← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 44

Sashe 40

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Nikaina 'yar rahotonku saida yawuna ya tsinke😋.

Ahankali takeci tamkar bataso, gefe kuma masu aikintane kemata tausar k'afafunta.
Wayarta dake wringing tamik'a hannu ta d'auka, ganin mai kirannata yasa murmushi fad'ad'a afuskarta.
Hello Hajja Sadiya ykk?.
Daga can aka amsa mata da lfy lau Hajiya lubna, dama kayane suka iso shine nace bara na sanar miki kafin mutane su za6e.
Wani murmushin k'asaita Lubna tayi, tareda danna tsokar nama abakinta, cikin tauna naman ta ce, "OK Hajja sadiya ngd fa, zuwa anjima kad'an zan shigo insha ALLAH, Dan munada biki satin sama.
To shikenan ALLAH ya kaimu lafiya.
Uhum tafad'a tana ajiye wayar batareda ta yankeba.
Kad'an takumacin naman ta tureshi gefe tana yatsine fuska. Bilki akaimin fruit d'innan cikin firij saina dawo zansha. Tayi maganar idonta akan 'Yar aikin dake dama da ita.
Cikin hanzari kuwa bilki mai aiki ta amsa, d'aukatayi tanufi kicin domin cika umarnin madam.

Lubna kuwa d'aki tashiga, aka sake sabon wanka, cikin shiga ta alfarma, saigata tafito rik'eda key n mota, da k'aramar handbag mai azabar kyau. Takun lubna kawai abin kallone, Dan tabbasa 'Yar gayuce ta fad'a da k'ari, komai nata mai ajine🧐.
Motarta tashige sai gidan Hajja sadiya dillaliya, amma mai lasisi, dankuwa kayane Na manyan k'asa take kawowa. babu tambayar miji atsarin Lubna, ayayinda zata anguwa, saidai yazo ya iske bata nan.
Yanzuma tana fita yana shigowa anguwar, yad'anga gilmawar motarta, amma zuciyarsa bata amince itad'in baceba. Saida yashigo harabar gidan ya faka tashi motar sannan yakula babu d'aya daga cikin motocin Lubnar. (Dan kuwa motar Lubna ak'alla takai hud'u agidan, kuma duk Na gararine da nunawa sa'a).
Baice kimaiba yanufi cikin gidan.............

*_(((S))).......2018_*
*_I Love you all my fan's_*
[1/6, 5:08 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

*_page→73-74_*

..........Babu kowa afalon sai k'arar AC dana TV. Su bilki sunacan kan sauran farfesun da Lubna ta rage sunaci itada saude.
Cikin d'akinta ya k'arasa, ko INA k'al yake, dama a 6angaren tsafta bashida Matsala da Lubna, dukda dai 'yan aiki keyi ba itaba, saman sofa ya kwanta yana k'arema ko INA na d'akin kallo, amma zuciyarsa da tunaninsa nakan ganin da sukaima Umar ayau.
Lallai suma sunsan Umar yagama kama k'asa, kuma kaf d'insu yafisu komai. Dama can yafisu d'in, ayanzuma garashi dayake auren Lubna kud'i sun k'ara zauna masa. To amma aii banasa baneba, dan yamzudai kam Lubna babu abinda bata fishiba, koda kaddarorin data samu a gadonta sun Isa ta keremasa sa'a, shiyyasa yakula take kallon kanta samadashi. Wata kwafa yayi yana kad'a kai, yakula idanfa yatsaya jiran ya huce, tofa rabon wani zai ratsa. Da sauri yatashi zaune, haryanzu yana a duniyar tunani. Tabbas a farko ya auri Lubna ne dansu bak'anta zuciyar Umar. Ammafa ayanzu tunaninsa yafara sauya akalar tafiya wani 6angare. Yatuna da maganar Kabeer alokacin dasuke kulla wazai auri Lubna d'in?.
*_tab wlhy dabadan matana biyuba, kuma ko sati biyu ban k'ullah da k'ara aureba, ga dokar da dady yasamin akan k'aro ta uku, toda wlhy nizan auri Lubna koda Umar zai mutu. Sannan ita kanta saina tatseta tas, dan fak'iriya ta gsk zan maisheta aradu kuwa. Suma aii Tara musu akayi, kunga kuwa nima saina dangwali arzik'i._*
Alokacin Hafiz babu haka kokad'an aransa, da zuciya d'aya ya amsa zai auri Lubna tunda yad'an fisu k'yau da kud'i, kaitsaye zatafi kar6arsa fiye dakiwa a majalissar.
Ya wani mik'e tsaye yana tafa hannaye, _"ni shegiya inji d'an daudu!"_ dazanma kaina sabalula, baijira wani dogon tunaniba yafara bincike ad'akin Lubna, duk wasu muhimman takardu Na filaye da gidaje Na Lubna saida ya lalubesu Tas, k'ananun kawai ya bar mata, yana gama had'awa Yakama hanyar fita, harya kai falo saikuma yadawo, wani tunanine yazo masa, baikamata yakwashe komai lokaci d'ayaba, Dan tabbas zata gane shine.
Saikawai yajuya yamaida komai, takarda d'aya ya d'auka da wasu kud'i 200k daya gani a dirowar gefen gado yafita zuwa gidan Uwargidansa, dama yau itace dashi, yazo yima Lubna sallamane kawai.

