← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 34

Sashe 28

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
63&64
Islam tin da ta fito daga bandaki take kuka haseena ce ta kalleta tace dan allah islam kiyi hakuri kinji,kinga yaya khalifa bai ma san yayi ba please so sorry dago kanta islam tayi ta kalleta tace to ina amfanin shaye shaye haseena me ya amfanar, dole ne ma mu taka masa birki haseena dole taya muna ji muna gani zai kashe kansa a banza,yana shaye shaye over kuma ace ba ma iya cigarette ba shine shisa,giya,cocaine ke dik wani kayan shaye shaye sha yake ki duba fa haseena a lokaci daya ji yadda ya koma yayi wani baki ya rame ya zama kamar ba shi ba, ni narasa taya akai ya khalifa yake irin wannan rayuwar haba haseena kara fashewa tayi da kuka tana rarrashinta haseena cikin kuka ta furta islam ya yakike so muyi da shi ne ya kikeso muyi fa shi daddy ya fiki jin bakin cikin hakan fa jin ana knocking ne yasa su goge hawayen fuskarsu haseena ce ta tashi ta bude mai aiki ce yace ku fito kuje kuyi break inji hajiya to kawai haseena ta bata amsa ita kuma ta dawo cikin dakin....
Dr zubair yana shiga idanunsa suka sauka akan intisar da kanta yake zubar da jini yayin da nurse ke kokarin yin dressing din wajen sai kuma hannunta da tashin farko ya wani kumbura over sai fuskarta da 'YAN raunika kanana,karasa wa yayi hameed ne yace dr dama abinda yasa muka kira ka kenan ka duba mata hannunta karaya ce sai kuma tana buqatar jini kuma ni banga wani dan uwanta da yazo ba dik da dai mun kira mahaifiyar ta zubair ya kallesa yace ba matsala ai wannan dik mai sauki ne yanzu dai bara mu fara duba ta din....
Inaya sun sha raban chewing gum dan sai la'asar suka dawo sannan kowa ya kama gabansa...inaya ce ta fir daga wanka tare da shigewa daki sai da ma ta shirya sannan ta fito tace wasshhh wallahi inna munsha yawo kinga kuwa ajiye mata abinci inna tayi tace ai sai kici gashi nan dariya inaya tayi ta fara ci,inna ce ta kalleta tace kinzo kin ajiye min waya akai ta kira kinsan bansan inda zan danna ba bare na daga miki kiran amma gata nan dauki sai ki kira...
.....BAYAN SATI DAYA.....
Abubuwa da yawa sun faru a ciki harda sallamar intisar da akai sai kuma bikin ikilima da angonta..Hajiya haneefa ce ta kalle ta tace kinga abinda nake fada miki ko hajiya ai nagayamiki ni kara ma da allah yasa hakan ta faru ga magani dai yayi aiki dariya hajiya indo tai tace ai bamu gwada ba tukun na amma bara nasan da hannun nan yayi sauki za a fara aiki ko dariya dikansu sukayi tare da kallon intisar da ta fito....
Khalifa ne zaune akan kujera a dakinsa ya ziba uban tagumi yayi da hawaye ke gangarowa daga idanunsa ya rasa me ke masa dadi sallamar hajiya ce ta katsesa yayi saurin goge hawayen ya juya tare da dan murmushi kallonsa hajiya tayi tare da zama sai kuma tace khalifa sannu da hutawa kaji amsawa yayi tare da gaishe da hajiya kallonsa tayi sai kuma tai shiru khalifa ne yace mom kiyi hakuri kinji da abinda nake muku wallahi nima banasan hakan mom bansan me nakeyi ba a lokacin da na sha wannan abar mom ce ta kallesa tace to khalifa ka daina sha mana wannan wace irin rayuwa ce khalifa dai dai da mahaifinka pishi yake da kai,kai yanzu khalifa ka zabi hakan ke nan shiru yayi kawai....
Wayar inaya ce tai kara dubawa tayi sai kuma tayi murmushi tare da dauka dan gaba daya inaya ta gama sanin ikram son ta yake dan haka ita ma yanzu take biye masa sun dade suna waya dan zasuyi a kalla 30 mint sannan sukai sallama.....KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
65&66
ZUBAIR ne ya shigo gidan su intisar sallama yayi aka basa izinin shigowa shiga yayi anan ya tarar da su a falo gaishe da su yayi sai kuma ya kalli intisar yace ya jikin naki cike da kulawa tace ai da sauki dauke da murmushi a fuskarta hajiya indo ce ta tashi sai kuma haneefa ta bi bayanta suka barta anan suna shiga hanifa tace ke kinsan kuwa naga wani alamu tattare da wannan mutumin hajiya indo ce tace allah to me kika gani tabbas wannan likitan son intisar yake murmushi kawai indo ta saki tace dan allah ki ce na daina wahalar da kaina wajen ganin na hadasu hanifa ce tace ea mana taya ma hakan zai yu kawai ke dai mu tambaye ta mu ji inda aka kwana ko....
