← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 34

Sashe 14

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kafin ya shugo inaya har ta shimfida masa tabarma ita kuma inna tana zaune akan kujera ta katako dr ne ya zauna tare da gai da inna gaisawa sukayi tana ta masa godiya akan abinda ya musu sosa kai yayi yace to inna ai yiwa kaine ba komai wallahi inna ce tace ai a zamanin nan ba kowa bane yake taimakon talaka ba dan nan shi dai shiru yayi inaya ce ta ajiye masa ruwa a kofi sai plate din abinci sannan suka gaisa dashi cike da fara'a ya amsa mata itama godiya take masa shi abinma mamaki ya fara bawa zubair wannan godiya da adduoi da suke jero wa haka ruwan yasha kadan inaya ce tace dr kaci abincin mana dariya yayi yace aa inaya wataran idan nadawo na ci yanzu fa sauri muke bakiga ni da wani ba inna ce tace aa shikuma bai shigoba zubair ne yace aa dama inna muna sauri shikenan nan ai zubair ne ya kalli inaya yace biyoni ki amshi wani sako inna ce tace aa zubair kabarshi hakan ma dakayi mana allah ya biya ka dan nan allah yasa a mizani ameen ya amsa sannan yace haba inna siyayyar fa nariga danayi kuma inna yaza ai haka ba yanda inna batayi ba amma yace aa dan haka dole suka hakura tashi yayi,yayiwa inna sai da safe sannan ya fito inaya ce ke binsa a baya unguwar ya kalla yace amma inaya wannan unguwa taku da dahu take murmushi tayi tace ea dr dama haka unguwar take ai amma kuma ai tana da dadin zama shidai kawai murmushi yayi ya juya ta bisa kallon inda ya bar ikram yayi amma yaga wayam sai da suka fito ya hangosa kusa da motar su tafiya yayi suna zuwa inaya ce ta gaida ikram shiru yayi yana tina inda yasan wannan muryar sai da zubair ya taba shi sannan yace lafiya lau ykike alhamdulillah tace kawai zubair ne ya boot ya fito da katuwar leda ya mika mata kallonsa tayi haba dr wannan kayan sunyi yawa wallahi na amsa inna ta sai ta min fada murmushi zubair yayi yace iya fada ai nadauka har da duka dariya tayi kawai wata mota ce ta taho ta haske su ikram idanunsa akan inaya take ya furta kai dama kece itama din kallonsa tayi tace aa yallabai wallahi ni ce zubair kuwa ya zama dan kallo a wajen nan fa ikram ya hau zuba shi zubair abin ma mamaki yake basa yanzu ace ikram ne yake wa mace wannan surutun lalle inaya taci sa'a ganin sun maidashi dan kallo ne yasa ya kalli inaya yace ki wuce mana kin bar inna ita kadai to ta bashi amsa sai da safe tayi musu sannan ta wuce yayin da ikram ya bita da kallo kawai zubair ne ya tabashi yace wai kai a ina kasanta ne ma....
Tafiya suke kowa yayi shiru akwai saken saken da kowannen su yake zubair mamaki yake yanda akai har ikram yasan inaya ikram mamaki yake kar dai ace itace yarinyar da ya ke taimaka musu zubair ne yayi karfin halin fadar ikram dama kasan ta ne kayataccen murmushi yasaki shikuwa zubair yasaki baki yana kallonsa amsa ya basa aa na taba kadeta ne a lokacin ina sauri zanzo wajenka to shine bama taji wani ciwo ba daganan dai muka saba kace inaya sunanta ko amsa ya basa da eaa yaci gaba da driving dinsa...
Direct gidan su amarya suka nufa tin a kofar layin sukaga motocin daukar amarya wayar ikram ce tai kara dubawa yayi yaga an rubuta ahmad dagawa yayi ikram wai yadai naga fa har yanzu shiru ikram ne ya mikawa zubair,zubair ne yace kaganmu mun iso ma yanzu haka mune moyar karshe ok ahmad ya katse shi kadai a tsaye yana mamakin halin ikram na rashin yin magana ya kirasa amma yabawa zubair can kuma yayi murmushi yace kai allah ya kyauta dai ikram ne ya kalli Zubair yace amma dr badai mata zaka dura mana a cikin wannan motar ba kafin ya rufe bakinsa intisar ce da hafsa sai wasu kawayensu biyu sunyi knocking wajen zaman zubair yana budewa ya kalli intisar yana murmushi itakam hankalinta na kan ikram bude mana mu shiga ta fada tana kallon ikram zubair ne yace ok tare da maida glass din ya rufe ikram ne yace ok kaje nikam kara na sauka nabi su ahmad zaka zo ka dauki wannan mata haka wayarsa ya dauka kawai ya fito har yayi nisa intisar ta bisa cak ya tsaya ganin ta rike masa hannu tana turo baki yakuna fuska yayi yaja tsaki wasu shahararrun maruka 2 ya bata a kowanne kunci na fuskarta sakinsa tayi kallonta ya kuma yi ke baki san darajar mace ba ne ko me kizama mace mai tarbiya mana ko angaya miki ni abokin wasan ki ne har zaki rike min hannu ke ya isheki ma meye hadina dake wallahi sai na fasa miki baki shegiya ai ni ba abokin ashararancinki bane yar iska kuma ki koma makaranta kinji dan naga ilimin addini bai isheki ba juyawa yayi fuu sai da yayi kamar taku 3 sannan cikin kuka intisar ta furta wallahi zaka sani badai ni ka wulakanta ba zan maka abinda baka taba zato ba juyowa yayi tare da murmushi fatan nasara allah ya baki sa'a kinji....👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷
Chapter 14 · 0% Book details