← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 34

Sashe 32

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zubair ne ya fito yana kokarin cire safar hannunsa,matsawa yayi kusa da alhaji aliyu tare da furta kawu kayi hakuri nan da yan awanni zai farfado ba wani ciwo yaji sosai ba idan ka cire ciwon hannunsa to dik ba wani ciwo,alhaji aliyu ne ya kallesa tare da furta nagode zubair amma kai kasan yarinyar ko eaa zubair ya bada amsa,alhaji aliyu ne ya zauna tare da cewa fadamin yadda abin ya kasance, zubair zama yayi shima tare da bawa kawu labarin yadda abin ya faru,sai kuma ya mike tare da nuna masa kofar wani daki yana cewa waccan ita ce mahaifiyar inaya,alhaji aliyu ne ya kalleta sai kuma ya dawo da dubansa kan zubair yace shikenan ka kula da ita dik abinda ya dace kayi mata ni zan bada dik wani abu da ake buqata,kana da hotan yarinyar ya jefowa zubair tambaya,girgiza kai yayi,inam ce tace uncle ni ina da ita kituran ta whatsapp yanzun nan,ficewa yayi daga wajen tare da zuwa harabar hospital din dialing number yayi ana dagawa bayan sun gaisa ya furta case na sace yarinya kuyi iya kokarin ku akai, ka duna na tura maka da hoton yanzu, dan allah asan dik yadda za ayi wajen nemota kit ya kashe wayar ya dawo yana zama wayar sa na kara Kallon ta yayi yaga daga campany ne sai a lokacin ne ma ya tina da ganawarsa,kallon in'am yayi yace in'am ki kula da yayanki ni yanzu ana jirana a campany nan da awa daya zan dawo toh kawai ta furta, ya tashi tare da kallon mahaifiyar inaya ta window ya wuce, zubair ne ya kalleta yace in'am ki shiga dakin kinji to kawai tace ta tashi ta nufi dakin,beds biyu ne sai taga hudu dakin ba kowa sai ikram a gefen gadon ta zauna,tana kallon fuskar yayan nata da aka nade saman kan da bandage.

Hafsat ce ita kadai dai tayi shiru kamar kullun,ni wannan lamari yana bani mamaki fa akan intisar,kar dai abinda naji suna tattauna wa ne shi ne ya faru,idan kuwa har shine to tabbas mahaifiyar intisar bataiwa intisar adalci ba, intisar tabbas tana son inaya da kwanace amma gashi ta lalata kawancen ta hanyar bin bokaye da malaman tsibbu,wannan wace irin uwa ce haka ya allah kasa ta gane ta daina abinda take amin.

Hajiya ce ta kalli alhajin tana share kwallah tace yanzu wannan hukuncin kana ganin yayi dai dai,to hajiya idan ba haka nai ba ya kikeso nayi da khalifa,amma nayi magana da wani malami akan za a dinga karbowa khalifa rubutu domin ni wannan shaye shayen bana sansu,na tabbata hakan zai taimaka matuka,kar ki manta na turashi England domin yaje yayi karatu amma daga karshe kalli abinda ya koyo, dabiar shaye shaye nidai hajiya abinda nakeso da ke shine kawai ki ci gaba dayi masa addua na tabbata zai dawo da yardar allah,domin adduar uwa karbabbiya ce da haka ya tashi kawai ya bar dakin, bai dade da fita su haseena suka shigo tare suma da kwantar wa da mahaifiyar su hankali akan batun dan ta khalifa.KAWANCEN MU
Writing and Story
Waleedah Muhammad
AUNTYNNMU

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
81&82
Inaya haka ta kasance a cikin wannan dakin bayan hasken yana nan a taje taga glass din wajen dazu yana motsi idanunta na wajen, sai dai me tarr taga hoton intisar a jiki tana mata murmushi wata zabura inaya tayi tana ja da baya tana kallonta tare da saka kuka tana furta ke ce, ke ce dama intisar tabbas kin cuceni, tsawa intisar ta daka mata tareda fadin ki min shiru mana aikin banza kawai, inaya wallahi banyi niyyar cutar da ke ba ke kika siya da kudinki inayace ta share hawayen fuskarta tace to ni mai nai miki ne ki fadan me nai miki, wata gawurtacciyar dariya ta saki tace Inaya wallahi dole ne na sace ki, kuma kinsan bazan taba sakinki ba har abada sai dai waccan gyatumar taki ta mutu a banza, zaro ido inaya tayi ta durkushe a wajen tana kuka tana furta wai intisar me nai miki me na aikata miki, kawai dan na kasance talaka shikenan sai ki dinga yi min abinda kike so,kinsan fadana ni da ke ne ba da mahaifiya ta ba, intisar idan kina kaunar annabi ki sakeni, tsaki intisar ta ja tace sai ki yi kuma ko ba ni ba mhhh kina wasa da intisar kit wajen ya bace wani irin kuka inaya ta fashe dashi,juyawa tayi taga ruwa na zuba tashi tayi tare da dauro alwala,ta dawo kuma ta zauna.

