← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 44

Sashe 7

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A6angaren ya Umar kuwa ransa a6ace yashiga gidan, inna data fito daga d'akin baba mahaifinsu Asma'u ta ce, "a'a Umaru kaine agidan?.
Murya acinkushe ya ce, " nine Inna, sannu.
Yauwa Umaru, amma yanaga kamar Ranka a6ace yake?.
Da sauri ya saisaita nutsuwarsa, shikansa yana mamakin yanda baya iya 6oye Bacin ransa idan yaga Asma'u da saurayi, kuma aii hakan bata faruwa akan Mufida kosu fatee, wata zuciya ta ce, "aigara Mufida tayi girma tunda tana 100L a jami'a, amma Asma'u fa SS 1 take a secondary........
Innace ta ta6ashi, firgigit yadawo daga duniyar tunani, ta ce, " tunaninmi kuma kakeyi Umaru?.
Cikin inda-inda ya ce, "babu komai Inna wani albishir Nazo miki dashi, amma mi Asma'u yakeyi awaje da safennan?, mima yahanata zuwa makaranta.
Dariyace taso kufcema Inna saboda hango kishi k'uru-k'uru a idanun Umar, amma saita dake tace kasan suna Exam, toyau basuda ita shiyyasa, wancan kuma Zayyanne wai zaiyi tafiyane shine yazo suyi sallama.
Kansa kawai yagyad'a amma bai iya cewa komaiba yamik'e yana fad'in bara nagaida baba.
To kashiga yana ciki.
Ak'ofar d'aki yayi sallama, saida aka bashi izinin Shiga sannan yashiga.
Baba na zaune yana karin kumallo Umar yashiga, cikeda fara'a yataresa, Fharuku kaine agidan namu?.
Nine baba ina kwana?.
Lfy lau Umar ya hidimomin duniya?.
Alhmdllh baba.
To masha ALLAHU, kaga matso muci abinci ko?.
A'a wlhy baba nakarya nikam.
Kai Umaru karfa filako kakeyi?, a'a baba yazanyi filako agidanmu, nak'oshine kawai, to shikenan, yawajensu Maman taku?, lfy lau suke baba sunama gaisheku, a muna amsawa wlhy.
Umar yamik'e to baba bara naje mugaisa da Inna natafi wajen nema.
To Umaru ALLAH yabada sa'a kaji, ayitadai hak'uri da yanayin rayuwa, duk Wanda kaga yayi hak'uri baici ribaba to d'an kad'an yayi, duk abinda ALLAH ya albarkaci mutum dashi karya raina yace Alhmdllh, to insha ALLAHU ALLAH zaibasa mafiyinsa agaba kajiko?.
To baba ngd sosai, ALLAH yak'ara yawancin kwana.
Ameen Umaru ALLAH yayi albarka kuma.
Amen summa ameen baba, naira 500 ya ajiyema baba, baba ga wannan asha fura.
Kai a'a Umaru zoka d'auki kud'inka kaji, nikam bazan kar6aba, airik'e kankuma dakukeyi abin alfahirinmune basai kumbamu ko sisiba.
Hhh baba Dan ALLAH ka kar6a kasamusu albarka, nima banisu akayi.
To shikenan Umaru ALLAH yak'ara bud'i na alkairi ngd sosai.
Babu komai baba Umar yafad'a yana ficewa daga d'akin.
d'akin Inna yashiga, azaune yatadda ita tana jiransa, yasamu waje yazauna suka k'ara gaisawa da tambayar lfyar juna.
Alhmdllh Inna sai godiyar ALLAH.
To aii haka akesonji Umaru, wanekuma albishir aka kawo mini?.
Murmushi yayi tareda gyara zama yazayyane mata komai tundaga jiya har safiyar yau.
Farinciki sosai Inna ta Nuna harda kukan dad'i, tashi tayi tagad'oma baba shima yayi farinciki sosai, har d'akin inna yashigo yataya Umar murna da wanan k'yauta.
Suna cikin farincikinsu saiga Asma'u tadawo hannunta d'auke da Leda.
Itadai kallonsu kawai takeyi, data kasa jurewa saita ce inna wai miya farune kuketa murna haka?.
Inna ta zayyane mata komai, itama sosai tanuna farincikinta akai, ya Umar kam sai antaya mata haarar yakeyi, ko a jikinta wai antsikari kakkausa.
Bayan sun gama murnar yatashi yatafi akan zaidawo gobe yanuna musu motar.
To d'an Albarka, ALLAH yayi albarka kaji.
Ameen inna saina dawo.........

