← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 34

Sashe 16

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
33&34
Ikram ne ya fito sanye da wata dakakkiyar shadda sky-blue kai da kaga dinkin kasan ansha naira mukullin mota ya dauka ya nufi harabar gidan mota ya dauka wata black sannan yayi horn gateman ne ya bude masa gidan asa kai ya fice....
Inaya tana zuwa makaranta ajinsu ta nufa tana shiga kawai sai ihunsu taji suna kuda wajen kwadayi akan mutu amma batayi musu magana ba ilham ce tai musu magana wai ku meyasa kuke haka haba dan allah wannan ba dacewa bace ba inaya kuwa shuru tayi kawai ta zauna kusa da ilham suna gaisawa malam ne ya shigo ajin sai da ya kalli inaya sannan ya kau da kai gefe aka fara karatu.....
Hafsat ce suke gaisawa da umma da murmushi ta amsa tana aa su hafsat ansha biki kinga ke harkin fi kawarta ki itafa ko tashi batayi ba balle tai shirin makarantar amma ina zuwa bara na taso miki ita murmushi hafsat tayi tace to umma ce tsaye akan intisar tana tashinta da kyar ta motsa umma ce tace ke ki tashi ki shirin makaranta ga hafsat can ta biyo miki firgigit ta tashi zaune tana raba ido tashi tai toilet din dakin ta nufa tai wanka ta fito hafsat na zaune suna hira da umma sai ga intisar ta fito break tayi suka dau hanyar makaranta intisar na shirya muguntar da zatayiwa inaya hafsat na zugata.....
Karatu ake a lokacin malamin har ya fita sai kuma ya dawo kallonsu yayi yaxe inaya muktar amsawa tayi sai yace ki sameni a office to tace ta tashi ta bishi su intisar ne suka shigo ajin ita da hafsat inda inaya ta tashi nan intisar ta zauna ilham ce tace kai intisar wajen fa inaya ne kallon banza ta watsa mata and so what dan wajenta ne ke banason iskancin banza mana ilham kuwa kuluwa tayi ta mike tare xa fadin ke karki rainamin hankali mana ni fa ba inaya bace ni zaki na gayawa magana idan kudi kike takama dashi kinsan dai ubana ya taka ubanki ko dan be careful banason shirme ganin ta bude mata wuta yasa intisar mike wa tana dariya ke ma fa wasa nakemiki haba ilham a lokacin inaya ta shigo ajin kallon wajen zamanta tayi taga intisar a tsaye batayi mata magana ba kawai ta nemi wani wajen ta zauna tayi shiru malam ne ya shigo yace kowa ya dakko kawa'idinsa kowa ya dakko banda inaya datayi shiru shima kuma bai bi ta kanta ba......
Ikram ne zaune akan kujerar dakin gefe daya kuma wata mai kama dashi ce ba ta inda ta baro sa kana kallonta kasan tana da jibi da shi murmushi tayi tace my bro nifa nagama secondary amma dai zaka kaini poland din ko zaro ido ikram yayi haba in'am poland pa aa karatunki ya tsaya iya kasarnan kinji dan turo baki tayi ta kallesa nidai nidai my broz sallamar wani dattijo ne kai dagani kasan boko ta zauna anan ya sata mikewa tare da fadin my inkun gama zanzo mukarasa ta ficewarta....
Tsohonne ya numfasa ya kalli ikram yace ikram ya kamata fa kazo ka karbi dukiyarku kaci gaba da kulawa da ita kaga yanzu a kalla akwai campanies har 5 wanda ba wani tsayayyen manager da zamuce muna dashi kazo sai ka ci gaba da kula wa dasu ikram yana kasa yanajin bayani dattijon can kuma yace baba shikenan yanda kace haka za ayi zan karba sauran kuma insha allah zamu saka muna neman ma'aikata kaga daganan sai mu tantance shikenan Muhammad allah yayi maka albarka amma ya kamata ka fito da matar aure dan murmushi yayi yace to insha allah baba babanne ya kallesa yace ai dama kullun haka kake cewa yawwa ya maganar karatun in'am wai naji tana poland zata karka sake ka biye mata nadai fadamaka dan murmushi yayi yace dama baba bazan biye mata amma kuma ina neman alfarma a wajenka shikenan inajinka menene ikram ne ya gyara zama ya fara zubawa baba bayani....
Tafiya inaya take yayin da hafsat da ikram ke binta a baya Ibrahim ne ya fito daga mota ya tareta sai da ya kalleta yace inaya harkin dawo murmushi tayi eaa wallahi Ibrahim ya gida ya aiki amsawa yayi alhamdulillah anjima idan kina free zanzo kinji shikenan sai kazo cewar inaya ta kara gaba dik abinda akeyi akan idon su hafsa intisar ce taja hannun hafsat suka matsa kusa da shi a lokacin har ya shiga mota intisar ce tai masa knocking daga glass din yayi ya kallesu tare da furta lafiya dai fari hafsat tayi tace munaso muyi magana dakai ne akan inaya ok fitowa yayi ya tsaya kawai intisar ce tace naganku da inaya lafiya dai ko kallonta yayi yace budurwa tace kallon juna hafsat da intisar sukai ok bara mufada maka wani sirri wanda baku sani ba cewar hafsat intisar ce ta karbe kasan dai waccen yarinyar bakuwa ce ko to kasani yar tasha ce ko ma nace maka yar bariki ta zubar da ciki yafi sau 10 kuma yanzu haka tana dauke da cutar kanjamau ko nace maka HIV kai ko ubanta ba'a sani ba bare dangin ubanta zaro ido Ibrahim yayi yace to ke taya akai kikasani dan murmushi tayi tace karkai mamaki saboda nidin kawata ce ita saboda wannan halin ne yasa muka rabu da ita kaji dalili hafsat zo mu tafi jan hannun hafsat tayi suka fice..........
Ikram indai wannan ce matsalar bakomai insha allah zan shirya muje gidan amma sai zuwa asabar dan ranar ne kadai nake da tyme shima kuma daga karfe karfe 5 ne na yamma dan haka sai muje ko da magariba ne to baba shikenan alah ya kaimu nagode sosai dattijon ne ya kallesa yawwa ikram allah yayi maka albarka tabbas ka biyo halin iyayenka allah ya bada lada Ameen ikram ya amsa shikuma baba ya tashi yana fita yayi dialing number in'am......👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷
Chapter 16 · 0% Book details