Sashe 30
Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
71&72
Karfe 8 mai kyau hafsat ce ta sauka gidan su intisar a falo ta samesu suna breakfast cike da ladabi ta gaishe da hajiya indo yayin da ita kuma sai baje baki take tana amsawa har da tambayarta mahaifiyar ta bayan sun gaisa ne intisar ce taja ta dauke da plate din a hannunta mara karayar suna shiga intisar ce tace hafsat ya akayi ne me ya faru hafsat ce tace tabbas intisar hasashenki gaskiya ne domin da idanuna naga ikram da inaya suna hira suna dariya abin yayi marukar daure min kai intisar,intisar ce tace aa hafsat bazai daure miki kai ba wallahi domin ni dama nayi zargin hakan ko a lokacin da naje gidan su da irin cika bakin da take nasan tabbas akwai wani wanda ya ke dafa musu kuma tinda na kuskura na gano sa to wallahi sai na rabata da shi domin ikram na wane ni kadai hafsat ce tace tayaya kenan intisar murmushi tayi tace ba wanda ya sani sai ni kuma ba wanda zan bari ya sani ke dai kawai muje zuwa...
Kowa ya hallara a bakin dining hajiya ce ta kalli gate man din da aka kira da sauran masu aikin ta furta ku a cikin ku kuna nifin ba wanda yaga shigowar sa eaa dikansu suka bata amsa gate man yace hajiya khalifa bai dawo gidan nan ba tin jiya daya fita da yamma ni ma har 1 nazauna jiransa amma hajiya shiru bai dawo abin ya daurewa hajiya kai ga alhaji baya nan sallamarsu tayi suka tashi,wayar ta ta janyo taci gaba da kira dik da wayar switch off take fada mata amma taki yadda da abinda tace mata...ganin fa da gaske switch off ne yasata farakiran alhaji dagawa yayi yace lafiya dai koh hajiya ce ta furta ina fa lafiya alhaji tinda khalifa ya fita tin jiya bai dawo alhaji ne ya bata amsa kidaina wahalar da kanki hajiya domin ni nasan zai dawo da kafafunsa dan haka kawai ki jirasa fah kit ya kashe...
Indo ce ta fito da mayafi a kanta dakin su intisar ta shiga ta samesu suna hira intisar ta kalla tace to ni zan fita dan haka ki kula da gidan kinji to kawai intisar ta bata amsa suak ci gaba da hirarsu...bata zame ko ina ba sai gidan hajiya hanifa kallonta hanifa tayi tace ohh harkin shiryo kenan to kawai muje daga nan suka shiga mota suka nifi wajen garin sunyi wani tafiya mai nisa sosai sannan suka sauka sak wajen bokan nan suka koma amma a wannan karan bukkan da suka shiga ta 4 ce take wajen ya fara jujjuyawa da wani irin amo mara dadin ji...
Ikram ne na hango a filin jirgi yana tsaye shi da zubair suna kallon hanyar da mutanan suke fitowa dai dai nan idanun ikram suka sauka akan alhaji aliyu da sauri ya karsa yana kiran sunan kawu daganan kuma suka shige zuwa tafiya domin su isa gida da wuri suna cikin tafiya ne har suka hau mota zuwa gidan sa..... in'am tana jin an fada mata cewa kawu yau zai dawo ta dauki aniyar daukar aniyar yau ita zatai masa girki dan haka can na hango in'am a kitchen tana aikin dafa abinci yayin da sauran masu aikin suke taimaka mata bata dade da gamawa ba ta shige dakinta domin taje tai wanka ta jira kuma dawowar su...
A gaban bokan suka zube dariya ya babbake da ita yana mai ambatar sannunku da zuwa ya ke indo da kuma hanifa hhhhhhhh tin kafin kizo aljani zurukus ya gabatar min da zuwanku dan haka nasan ma meye yake tafe dake tafa hannunsa yayi sai ga wasu kullikan a hannunsa mika mata yayi yace ga wannan kije zakiga mai zai faru zata dawo son sa dahaka ku tashi kuje amma kafin nan zaku ajiye naira dubu dari 500 kudin akinki na baya da kuma wannan cikin rawar murya tace to suka ajiye tare da tashi suna muzurai suka kama hanya fita daga wajen....KAWANCEN MU
Writing and Story
Waleedah Muhammad
AUNTYNNMU
KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
73&74
Tin daga bakin gate zaka gane yau chakewar tafi ta kullun domin yadda ya buga kansa a jikin gate din ne yasa mai gadin budewa ya kallesa tare da furta kai khalifa daga ina kake kallinsa khalifa yayi yace "daga inda ka aikeni dallah matsamin hanya ni na huce domin bazan iya tsayawa ana ba gate man ne yace aa khalifa wazai shigo kuma da motar tsaki yaja kawai ya tunkude gateman din ya wuce ai da sauri daya daga cikin ma'aikatan ne ya shiga a fslo ya tarar da hajiya, kallonta yayi, yace hajiya ki fito ga khalifa nan ya dawo,mikewa tayi zata tashi dai dai nan khalifa ya shigo, kallonsa hajiya tayi tare da kawar da kanta daga kallonsa hawayen da take kokarin boyewa ne ya zubo mata tare da dan jan tsaki,islam ce da haseena suka fito sannan suka ga khalifa a gaban hajiya, hajiyar ce ta kalli mai aikin tace zaka iya tafiya kawai shikenan to kawai yace ya fito,khalifa ne ya kalleta yace mommy sannu fa ba ta iya kallonsa ba sai shigewa dakin da tayi kallon kallo ne tsakanin islam da haseena,ai da gudu suka bar falon suna rige rigen hawa upstairs,kallonsu khalifa yayi cikin maye kaji banzaye suke gudu to ni mai zan musu tsaki yaja yaci gaba da timbelensa ana wajen gaba daya da ka gansa kasan notin kansa ya kunce a kwale yake..