Daganan sai gidan Anty sa'a, ita kad'ai yatarrar agidan Dan yara suntafi makaranta, tamik'e da k'yar saboda tsohon cikin dake jikinta, oh ni Umar dama kana duniya?.
Dariya yayi ya ce, "Anty Sa'a ina zanje?, hidimomine kawai sukaimin yawa.
Haka kuka iya kullum kaida Abubakar da Harris bakwa rasa uzuri aii.
Tab Anty aii garani da wad'annan, kema kinsan ina k'ok'arin zuwa wajenki fiye dakowa agidanmu.
Eh to hakane kuma, amma aii kaima wani lokacin saika 6ace 6at.
'Yar dariya yayi ya ce, " hakadai kikace Anty sa'a.
Oh hakama zakace?, Anty sa'a tafad'a tana fita daga falon.
Babu dad'ewa tadawo d'aukeda tire shak'e da kayan ciye-ciye.
Da sauri Ya Umar yamik'e yatarota, kai Anty yakamata ki saukema kanji irin wad'annan aiyukan, ai kinyi nauyi dayawa.
Zama tayi da dabara, shima ya ajiye tiren sannan ya zauna.
Ta ce, "k'anina yazanyi, aii dole natashi nayima kaina, 'Yar mai aikin dake taimakamin kakarta tarasu taje gida tun shekaranjiya, jabeer da Laila kuma mizasu iyamin inbanda su 6ata.
To da wannan Dan wannan kuma, amma gsky mata kuna bani tausayi matuk'a, koda rainon cikinnan kad'ai akabarku aiba k'aramin k'ok'ari kukayiba, balle ga haihuwa, raino, tarbiyya dukfa suna kanku, kai ALLAH yasaka muku da aljannadai.
Amin d'an k'anina, Anty sa'a tafad'a tana dariya.
Shima dariyar yayi yana kai kofin zo6o bakinsa, saida yasha sosai saboda k'aunarsa da zo6o sanan ya ce, "big aunty dawani daddad'an albishirfa nazo miki.
Tofa k'anina ko ansami matar aurene?.
d'an tsaki yayi ya ce, " Anty wane matar aurefa, aii aurena banan kusaba kuma dainamin zancensa.
Umar kanka d'aya kuwa?, wai sokake saika tsofe agidane?, shekararka fa 28 yanzu, amma ace babu aure agabanka?.
Hummm Anty sa'a kenan, Ku kawai auren kuke ambata, amma bakwa tunanin inda mutum zai ajiye matar, abinda zataci, Wanda zai mata sittira dakuma matsalolin yauda kullum musamman na rashin lafiya dakanzo tamkar ha6o.
Hakane Umar amma aii duk ALLAH ne mai komai da kowa ko?.
Hakane Anty ALLAH yasa mudace to, dama albishird'in nawa shine..................tas ya zayyane mata komai.
Saboda farinciki jitake kamar tatashi taita tsalle, ta ce, "ALLAH sarki Umar kaga ribar hak'uri ko?, lallai yau nayi farinciki sosai, ALLAH yasa iyakar wahalar kenan.
Amen Anty sa'a ngd.
Sund'an dad'e suna hira sanan yatashi yaymata sallama yatafi.
Daga nan aikinsa yatafi, yau cikin d'unbin farinciki yakeyin komansa har zuwa dare daya koma gida.
Yaukam dawuri yakoma gidan Dan ana isha'i yakoma.
Afalo ya iske mutanen gidan suduka, har yaya Abubakar yazo, suka gaisa Harris da su mufidama suka gaisheshi, mamadai ta had'e masa gabas da gamma, amma wanan bai hanashi gaishetaba.
Kamar yafad'a musu saikuma yayi shiru da bakinsa, and'anyi hira ya Abubakar yatashi yatafi, shima Umar mik'ewa yayi yamusu sallama yatafi d'akinsa, ganin haka Harris ma yamik'e akabar mama da 'yan matanta..........