Inaya ce na hanga sai tafiya take cikin wasu sabuwar unguwanni dai dai gidan ahmad naga ta tsaya sai kuma ta fara knocking mai gadin ne ya bude ya leko cike da ladabi inaya ta tsugguna har kasa ta gaishe shi amsawa yayi sai kuma tace dan allah baba zeeya tana nan dan washe baki yayi yace eaa yarinyar shigo to,shigowa tayi tana kallon gidan tin daganan tasan gidan akwai kyau..
Hajiya indo ce suke sallama da zubair yayin da intisar ta tashi domin taje ta rakasa,hanifa ce ta kalleta tace kinga ba dama ai na gaya miki wayar hajiya indo ce tai kara kallon wayar tayi sai kuma kawai tai banza da ita hanifa ce tace bazaki daga wayar bane tsaki taja tace wallahi abinne ya fara bani haushi ace alhaji bazai dawo ba sai dai kullin bashi da aiki sai kira a waya haba ni fa na fara gajiya hanifa ce tace to ko shima wajen bokan zamu kaisa hajiya hanifa ce tace aa wannan ma so nake naga na rabasu kawai shisa na kai kaina amma nikam anya hanifa ba farraku zan sa ayi musu ba kuwa hajiya Hanifa ce tace kuma dai...
Har falon wannan tsohon ya rakata tare da yi ma ta iso da shigowa ciki zama tayi shikuma ya tsaya yana kwala kiran hajiya fitowa zeeyah tayi sanye da abaya blue da ratsin golden tace aa baba nace ka daina kiran hajiyar nan ko sai kuma tayi turuss ganin inaya a gabanta, ai da sauri ta karaso tare da dafata tana fadin aa wa nake gani ne kamar inaya dan murmushi inaya tayi tace ai kam dai ni ce wallahi,mai gadin ne ya fita ganin ta gane ta ya bar musu dakin.... zeeyah ce tace shine kuma kika ki zuwa biki ko sai intisar ce tazo dariya ta danyi sai kuma tace kai kema zeeyah yanzu ba gasji nazo ba tabe baki tayi tace sai da na shiga wata na 4 ba zaro ido inaya tayi tace yanzu har anshiga wata na hudu kenan,zeeyah ce ta bata amsa ba gashi ba kuwa tashi tayi ta nufi kitchen din dake falon sai gata dauke da katon tray a hannunta, zama tayi tana zuba mata jellop din taliya taji kifi sai kamshi take badawa sunayi suna hira abinsu inaya ba ita ta baro gidan ba sai wajen 3 itama dan tace zataje kasuwa amma sai magiya take mata akan ta dawo watarana....
Intisar ce ta shigo fuskar nan sai murmushi take zubawa zama tayi sai maganar indo taji tana intisar wai nikam meye tsakaninki da wannan mutumin amsa ta bata tana kallon gefe tace ya taba cewa yana sona amma ni gaskia ba shi nakeso ba ina da wanda nakeso kallon kallo akayi tsakanin hanifa da indo sai kuma ta ci gaba amma nasan har yanzun so na yake wayar ta ce tayi kara ta tashi da hannunta a sakale ta dauka ta wuce zuwa dakinta....hanifa ce tace indo me na gaya miki na gaya miki son juna suke to yanzu dai gashi nan ai kin gani ko dan haka sai ki gaggawar daukar mataki idan ba haka ba wallahi ta barar mana da damarmu dan wannan gayen da gani akwai naira fa hanifa ta fada tare da mikrlewa tsaye tana jan mayafin ta...
Khalifa ne zaune a falo shi kadai islam ce ta fito kiranta yayi tazo ta zauna bude baki yayi yace islam kiyi hakuri akan abinda ya faru waccen satin kinji islam ban san hakan zata faru ba amma dan allah kiyi hakuri,murmushi kawai tayi tace kai yaya khalifa ya wuce ai ok ya furta tare da fadin kawo mini abinci to kinji to tace ta tashi kawai ta nufi kitchen.....KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU
Chapter 28 · 0% Book details