ko an fada mata ana tabani a zauna lafiya ne ita dai hajiya indo murmushi tayi tace shigo mutafi nasan yadda zamuyi da ita kawai kinji badan taso ba ta shiga ta tada mita suka tafi zuwa gida...
Ikram ne zaune gabansa kuma ibrahim ne tsuggune dukun dukun dashi ga wani sawun duka a saman fuskarsa , kallon sa ikram yayi yace mai ya hadaka da inaya cikin daga kai ya dago yace eyeee eaah ikram ya bashi amsa ibrahim cikin inda inda ya fara wallahi yallabai dama katsesa shaik yayi cikin muryar manya yace ba da kai ake magana ba a zabure ibrahim yace yallabai wallahi da can budurwa tace amma daga baya sai akazo aka gayamun magana akanta ikram ne yace good me aka fada maka kuma me yasa rannan naganka kamar kana mata magana tana kuka ibrahim ne yace yallabai wallahi wata magana aka gayamun akanta cewa ita din 'yar iska ce wani wawan mari ya sakar masa karka kuskura ka karasamun shashasha kawai waya gaya maka wannan maganar kuma yallabai wallahi wata kawarta ce fadin ibrahim tsaki ikram yaja yace wacece ita yallabai bansanta ba amma zan iya ganeta idan na ganta sau daya ikram ne ya katsesa ba wannan ba abinda nakeso da kai shine ka wuce kaje ka sameta nan da gobe ka bata hakuri kuma inaso ka samin ido akanta dik wani abu daya faru da ita kazo ka gayamin kuma banason kowa ya sani dan haka ka kiyaye kaji ko to ibrahim yace ikram ne yayi wa shaik alamar su tafi tabashi yayi sannan suka juya ibrahim dai sai ido yake dan yasha wuya a wajen shaik....
Zubair ne ya shigo gidan dai dai lokacin shaik na fita a falo ya tarar da ikram zama yayi yace karfa ka manta kace zamuje wajen inaya kuma naga ko shiryawa bakayi ba dan murmushi yayi yace ai yanzu kuwa zan shirya dama zuwan naka nake son gani tinda kuwa kazo ai shikenan tashi yayi ya tafi bedroom shi kuwa zubair ya kunna kallo...
In'am ce ta fito iklima ce tace ke yanzu bazaki bari a jima ba haba in'am murmushi tayi tace ke bazaki gane ba yayana ya hanani dadewa a unguwa wannan ma fa bai san na fito ba wallahi iklima ce tace to muje na taka maki ko tafiya suka fara sai kuma in'am tace dan allah iklima muje gidan su inaya mana dan murmushi tayi tace to kinga gidan nan muje mana da sallama suka shiga gidan a lokacin inaya tana wankin kayanta ganinsu da tayi murmushi tayi tace ku shigo mana tabarma ta shimfida musu tare da kawo musu purewater,inna ce ta fito daga kitchen suka kara gaisawa iklima ce tace to inaya tinda ke bakya zuwa ni ai nazo kuma na huce gori dariya inaya tayi tace ya hakuri fa ga bakuwar taki har zata tafi ko murmushi in'am tayi tace aa in'am fa ba bakuwa ba gaba dayansu dariya sukayi sunyi akalla 5mint sannan suka tashi inaya sai da ta rakasu har kofar gida sannan ta dawo taci gaba da wankinta....KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU
Chapter 20 · 0% Book details