← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 34

Sashe 21

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
47&48
Intisar ce sai kyabe fuska take,fuskar nan dauke da hawaye suna zuba umma ce ta shigo falon ta kalleta tace ai sai ki zauna kita kukan tinda haka kika zaba ba zaki zauna ki karatun ta nutsu ba aikin banza kawai,intisar ce ta dago ta kalleta wai umma ya zanyi ne kallonta tayi tace idan kinshirya shawara sai ki taso mushiga daga cikin dakin ko,tashi tashi tana kallon jikinta yadda tayi dukun dukun da ita sai kuma taja tsaki.....
Ikram ne da zubair tsaye a kofar gidan su inaya kallon zubair yayi yace yanzu ya za ayi zubair ne yace ok bara kaga,sallama yayi a lokacin inaya tana dakinta jin sallamar namiji ne yasata mikewa ta fito a kofar kitchen ta tarar da inna kallinta tayi tace yawwa inaya leka kiga wanene yazo ok inna ta furta tayo waje zubair ta gani da dan sauri ta fito tace yau kaine dr ai da ka shigo juyowa tayi sai kuma taga ikram tace auu dama tare kuke to ku shigo mana.Tin lokacin da inaya ta fito ikram ya dora idanunsa a kanta take yaji wani darr a ransa a zuciyar sa ke furta lalle inaya kyakkyawa ce ga hankali,ga nutsuwa, ga tarbiyya tabbas wannan ita ce ta dace dani yanzu na sami mata,zubair ne ya tabasa firgigit ya juyo kazo mushiga ok kawai yace ya dakko wayarsa suka nufi cikin gidan allah allah ikram yake domin ya kara ganinta cikin abayar dake jikinta kamar ba inaya ba ya furta, a tsakar gida suka tarar da tabarma zama sukayi suka fara gaishe da inna cike da jin dadi ta amsa sai kuma tace to dr Zubair ina kuma aka samu wannan ta nuna ikram dariya yayi zai yi magana inna ta juya tana kallon inaya data rakube tace ke kuma me kikeyi haka tashi kije ki dakko musu ruwa mana to tace tare da tashi ta shiga kitchen.Hira suke sosai tsakanin zubair da inna sai ikram kuma da jefi jefi yake sa musu baki kiran wayar sa ne ya katsesa dauka yayi yace zubair bara naje daga waje zan daga wayar nan, to ya bashi amsa inaya ce ta fito daga kitchen dauke da ruwa a faranti ajiye wa tayi tare da gaishe da zubair gaisawa sukai sosai cikin sakin fuska zubair ne ya dauki ruwan yace to ni na dauki nawa ki kaima Ikram sauran yana waje dan na sami hira da inna dan dariya tayi ta dauki ruwan ta taho a jikin mota ta tarar dashi a tsaye yana kallon kofar gidan dagowa yayi dai dai nan ya katse wayar tare da furta inaya matso mana karasawa tayi tace to ruwan ta bashi ya dauka sannan kuma tai shiru, ruwan ya sha ya rage ya ajiye mata a kan farantin har zata juya sai yace saurin me kike yi haka, shiru tayi sai kuma yace inaya fa dago kai tayi tana kallon sa sai kuma ta kau da kanta gefe dan murmusawa yayi yace shikenan tinda kunya ta kikeji jeki ciki to da sauri ta wuce kamar ana hankada ta shi kansa dariya ma ta bashi ya juya yana murmushi tare da jujjuya kai cikin farin ciki kasancewar sa da ita..
Tana ajiye farantin a kitchen ya shigo dauke da katuwar leda tana hangensa ta window din kitchen din zama yayi yace inna ga wannan ba yawa inna ce tace aa ikram bazamu amsa ba haba ina laifi ma kayan da kabawa inaya waccan zuwan ikram ne yace aa inna kar muyi haka dake ke din tamkar mahaifiya ce a gareni bai kamata dannai muku kyauta ba ki nuna kin amincewar ki bazan ji dadi ba idan kikai hakan, da kyar da sa bakin zubair ta amshi kayan yayin da take ta kwararo masa addua ita kuwa inaya kawai leke take cikin leken ne inna ta kwala mata kira wai inaya mai kike aikatawa ne tin dazu kinki fitowa,cikin sanyin murya tace inna fa gani nan dan tabe baki inaya tayi tace ea kawai yayi ta kalleni a banza ji fa yadda ya zuba min na mujiya dan allah,fitowa tayi ta tsugunna tare da taya inna godiya sannan suka tashi zasu tafi,inna ce tace maza ki raka su kinji inaya toh kawai tace ta fito a tsaye taga ikram shi kam zubair na mota, Wata leda ya mika mata girgiza masa kai tayi tace aa kabarshi kafa bamu.. bata karasa ba ya dakatar da ita yace ya isa inaya banason nai kyauta ace min aa dan haka karbi ki huce,karba tayi amma ta kasa godiya sai raba ido take kamar wata bakuwa shi kam murmushi yayi yace sai anjima ko anan ne ta iya cewa to nagode sai anjima ta juya da mugun sauri, a soro taci birki tana dafe kirji wai ni inaya wai meyake nifine da ni haba sai kuma tace to me ma zai dani,kalleni fa murmushi tayi ta shigo da sallama a bakinta....
Inna wannan kayan fa kallonta tayi tace wallahi to kinga inaya dik wannan aikin ikram allah ya saka masa da alkhairi ameen inaya ta ce ta tsugunna tana kallon kaya tin daga kan Vaseline,powder,lipstick atamfa da sauransu dik da akwai sai da tagama gani sannan ta tina da ledar hannunta,dakko ta tayi tace inna kinga ma ledar daya bani budewa tayi sai tace laaa inna kinga waya ce saurin kallon kwalin tayi tace allah sarki ikram, kiciniyar bude wayar inaya takeyi masha allah sabuwa ce irin itel din nan karama da murmushi tace kinga inna nuna mata ita tayi ta ganta a hade take kunna harda sim inna ta gani inna sai sanya albarka take inaya ta kira sunanta ta dago anan ta fara yi mata nasiha akan duniya da kuma wa'azi daga nan kuma suka tashi sukai sallah magariba...KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU
Chapter 21 · 0% Book details