← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 44

Sashe 4

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanma ban hak'uraba dukanka zanyi, kashiga cikin wayar sosai insha ALLAHU zakagane idanma tawace ko akasin haka.
Shawararta yabi yashiga bincike awayar, tabbas tatace Dan hotunantama dake kai sun Isa shaida, yad'ago yana kallonta to Hajiya nawa zaki sayar?.
Kasiya yanda yadace, nidai ina rok'onka kamin adalci kawai, nima dolece tasakani saida wayar badan nasoba.
Jinjina kai yayi, ya ce, "nasiya 150k.
Idanunta tazaro waje, kai malam kallifa da k'yau kaga wayar dake hannunka.
Murmushi yayi Hajiya nagani sosai, wlhy nama saya da daraja aii.......
Kafin tayi magana wani dake kusadasu yana sayen waya ya ce, " gsky kacuceta Dan wayarnan bata sha wahalaba.
Asma'u da mamaki yakashe ta ce, nifa duk bamma fahimci inda kukadosaba, wayar dabata wuce 25k ba kuke kira mata 150k?, ahankama har ana fad'in an cuceni?.
Wanda yasaka musu bakin ya ce, "Hajiya amma dai bake kika sayi wayarnanba?.
Eh bani nasayaba, yayanane yasiyamin.
Haba shiyyasa bakisan kud'intaba, wannan wayar dakike gani, ana saidata 400k wlhy.
Idanu sosai Asma'u ta kwalalo waje, sai maimaita yawan kud'in take azuciyarta, dubu d'ari hud'ufa?, tabd'ijan, lallai ya Umar yayi k'ok'ari......
Tunaninta yakatse yayinda taji maganar labaran abayanta.
A'a Asma'u lfy kuwa?.
Lfy lau wlhy Labaran, nazo nasaida wayane.
Tofa ina wayar?.
Kaganta nan, tayi maganar tana nunama masa wayarta dake hannun saurayin.
Hannu yamik'ama saurayin yabashi wayar, saida ya rissina sannan yabashi alamar girmamawa.
Labaran yakar6i wayar ya jujjuya sannan ya ce, " nawa kasiya?.
In ina saurayin yafarayi alamar rashin gsky, labaran ya girgiza kai kawai danyasan halin yaran shagon dason zuciya.
Baice komaiba yak'irgo kud'i masu yawa yabata, Asma'u ga 330k kiyi hak'uri datayin farko dayayi mini.
Babu komai tafad'a tana murmushi, ngd sosai labaran, amma Dan ALLAH kozan samu memory nakwashe abin kan wayar?.
Babu damuwa, idan nakwashe zanbama Rafi'a takawo miki.
To ngd sosai labaran.
A babu damuwa Asma'u.
Agurguje tafice tasamu adaidaita cikeda kwarin guywa suka nufi asibitin..........

*_(((S))).......2017_*
*_luv you all my fan's_*
[11/21/2017, 4:33 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR AZEEK'I!!_*💎

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO......😜_*

*_page→6_*

.......Anshigar da ya Umar babu dad'ewa su mama suka iso, suduka sukai kan Asma'u suna tambayar jikin ya Umar d'in?.
Jikin Anty sa'a tafad'a tana kuka, wannan yasa suka k'ara rud'ewa.
Makwafcinsune yamatso, cikin hikima yamusu bayani.
Godiya sukai masa sosai, daganan aka koma zaman jigum-jigum.