Lubna tana zaune dirshen gaban Hajja Safiya, kaya kawai taketa lodama kanta Na garari, Hajja sadiya kam saida dad'i takeji, dama tasan Lubna babu wasa, data saya zata Baka kud'inka, gashi kuma zata yaya dayawa, Dan yanzu batada babbar customer kamar Lubna.
Saida ta Lodi kayan 2millions NATA Na kanta, sannan shima Hafiz ta d'iba masa. (Yo ba ita tataraba, batasan zafinsuba, sanda aka nema tana gado tana barci hankali kwance)😎.
Aledoji Hajja Safiya ta jibga matasu, tasaka 'yan aikinta sukaita kaiwa mota, todama kayan bawani d'inbin yawane dasuba, tunda Na 'yan k'aryane, daga less d'in 300+, sai tanfar 200+, hakama gyale dukna manyanne, barema takalma da jaka, ga yari da kayan kwalli, Dan komai Hajja sadiya saidawa takeyi. Amma dukda haka saida bayan motarta da but suka cika taf, Dan Lubna nason kayan Hajja sadiya, tana siyo kaya masu k'yau da Qualities, gasu designers. Shiyyasa bata k'yashin kashe konawane ta kwashi kaya, dama ga kud'in abanza ana gani.
Sallama sukayi da Hajja Safiya taja mota tatafi, sai gida........

'Yan aikinta ta tura suka kwaso kayan amota, ta kalli bilki amintacciyar mai aikinta kenan, bilki my Sugar yazo gidannan kuwa?.
Eh Anty yazo babu dad'ewama yatafi, inaga yagaji da jiran dawowarkine.
Baki Lubna ta ta6e batareda tace komaiba.
Bilki da sauran 'yan aikin suka fice, itakuma tafad'a bathroom Dan tayi wanka........

___________________________

Safwan kaine ka iya tunawa damu agidannan haka? Kodai 6atankai kayine haka?.
Wata 'Yar dariya Safwan dake gaban mom zaune yayi, mom dama kuna raina wlhy, yanzuma muhimmin abune yakawoni gareku, amma saina k'ara hutawa zamuyi maganar.
To shikenan, ainama godema ALLAH dana ganka yanzuma, jeka huta to, bara nasa ashiryamaka abinci.
To mom, amma yanaji gidan shiru? Inasu baby?.
To ka gujemu ina zakasan mike faruwa agidanku, baby da suhaima sunyi aure, yanzu dagani sai su twins agidan.
Kai yanzunan mom su baby sunyi aure?. Amma banji dad'iba da akayi bananan, ALLAH ya sanya alkairi to. Insha ALLAH dukzanje gidajensu. Matar Ameer fa ta haihu?.
Baki mom tad'an ta6e, ta haihu amma 'yar batazo daraiba.
Ayya my bros ALLAH ya canja damai alkairi, itakuma ALLAH ya jik'anta.
Mom dai batace komaiba, amma mamakin canjawar safwan takeyi sosai, dukya canja mata, ga wata k'iba dayayi ta alamun yanajin dad'i.
Shikam d'akinsa yashige yana wata dariyar mugunta, humm mom dakinsan da shirin danazo gidanan, wlhy datuni kin korani baya, ammafa da ikon ALLAH sainaci nasara akanku.....

😨tofa Safwan dami kazo?.
Chapter 40 · 0% Book details