In'am na zaune taga ikram na motsi saurin tashi tayi tare da zuwa ta kira zubair, tana fitowa sukai kicibis da zubair din alama tayi masa ya gane abinda take nifi,binta yayi suna shiga suka tarar da shi a zaune yana kokarin cire ruwan jikinsa, dakatarda shi zubair yayi yace wai meye hakan ikram dago jajayen idanuwansa yayi ya kallesa yace haba Zubair ya kakeso nayi kasan wane irin so nake mata, tin kallon farko da nai mata nake jin sonta a jinin jikina, da ba dan kowane bawa yana da kaddararsa ba da nayi fatan ni aka sace ba itaba in'am ce ta fashe da kuka tace yaya ikram sai kuma tayi shiru kallonta yayi yace ina jinki me zaki ce kanwata, zubair ne ya lallabasa tare da basa labarin dik abinda kawu yake akan lamarin a haka ya kwantar da hankalinsa.

A haka rayuwa taci gaba da tafiya mahaifiyar inaya jikinta dai yaki sauki domin kullun jiya iya yau a kalla an dau sati daya amma ba labari akan inaya, dik da ikram na iya bakin kokarinsa wajen nemota amma abu ya citira,a bangare daya kuma intisar ta kamu da son zubair shima kuma yaji dadin hakan tinda har yana sonta da gaskia soyayya suke, har lokacin intisar bata saki, inaya ba ko tausayin ta bata ji, ikram ya rame yayi wani baki ba inda yake zuwa kullun yana gida,khalifa yanzu dai da yaga ba kayan shaye shayen ya daina sha ya zamana sai dai yaci abinci, sannan ba a budesa sai an tabbatar yayi bacci sannan za a ajeye masa abinci da kuma rubutunsa na wajen malam a haka komai yake tafiya, indo da hanifa sunyi nasara akan soyayyar zubair a zuciyar ta.

Kamar kullun yauma tana farkawa taja kunshin ledar dauka tayi abinci ne ci tayi sannan kuma sai ga intisar ta bayyana a jikin bangon dakin,kallonta kawai tayi tace gaskia ne inaya dik abincin da kikeci amma kullun jiya iyau ba kya kara komai,inaya ce tace dan allah kiyi hakuri ki sakeni murmushi tayi zan sakeki amma da sharadin cewa tabbas bazaki fadawa police ni ce ba da sauri ta daga kai wata dariya intisar ta saki tace ai shikenan sannu mahaukaciya kittt komai ya bace haske ya dauke,cikin duhun take lalube,can kuma taga hasken fitala daya a wajen.

Hafsat ce tai sallama a gidan su intisar amsawa intisar tayi, shigowa tayi ta zauna tana zaune sai kuma ta kallii intisar bayan sun gaisa tace nikuwa ina umma ne, ta fita intisar ta bata amsa, hafsat ce ta juyo ta kalleta tacewai nikam intisar kinsan da batan inaya kwata kwata an nemeta an rasa wai,eaa haka nima naji, hafsat ce ta kalleta tace wai intisar me ye hakan kin manta wacece inaya a wajenki, cikin daga murya tace wacece kuwa banda banza, yar talakawa shashasha, wadda batasan me take ba, hafsat ce tai murmushi tace amma da ai a haka kike kawance da ita, tashi tsaye tayi tare da wanke hafsat da mari karki kuskura ki kara hadani da ita,cikin jin zafi hafsat ta rike kuncinta tace ni kika mara dan na fada miki gaskia ko intisar, to bari kiji ni nasan wani sirri wanda baki sani ba idan har kin kara ganina a gidan ku dan allah ki harbe ni aikin banza ficewarta tayi tabar gidan..

Cikin duhun daren garin dai dai kofar gidan hajiya hanifa naji wani irin gurnani shiga nayi har dakin hanifa take na ganta ta hada gumi,ga wani zabura da sambatu da takeyi wata murya naji mara dadin sauraro tana fadin idan har baki karya asirin da indo tayi ba to ki sani ke naki burin bazai taba cika ba, na hango hakanne daga cikin littafi na dan haka sai ki san yadda zakiyi, zabi ya rage naki hanifa,zumbur ta mike tana mai shre gumi tare da furta mai hakan yake nufi kenan.KAWANCEN MU
Writing and Story
Waleedah Muhammad
AUNTYNNMU

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
83&84
In'am ce ta fito da plate a hannunta dauke da kayan marmari,a kwance tagansa akan kujera ya rufe idanunsa kamar mai bacci, matsawa tayi tare da taba shi tana mai cewa yayana tashi kaci fruit, din nan yanzun nan na hada maka sabida naga baka ci komai ba yayana,kallonta yayi yace in'am na koshi fa dan allah ki kyaleni, yayana indai inaya ce za a ganta amma ka tashi kaci fruit din kaji, tsaki yaja tare da furta in'am nace miki na koshi fa haba wai dura min zakiyi ne shiru in'am tayi can kuma kamar a mafarki yaji shasshekar kukanta,tashi yayi tare da kallonta sai kuma ya kara rungume ta yana mai fadin yi shiru, kiyi shiru kinji in'am cikin kuka take magana yaya ikram so kake kaima kenan kabi su momma da abieeh ko shikenan yayana ka zabi kai wa kanka horon yunwa, yaya idan ka tafi ni kadai zaka bari, dan allah yaya kada ka tabi ka barni, shhhish in'am yi shiru ba inda zani kinji, yaya na kai kadai ne kasan momma da abieeh ni bansan momma ba amma kunce nasan dad yaya momma sai a hoto nake ganinta fa, shi kuma dad kunce yana kama da uncle ko katseta yayi yace yi shiru mikomin plate din share hawayen, ya hakuri tashi tayi tare da miko masa tana mai goge hawayen din ta...
Chapter 32 · 0% Book details