← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 44

Sashe 44

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-
Asma'u dake zaune Afalo taci wwalliyarta, gefenta masu aikintane suna zaune sai hira Duke zuba mata tana dariyar. It's babu ruwanta da German kan nan irinna hajiyoyi.
Da gudu fodiyo da Batul suka shigo falon suna kiran Ammi! Ammi!! Mundawo mundawo.
Itama cikin azama tamik'e ta taresu Rana farincikin dawowar 'ya'yanta ababen alfaharint.
Suna cikin murnar saiga ya Umar yashigo d'aukeda Affan ahannu, shima sanye cikin Mayan makaranta.
Shida Affan d'in tahad'a ta rungume tsam ajikinta, shima ya Umar k'yak'yk'yawar tarba yamata tareda manna mata Sumba agoshi.
Affan ya ce, ammi yau antynmu tace Nafi kiwa kokali a class d'inmmu.
Masha ALLAH autana, haka nakeaonji.
Ya Umar ya ce, ''autan lfy hajiyata, idanmma zaki dage ki Dage, autana bai zoba har yanzu, shine zaizama k'anin Affan na tara.
Sosai Asma'u tazaro ido, gaba ya Fharuk rufamin asiri mana, ukunnan ma aii ansha fama kafin suzo.
'Yar dariyar ya Umar tayi, ya ce, "ahaka kuma nake jiran tara nan gaba.
Habadai wasa kakeyi wlhy.
Said a suka zauna sannan yace babu wani wasa da gsk nakeayi.
Shiru tamasa taje takawo masa abinsha, sannan tafara cirema Affan Mayan makarantar.
Suma su fodiyo duksun cire, kowa yama k'ok'arin nuns mata homework d'in da aka basu, sukaji sallamar yazeed.
Yaran kowa ya yard a abinda ke hannunsa suka kwasa da gudu suna fad'in oyoyo dady.
rungumesu yazeed tayi, shima yama fad'in oyoyo yarana.
Ya Umar da Asma'u dai kallonsu kawai sukeyi suna dariya.
Lubna dasu Amrah kam suna baya said kalle-kalle sukeyi agidan.
Saima yanzu su Asma'u suka gansu.
Ko kad'an Asma'u bata gane lubna ba bare su Amrah.
Amma kuma kamar dasukeyi dashi yasakata taura musu idanu.
Shikam ya Umar suna shigowa yaganesu suduka, Dan d'azu yaga Afrah da Amrah a mall d'insa tareda wasu samari biyu. Kuma yaji ajikinsa 'ya'yansane. Har hawaye saida tayi alokacin, yana k'ara yima Lubna ALLAH ya Isa, Dan asanadinsa yaransa suka lalace, shidai bai ta6a Yar kowaba tunyana saurayi bare yanzu.
Amma gawasu suna lalata 'ya'yansa ta dalilin halin ma haifiyarsu.
Yazeed ne yacema su Lubna su zauna.
Duk suka zazzauna.
Asma'u takawo musu abubuwan motsa Baku.
Ran ya Umar a6ace yatashi zaibar falon. Da sauri yazeed yarik'e hannunsa yana fad'in karfa ka manta, a tsakaninmu babu jayayya.
Idon ya Umar yayi jajur saboda 6acin rai, yajuyo yana kallon yazeed, kayi hak'uri d'an uwana, wannan jayayyar tasha banban da wadda bakaso.
No Umar duk d'ayace, Dan ALLAH kayi hak'uri kazauna plss.
Saida ya Umar yay kwafa sannan ya zauna. Amrah da Afrah kam aii tuni sun nutsu, Dan basuga wajen wargiba.
Sudai su fodiyo suna tsaye agefe suna kallon iyayensu.
Lubna ta Haida ya Umar, bai amsa mataba. Bata damuba itama, ta kalli Afrah da Amrah tace augaidashi.
Amamakinta saigashi sun gaidaahi, harma da Asma'u.
Sumad'in bai amsa musuba, saima cikin tsawa ya ce, "Lubna! Miyakawoki gareni? Dawane shiri kuma kikazo yau?.
Tsawar babu Wanda bata razana a falonba, Affan ya k'ank'ame Asma'u yana kuka, Dan basu ta6a ganin baban nasuba a irin wannan yanayinba.
d'aukarsa tayi tana lallashi, fodiyo da Batul ma duksun mak'ale jikin yazeed.