*_3h...ago_*
Dr yafito shida Nurse's dasuka taimaka masa.
Shimadai rufuwa akansa sukayi suna tambayarsa jikin ya Umar.
Yabuk'aci ganin wasunsu a office d'insa, amma babu Wanda zaya iya hak'uri abarsa abaya, Dan haka suka tafi suduka.
Dr bai hanasuba saima gurin zama daya nuna musu.
Kowa yasamu waje yazauna yanajiran bayani, bayan Dr yagama 'yan rubuce- rucensa yad'ago yana kallonsu, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Alhmdllh, gsky Ku k'ara godema ALLAH akan taimakon daya bama Alhaji Umar danba kowane yake irin fad'uwarnan yatashi dai-daiba, amma shi Alhmdllh babu wata Marsala, saidai yana cikin matsannanciyar damuwa wadda saida taimakonku aikinmu zaikai ga nasara, yanzudai yasamu barci kuma bazai farkaba harsai nanda 24h Dan munaso zuciyarsa tasami Hutu sosai.
Yanzu ga wannan zakuje kubiya kud'ad'en sannan kuma asayi wad'annan magungunan kafin ya farka.
Atare sukace to Dr mungode sosaifa.
Karku damu aikinane.
Godiya suka masa sannan suka fita.
Suna fita Mama ta kalli ya Abubakar, ta ce, " Abubakar saika amshi takardun kaje kabiya kakuma sayo magungunan ko?.
Fuska ya murtike tamkar zai fasa kuka ya ce, "to kuzama shaida idan yatashi zai bani kud'ina Dan na kasuwane.
Asma'u da Anty sa'a, mufida, Rafi'a duk kallon mamaki suke masa, shikansa ya fahimci haka amma saiya basar yamik'ama Asma'u hannu alamar tabashi takardun.
Kanta ta girgiza ta ce, ''ya Abubakar kabarsa akwaima kud'i awajena kuma insha ALLAH zasu ishemu komai.
Babu kunya ya washe bani yana fad'i a to kinyi k'yankai Asma'u.
Babu Wanda yatanka masa acikinsu, Asma'u da Anty sa'a suka tafi wajen da Dr yafad'a musu.
Sunbiya kud'in komai sannan sun sayo duk magungunan da ake buk'ata, dawowarsu babu dad'ewa ya Abubakar yawuce kasuwa akabarsu mama anan.
Sumadai zuwa dare duk suka tafi akabar Asma'u kawai awajensa, da mamace zata tsaya Asma'u tace taje tahuta ita zata zauna dashi, dak'yar tayarda saida su Anty sa'a suka saka bakima.
Bayan tafiyarsu Asma'u tayo alwala tashimfid'a sallaya, sallar isha'i tagabatar tayi addu'a sosai darok'on ubangijin al'arshi akan yakawoma mijinta d'auki da sassaucin halin daya tsinci kansa aciki, tashafa addu'ar tanamai zubar da hawaye, bayan kammalawarta saman kujerar dake d'akin tadawo ta zauna ta talsurama k'yak'yk'yawar fuskar ya Umar idanu, duniyar tunani tafad'a wa rayuwarsu tabaya maicikeda abubuwa na ban mamaki, ban haushi, al'ajabi, tausayi, farinciki, da jarabawoyi kala-kala...........