Intisar kallon wayar hannunta tayi sai kuma naga kawai ta kara a kunne tare da fadin hello banji me akecewa ba sai ji nai tace ok shikenan nan da gobe kawai ma ya isa sai kuma ta katse.. intisar ce kawai tai murmushi tace inaya gani nan kanki wallahi dan nadau alkawarin sai na miki abinda yafi na baya...hanifa ce ta kalli indo tace wai ke tsaya ya kikai da maganin da wannan bokan ya baki kallonta tayi tace wane magani,maganin da aka baki na yadda zataji tsanar inaya ohh wai wannan a lokacin mana ta tai accident anan na samu na karar dashi dan haka na tabbata yanxu intisar akwai abinda take kullawa akanta...
In'am ce zaune sai kawu daya ke akan kujera masu aikin ne suka jeru domin su gaishe dashi suna gamawa falon ya zama na daga Ikram sai zubair da in'am hira suke sosai a dai dai lokacin wayar alhaji aliyu tayi ruri dagawa kawai yayi sai kuma yace ok zanzo.... Zubair ne yayi masu sallama ya wuce aka barau daga shi sai in'am ikram ne yayi shiru sai kuma ya nisa yace uncle dan allah inaso idan kasamu dama inaso muje dangin ku,kallonsa aliyu yayi yace eaa kuma kaima kace wani abu nima inason muje amma kuma banasamun lokaci amma kuma zamuje idan yaso sai mubar company a hannun Micheal ko ikram ne yace eaa wallahi kawu,kawu ne yace ya wajen su hajiya samira ya kuka barosu,alhamdulillah sunce kawu dik a gaishe da ku muna amsawa shikenan kawai ikram zamuje din yadda kace ko to kawai yace tare suka tashi suka nufi dining din daya dakin....
Hajiya ce take zubar da hawaye daga idanunta su islam ne suka shigo suma hawayen ne yake zuba islam ce ta kalleta tace dan allah mommy kiyi hakuri kinji to islam ya kike so nayi ne iya tarbiyya na bawa Khalifa amma yanzu ya barar da wannan tarbiyya narasa ta yadda akai khalifa ya koma shaye shaye har yake driving ba da ban allah yana tsarewa ba sai dai wani zancen islam haseena ce tace aa kiyi hakuri mommy kinji dan allah kiyi shiru goge hawayen fuskarta tayi tace yanzu yana ina mun barsa a falo fadin islam shikenan muje muga me yake aikatawa kamar mommy ta sani tana fitowa suka ganshi yana ta kuza amai ga wani hamamin wari yana tashi daga falo take dikansu suka toshe hanci banda mommy....KAWANCEN MU
Writing and Story
Waleedah Muhammad
KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
75&76
Inaya tin bayan dawowar ta daga makaran ta tana zaune kamar kullin abincin ta taja ta fara ci cike da tinanin ikram ita kadai sai kaga tana murmushi abinda da farin shiga a soyayya inna ce tace wai inaya mai kikeyi ne haka kiyi ki tashi ki wuce ki min wanke wanke ga shara ma banba kuma anjima inason ma kije kasuwa amma ke kinki bada hankalinki kiyi da jiki ko murmushi tayi tace inna dik zanyi tinda nasan aiki na ne ai,kuma zanyi wanki ma naga kayan naki sun yi dauda ko,inna ce tace eaa da kuwa kin kyauta...
Indo dauke da kasakon tiraren wuta ta wani banka wani magani mai shegen wari gaba daya gidan wani wari yakeyi da alama maganin da boka intisar ce ta fito cikin yatsina face tsayawarta kenan a falo wani amai ya taso mata da sauri ta shige bandaki sai da tafito indo ke tambayar ta lafiya ganinta tayi sanye da hijab kallonta tay tace intisar ina zaki kuma amsa ta bata asibiti mana umma ko kin manta yaune za a kuncemin hannun nan murmushi umma tayi tace to idan kinje ki gaishe da zubair kinji,zai ji kawai ta bata amsa tare da fadin sai na dawo umma tana fita tai murmushi tace daga farawa da samun nasara dole ma na rike boka hannu bibbiyu..ficewa tayi tana fita batai tafiya mai nisa wata mota tazo tai parking shiga kawai tayi dai dai asibitin ya sauketa har ta fito ta leka ta glass tace kagane ai saura kuma kai min shirme wallahi a cikin kudinka dan nasanka da shiririta...amsa ya bata aa hajiya insha allah ai ba shirme indai da naira ba matsala fa...