K'asa Lubna tadiro tana kuka da neman gafarar ya Umar.
Ka gafarceni nida iyayena da 'yan uwana Umar, wlhy duniya takoyar damu hankali, munyi nadamar abinda mukaimaka. Umar yanzu bamuda abin jayayya Sakai, dukiyar damuke tak'amar da ita tak'are. Ciwo da bak'in cikin rayuwa sune suka maye gurbin arzeek'inmu.
Umar kayi hak'uri, ga 'ya'yankanan zan maido maka, Dan ALLAH karkace bazaka kar6esuba, Umar wlhy nasan nikaina ina gab da kamuwa da wani ciwonne, rayuwar dasu Amrah da Afrah suka saka kanau kawai ta Isa lafiyata baraza......
Da sauri ya Umar yad'aga mata hannu a hasale, yana fad'in suka saka kamsu, kokuwa kika sakasu ciki. ALLAH shine zaidata van ta6a zina da 'Yar kowaba amma ta sanadinki ga 'ya'yana sunayi. Lubna kin cuceni, kin zalinceni, yama za'ayi Na yafe miki?, kin rabani da 'ya'yana Ashe badan ki kula dasuba? Saidai ki watsa musu rayuwarsu? Wata 'yan kwallah ta taru masa a gefen ido......
Yazeed da Asma'u ne suka saka baki wajen taya Lubna Neman gafara.
Dak'yar ya hak'ura, Afrah da Amrah aukazo suka rungumeshi suna kuka suma. Yauce rana tafarko dasuka gane kuskuren dasukaso tafkawa rayuwarsu, ALLAH ya taimakesu ya tsaresu basuta6a bama wani saurayi kansuba, saidai soyayyar shan minti da romances da samarin sukanyi dasu.
Shima ya Umar rungumesu yayi, yau ga 'ya'yana sundawo gareshi, bayan kwacesu da akayi daga hannunsa Na tsawon shekaru.
Daga nan wajen Asma'u sukazo itama suka rungumeta, basu manta da itaba, suka rungume 'yan kannensu dabasu sansuba.
Lubna sai dad'i takeji, ga hawauenta sunk'i tsayawa, ta rungume su fodiyo itama tanajin dayanzu k'ila itace ta haifesu, amma San zuciya da rud'anin duniya yahana tsaida zuciyarta waje d'aya. Aigatanan a makarantar nadama.......

Anan tabarsu Twins kamar yanda Asma'u ta buk'at.
Aiko hakan yamusu dad'i, saijan 'yan k'annensu sukeyi ajiki, suma dayake sunada saurin sabo harsun saki jiki dasu.

Washe gari, ya Umar yaje har gidansu Lubna d'in yad'auki mom da Suhaima yakaisu asibiti.
Mom sai kuka takeyi, babu bakin magana, hakama Suhaima tanata kuka da Neman gafarar ya Umar, tasanar dashi sune itada mom sukaita zuga Lubna, akan tarabu dashi, run bata aminceba harta amince.
Ya Umar saidai kawai yayi murmushi ya ce, ''ya yafe musu.

*+++++++++++++*.
Cikin wata biyu jikinsu mom da Suhaima yayi k'yau, Dan yanzu mom nad'an iyayin magana kad'an ², dukda dai bata fita sosai, hakama Suhaima alhmdlh, jikin nata yayi, k'yau.
Mom sai sakama Ya Umar albarka takeyi da k'ara Neman gafararsa.
Koda yaushe yakance ya yafe musu.
Asma'u kam bata ta6a gazawa wajen kawo musu abinciba kullum safe da yamma.
Duk sanda Lubna ta gansu dasu da 'yan 'ya'yansu saitayi kuka, da nadama, mai makon Umar yayi baya, kullum saima gaba yake k'arawa. Tagujeshi saboda *,"karayar arzeek'i"_* yau gashi shine yake taimakonsu da dukiyarsa.
Tayi kuka harta godema ALLAH, tayi nadama rayuwarta, shiyyasa akace idanu gemun d'an uwana Yakama da wuta to yayyafama naka ruwan. Idanu kuma ALLAH ya jarabci bawansa badan bata sonshi baneba.
Itakam taga zahiri akan Umar.
Itada 'yan uwanta kam duk ga yanda tasu rayuwarsu tak'are, sun rasa alokacin Dana Umar yadawo.
ALLAH ka shirya zukatanmu, ka ganar damu gsky.

Ni bilynku nace ameen😭.

Alhamdulilahi.

Anan nakawo k'arshen wannan d'an littafi NASA mai suna *_KARAYAR ARZEEK'I_* abinda nafad'a saidai, ALLAH kabani lada, Wanda nati kuskure ALLAH ka yafe mini.

Ina godiya ga d'umbin masoyana, musamman masu bibiyar buk d'innan Na *_karayar arzeek'i_* ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, Nina INA k'aunarku da alfahari daku aduk India kuke.

*_Writer's 'yan uwana kuma inata mik'o godiya agareku, ALLAH yabarmu tare, yak'ara dank'on zuminci, ALLAH yak'arama kowa baseeer da hak'urin typing._*

Bilkisa Ibrahim
Bilyn Abdul.

Marubuciyar.
_rashin Sani_
_auren k'addara ko biyayya?._
_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?_
_nida aminiyata_
_kukan kurciya_
_sabon al'amari_
_nawaff_
_ban saketa ba_
_Abdul-maleek bobo_
_karayar arzeek'i_

*_Sharhin littatafaina 10 nanan zuwa agareku insha ALLAHU_*

_NGD SOSAI, ALLAH YABAR ZUMINCI._

*_BILYN ABDUL CE._*👌🏼😁

*_(((S))))........2018_*
*_I love you more...._*
Chapter 44 · 0% Book details