*_SHEKARUN BAYA DASUKA SHU'DE_*🤔
Malam Tsalha baduku tsohon kirki mai mata d'aya da 'ya'ya uku aduniya.
Hajara tsohuwa mairan k'arfe uwargida kuma amarya agidan malam Tsalha baduku, ta haifamasa yara uku 2maza 1mace.
Usman, Kabiru, Binta.
Sun rasu suduka tun shekarun baya dasuka shud'e.
Usman yanada mata d'aya da yara Uku shima, Mero itace matarsa suna kiranta da mama, malam Usman mutumne mai hak'uri da kawaici, yanada son 'yan uwansa sosai dakuma iyayensa, bawani mai k'arfi banebashi amma mutumne mai Neman nakansa cikin tsaftatacciyar hanya, akwaishi da wadatar zuci dakuma Nuna godiyar ALLAH kan abinda yabashi walau kad'an kokuma mai yawa.
Saidai Bahaka bane ga matarsa Dan itakam akwai hange-hange da son kud'i damai kud'i, Indai Kanada naira tokuwa kai abokin tafiyane, idankuwa babu to kana gefene awajenta.
Yaransu uku Sa'adatu, Abubakar, Umar Fharuk.
Sai kuma Kabiru matarsa d'aya wasila amma basu ta6a haihuwaba.
Halin Kabiru shima yasha banban Dana malam Usman dankuwa shimadai akwai son 'yan canji, toshikam babu laifi yanada d'an hali danyafi malam Usman arzik'i.
Sai Binta itamadai tayi aure harda yaranta, halintakam irinna malam Usman ne dantanada hak'uri sosai da kuma zafi idan ka k'ureta.
Yaranta hud'u duk mata, Saratu, Asma'u, Fateema, Hasiya.
ALLAH yayima malam Usman rasuwa tunsu Umar suna k'anana danshi bama sosai yasanshiba, bashida wayo sanda yarasu.
Bayan Rasuwar malam Usman rik'on yaran yacigaba gudana hannun mahaifiyarsu mama, ta taka rawar gani sosai wajen kula dasu har bayan shekara uku da rasuwar malam Usman sai kawu Kabiru yazo da buk'atar auren mama abisa shawarar da inna binta k'anwarsu tabashi.
Dagudu kuwa mama ta yarda Dan tasan Kawu Kabiru yanada d'an abin hannunsa gashi kuma baita6a haihuwaba, ba'a wani 6ata lokaciba aka d'aura auren, anan gidan tacigaba da zama, cikin ikon ALLAH kuwa saiga ciki, wayyo zokaga murna wajen kawu kabiru da family gaba d'aya, tattali sosai yakema mama, ciki yanakai wata Tara da wasu kwanaki ta sunkuto d'anta Namiji Wanda yaci suna Usman suna cemasa Harris, shekarar Harris biyu mama takuma haihuwar mace Mufida, daganan sai Auta Rafi'a.
Rafi'a nada shekara biyar aduniya Anty sa'a tayi aure bayan ta kammala karatunta na Secondary, taso cigaba da karatu amma hakan bai samuba, shima Ya Abubakar a daddafe da buga-buga yakammala Diploma d'insa, daganan yay aure yanad'an sana'ar saida kayan provision awani shago dake k'ofar gidansu.
Bata sake zaniba akan Umar Fharuk dan shimadai duk ajirgi d'aya suka sauka, bayan kammala secondary yafara karatun nasa a B,U,K saboda k'yawun result d'insa kai tsaye degree suka basa, dahad'a gabas had'a yamma aka kammala, ALLAH yabashi nasarar fita da result mai k'yau, yayi farinciki sosai hakama 'yan uwansa musamman ma mama Dan aganinta itamafa karan 'ya'yanta yakai tsaiko yanzu.
Umar yadawo zaman gida babu aikinyi, tun zaman yana masa dad'i harya fara gundurarsa, tuna maganarnan ta hausawa dasukance babu maraya sai rago tamasa allurar tashi domin Neman abinyi, duk abinda yasan zai rufa asirinsa yinsa yakeyi babu sanya ko girmankai irinna 'yan bokon nan, ana haka wani abokinsa yay masa hanyar Babur na adaidaita sahu, sosai Umar yaji dad'in wannan taimako, cikin farin ciki yazoma mama da kawu Hamidan wannan labari.
Hummm, amma saisuka gwaleshi da nuna masa wannan k'ask'ancine, yaza'ayi kamarsa dayakeda kwalin degree yak'are da tuk'a babu, gsky yacanja shawara amma ba wannanba.
Wannan lamari ya6ata ran Umar sosai, Dan haka ransa a6ace yanifi gidan inna binta.
Tarba sosai yasamu agurinta Dan d'an gatantane.
Inna tasaka Fatee takawo masa abinci da ruwa, saida yaci yak'oshi sannan yakwashe komai yafad'a mata.
Itama ranta ya6aci sosai Dan haka taita fad'a kamarsu mama na gabanta, takuma kwantar masa da hankali akan zata samesu, shikuma yaje yakar6i adaidaita sahud'in yafara aikinsa.
Yaji dad'i sosai Dan haka yayta mata godiya, daganan hira maidad'i suka cigaba dayi Dan akwai shak'uwa tsakaninsu sosai.
Sallamar Asma'u da Hasiya ne yasakasu katse hirar suka amsa.
Asma'u tazube littatafanta na islamiyya tana fad'in wash inna wlhy nagaji yau.
Binna ta ce, "to sannu ragguwa, amma bakiga yayankiba.
Idanunta tad'ago ta kallesa, saikuma ta kauda kai tace ina yini.
Bai amsataba saima hararta dayakeyi, takuma fad'in inayini, Dan ita azatonta baijibane, d'an yatsine fuskarsa yayi sannan ya amsa, yamaida kallonsu ga Hasiya da itama take gaidashi, ya ce, " Autar inna ya islamiyyar?, kinadai yin k'ok'ari ko?.
Hasiya ta jinjina kai ta ce, "eh yaya munayi, yanzu hakama ina ajin sauka nida yaya fatee, yaya Asma'u kuwa sune manya Dan sune 'yan ajin hadda.
d'an satar kallon Asma'u yayi, suna had'a ido ya kauda kai.
Asma'u tad'an ta6e baki tareda mik'ewa tashige d'akinsu tana k'unk'unai Dan haushin ya Umar takeji saboda abinda yay mata shekaran jiya, tana hira da saurayinta ya koreshi, abin bak'aramin haushi yabataba.
Bata k'ara fitowa falonba saida taji yatafi sannan tafito.
Inna tabita da kallo, kekuwa Asma'u mikikeyi ad'aki tun d'azun?.
Kanta tad'an sosai ta ce, "inna ina wayane da Anty saratu fa.
Inna batace komaiba ta mik'e, saida takusa zuwa k'ofa sannan tajuyo tana kallon Asma'u, ta ce, "idanma laifi kikaima Umar to wlhy kiyi gaggawar bashi hak'uri Dan kinsan Sam banason raina nagaba.
Asma'u ta kwa6e fuska kamar zatayi kuka, nifa inma ban masa komaiba.
Ohodai nidai nafad'a miki, inna tafad'a tana ficewa daga falon........

*_(((S)))......2017_*
*_Luv you all_*
[11/22/2017, 1:23 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*

*_page→7-8_*
Chapter 4 · 0% Book details