← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 34

Sashe 17

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
35&36
WANENE MUHAMMAD IKRAM
Alhaji muhammad Saleh asalin sunan mahaifin ikram dan cikin garin katsina kowa nashi yana garin katsina mahaifinsa alh saleh wato kaka ga ikram ya kasance malami ne babba a cikin garin yana da yara 5 dika maza akwai Aliyu,Usman,Salisu,Muhammad,Abubakar karaminsu kenan ya kadance yana da mata biyu daya Maijidda daya kuma saratu mai jidda mace ce mai hakuri akan komai sabanin saratu masifaffiya ce dik da cewa ita ce amarya ita saratutana da yara 2 salisu da kuma abubakar sai maijidda mai yara 3 usman aliyu muhammad tin tasowarsu sun taso cikin ilimi da sanin ya kamata sannan basu da jan fada sabanin yaran saratu da kullun sai ankawi kararsu malam tin yana damuwa har ya daina idan yayi musu fada sai tayi fishi ta tashi ta bar masa wajen sai idan yazo dakinta sai ta rinka sakin bakaken maganganu ba abinda take gani sai yaran maijidda ace warta su maza ne koba komai gadonsu sai yafi nasu yawa da wannan dalilin ta tsanesu bata kaunar ganinsu a haka dai ske rayuwa da dadi ba dadi.....
Wata rana sun dawo daga makaranta a lokacin malam yana masalaci ita kuma maijidda bata nan taje gidansu su usman ne suka shigo suna dariya sun dawo daga makaranta sarstu tana ganinsu tace maza ku ajiye jakunkunan ku ku debo min ruwa maza kallon kallo suka farayiwa juna sun san dai ba'a sasu dibar ruwa aliyu ne ya kallesu ya kalleta yace wallahi bazan debo ba ba malam yace kar wanda ya kara gani zai debo ruwa ba saratu tashi tai ta sameshi tai ta dukansa sauran sukazo cetansa da kyar ta kyalesa koda malam yazo sai ta futittike tace ai aliyu ne ya zageta dole suka hakura.....
Bayan sati 2 Usman ne da maijidda suna yiwa saro sallama akan su fa zasuje kauye sai sun dawo kuma da saratu kamar bazata tanka ba sai kuma tace to sai kun dawo suna gama sallama ta dawo dakinta tare da furta allah yasa ki hadu da ajalinki ke da bakyajin haushi tin tafiyar maijidda saro ta samu yan aiki dan tadaina barinsu suna zuwa makaranta indai malam yayi fitar sassafe dik da wani abun aliyu bayayi sai dai Muhammad yayi.....
Kwanan maijidda 3 a hanyarsu ta dawowa suka hatsari kuma suka mutu ita da danta usman bayan sadaqar bakwai nan fa saratu ta fara jaraba akan dole su Muhammad da ali su koma shagon kofar gida saboda wai dakinta yayi mata kadan gasu abubakar malam ma ya yadda da shawarar ta ta haka aka mai dasu waje bayan wani lokaci Muhammad ya gama karatun secondary sai kuma ya fara zuwa kasuwa yana ci gaba kuma da kulawa da kanensa aliyu dik da idan suka shiga tana nuna musu su fita.....
Bayan shekara 2 Muhammad natafiya kasuwa kuma alhamdulillah kasuwa tana kyau dan yanzu sun daina cin abincin gidan sai dai Muhammad ya siyo musu bayan aliyu yayi graduation ya nuna yana son ya rika zuwa kasuwa amma Muhammad furr ya hana akan shi yafiso ya yi jamb yaci gaba da karatunsa saboda shi ya samu ya yi ilimin haka aliyu ya hakura yana jiran lokacin ta bayan wasu watanni kwatsam suka tashi da mutuwar mahaifinsu malam saleh tabbas sunyi rashi kamar yadda suka rasa mahaifiyarsu....
Saratu bayan sadaqar arba'in kwance take akan tabarma gefe daya kuma radion ta ne tana ji aliyu ne ya shigo ya tsugunna yana gaishe ta tsaki taja kai ni rabu dani mana salisu ne yayi sallama aliyu ne ya gaishe shi amsawa yayi cike da murmushi a fuskarsa saratu kuwa tabe baki tayi tai banza dasu....bayan shekara 5 komai ya chanja aliyu ya gama degree din sa a bangaren business Muhammad kuma yana dan zama ana koya masa waani dik da ya samu wata makaranta ta yaki da jahilci yana zuwa da daddare kullun banda weekend to shima ya samu kasuwanci suke yayin da suka ma tashi daga garin funtua anan allah ya hada sa da wata yarinya mai suna Nafisa har dai allah yayi akayi auren ta da Muhammad bayan wata tara suka haifi yaro namiji kyakkyawa wanda aka sa masa suna MUHAMMAD IKRAM arziki a wajen Muhammad sai abinda yayi gaba bayan sunan aliyu ne zaune shi da dan uwansa kallonsa yayi yace yaya mai zai hana mu bude company shiru Muhammad yayi yace amma tayaya aliyu yayi murmushi yace kawai ka barmin komai yaya shikenan ya furta....
Bayan shekara 7 da haihuwar ikram sannan allah ya kara bata ciki shikuma yanzu Muhammad yanzu suna da company daya wa dan a kalla zasuyi 5 dik da hudu na Muhammad ne bayan wata tara da watarana nafisa ta tashi da ciwon nakuda haka aka tafi asibiti da kyar ta haifeta ita kuma anan allah ya dauki ranta anan aka mayar da sunan mahaifiyar ta nafisa suna mata lakabi da in'am Muhammad yayi bakin ciki kwarai dikda aliyu na kwantar masa da hankali amma sam shi sai dai daga baya ya hakura haka suka taso suna rayuwa har shima Muhammad allah ya karbi abinsa kar kazo kaga bakin ciki wajen aliyu har susuce wa ya fara sai da kyar aka samu ya dawo dai dai bayan mutuwar sa ne shima sai ya yanke shawarar aure kuma haka aka daura masa aure shi da wata mai suna asiya daga nan ya dauketa sai garin malumfashi asiya ta kula da su ikram tamkar yaranta amma ita allah bai bata haihuwa har ita ma tayi accident a hanyar ta ta zuwa funtua allah ya karbi abarsa wannan kenan......
ALLAH KAJI KAN 'YAN UWANMU WADANDA SUKA RASU ALLAH YA KYAUTATA TAMU MUMA YASA MUCIKA DA IMANI....AMEEEN...KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNMU
Chapter 17 · 0% Book details