*_(((S)))........2017_*
*_luv you all_*🤝😻.
[11/23/2017, 4:57 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*

*_Gaisuwa da fatan alkairi agareku, Action baby & Maman Khaleed, alkairin ALLAH yakai muku aduk Inda kuke, ALLAH yabar zuminci, INA alfahari daku😻😍❤👌🏼._*
*_page→13-14_*

........washe gari Umar yay shirinsa, kamar yanda yasaba yalek'a ya gaida mama, dukda bata wani amsa masa yanda yakamataba amma hakan bai damesaba yamik'e yashiga d'akin Abba shima ya gaisheshi, baisake bin takan kowaba yafice abinsa sai gidan Alhaji.
Yau har ciki mai gadi yabarsa yashiga da Babur d'insa, yananan tsaye saiga baby tafito yaudai tayi kwalliyarta sa6anin jiya dayasameta cikin kayan barci.
Cikeda rangwad'a tak'araso garesa, Umar yajanye idonsa daga kallonta, Hii my guy, tafad'a tana dafa adaidaita sahun.
d'aure fuska Umar yayi, ko kallonta baiyiba barema tasamu amsa.
Abin ya6ata mata rai, amma saita dake, ta ce, "sorry Assalamu alaika.
Sai yanzu Umar yajuyo fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, " wa'alaikissalam.
Murmuahi tamasa tareda fad'in dama haka kake babu sauk'i?.
No bahaka bane, yadace duk inda d'iyan musulmi yashiga farko yafara sallama kafin yasamu damar aiwatar da Abu nagaba, ina fata daga yau zaki gane kuskurenki ki gyara.
Tayi far da idanunta, cikin sanyin murya ta ce, "kayi hak'uri zan gyara insha ALLAH.
Wani murmushin daya kasheta yamata, talumshe idanunta domin jin wani dad'i ya ratsa zuciyarta, bata dawo daga magagin shauk'in so ba muryarsa tadaki kunnenta.........
Wai miye cikakken sunankine?, nasandai baby ba suna baneba......
Da sauri taware idanunta akansa, cikeda salo ta ce, "sunan Lubna."
Shima maimaita sunan yayi a la66ansa, ya ce, "lubna!, nice name.
Cikeda jin dad'i ta ce, "da gsk?.
Kansa ya jinjina mata yana murmushi.
Wani uban tsalle tayi Wanda yasakashi tsayawa kallonta, ngd ya Umar I love you wlhy.
Umar kam yadaskare atsaye, mamakinta yakeyifa, tun jiya take ambatar kalmarnan akansa, amma yagaza gane inata dosa......... Muryar alhajice takatse masa tunaninsa, Umar kayi hak'urifa baby tacikaka da magana.
Murmushi Umar yayi ya ce, "babu komai Alhaji aii muna gaisawane.
Duk'awa yayi yana gaida Alhajin, Alhaji ya amsa yanamai kamasa ya tadashi tsaye, Lubna tazo saitin kunnen Dad d'inta tagaya masa wani Abu danima banjiba.
Dariya dad ya ce, " baby da gsk koda wasa?.
Dad serious wlhy, tarufe idonta.
Masha ALLAH babyna ALLAH yatabbatar mana da alkairi, kisa aranki kinsameshi kinji, kanta tagyad'a tanamai farinciki, shidai Umar dabaisan miye zancen nasuba kallonsu kawai yakeyi.
Chapter 7 · 0% Book details