← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 44

Sashe 28

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Koda ya Umar yafita saiya samu adaidaita yashiga zuwa gida. Zuciyarsa namasa ciwo da tunanin hali irin na mahaifiyarsu, amma kokad'an abinda take masa bai gutsiri ko kwayar zarrah daga k'aunar dayake mataba irinta d'a da uwa, yanason mahaifiyarsu, akullum kuma yana mata addu'ar neman shiriya wajen ubangiji.
Har suka iso baimasan sunzoba, saida mai Babur yata6ashi sannan yakawo nimfashi, kud'insa yabasa yay masa gidiya.
Shago yafara Shiga suka gaisa dasu Harris sannan yak'arasa cikin gida.
Idonsa nakan Asma'u dake a kwance a tsakar gida bisa tabarma, agogon hannunsa ya kalla 5:13pm. Ya girgiza kansa, afili ya ce, "yarinyarnan bazaki daina wanan barcin la'asar d'inba dakika koya ko?. Narasa mike damunkine haka?.
Yana maganar yana tafiyane gareta, harya k'araso yazauna Kusada ita. takalmin k'afarsa yafara k'ok'arin cirewa yana fad'in Husna! Ke Husna! Tashi mana.
Asma'u batada nauyin barci sosai tabud'e ido ahankali, ganin ya Umar zaune Kusada ita yasata yunk'urawa ta tashi da k'yar. yad'an juyo ya kalleta ya kakka6e safar daya cire. Waini barcinnan dad'i yakemikine dakika kasa dainawa? Magana tanawa nayi miki akan barcin la'asar?.
Hamma Asma'u tayi tanad'anyin mik'a, kayi hak'uri Yaya wlhy nima bansan sanda barcin ya sacenibamafa, zaune nake ina kallo awaya.
Takalmansa yagyarama zama, yad'ora safar akansu sannan yamatsa baya sosai ya zauna tareda jingina da bango.
Jawo Asma'u yayi kusadashi. Husna kodai akwai abinda ke damunki? Wanana barcin naki yafara yawa, yanzufa mawuyacine nashigo gida ban tarar dake kina barciba. Kalli yanda tsakar gidanan yay datti amma kinkasa sharewa, kuma aii da bahaka kikeyiba, kalli wancan wanke-wanken tunda zan fita naganshi acan gurin, haba Husna sokike kikoyi k'azantane?.
Kanta ak'asa ta ce, "a'a!."
Tomike damunkine?.
Wlhy Yaya nima ban saniba, haka kawai barci baya isata yanzu, koda zanyini inayinsa.
Shiru yayi yana kallonta, itama shitake kallo, ajiyar zuciya yasauke yana fad'in to ALLAH ya k'yauta. nibara narage kayan jikina.
To tafad'a tana binsa da kallo.
Silifas d'inta yasaka, yad'auki takalmansa yanufi cikin falon.
Yana shigewa Asma'u takoma ta kwanta abinta.
Bayan kamar minti 16 ya Umar yafito, kallon Asma'u kawai yayi ya girgiza kai. Shibaima San yazai mataba wlhy, amma zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dolene yakaita wajen Dr Al-ameen, k'ilama shawarace ke damunta, dama gata makwad'aiciya.
Tsintsiya ya d'auka yafara k'ok'arin share tsakar gidan. Tas kuwa yashareshi, dama bashida wani girma, yajawo ruwa a rijiyar dake gidan ya ciccika bambun waje dana toilet d'insu duka sannan yafara wanke-wanken.
Duk abinda yadace saida yagyarashi sanan. Aikodai yaji jiki, jiyakema bayansa ya rik'e. Mik'a yayi yana mammotsa ga6o6insa. Kai mata mafa suna aiki, kana ganin aikin cikin gida kamar k'aramin Abu ammafa ba k'arami baneba, wlhy bayana harya k'age, aidole nayi wanka da ruwa mai zafi.
Shikad'ai yaketa surutanta yayinda yake kwashe kayan wanke-wanken yana kaiwa kichin.
Yana gamawa ana kiran sallar magriba, alwala yayi kawai. matsowa yayi Kusada Asma'u yana tada'ita, k kasa sarkin barci tashi lokacin sallah yayi.
Da k'yar ta iya tashi, Dan jin jikinta take dukyayi nauyi, saidama ya taimaka mata sanan tamik'e tsaye. Zaki iya kona rakaki kiyi alwalar?.
Asma'u daketa faman lumshe ido ta ce, "a'a zan iya."
To ni saina dawo.
Bai wani tsaya jirantaba yafice masallaci.
Itakam sororo tatsaya tanabin ko'ina nagidan da kallo, abin mamaki wai yau ya Umar dakansa yay aikin gidan? K'arasawa tayi wajen banbunan ruwa, ko ina cike yake da ruwa, talek'a kichin nanma tsaf, dukda dai yasaka kayan wanke-wanken duk ba daidaiba. Murmushi tayi ta ce, "ina sonka dayawa yayana, ALLAH yabarmu tare.
Itama sallar taje tayi.
Tana idarwa tafito da zummar nema musu abinda zasuci, leda ta hanga saman tabarmar data kwanta, tak'arasa tad'auki ledar tabud'e, tofa wayabama Yaya dambun nama haka?.
Mamace tace nakawo miki.
Da sauri tad'ago danbataji shigowarsaba. Tayi murmushi kai amma nagode, tana nan lafiya itada Abba dasu Rafi'a?.
Lafiyarsu k'alau, bamma tadda kowaba agidan, Abba yana wajen aiki, su mufida kuma suna islamiyya.
Ayya.
Robar tamaida ta k'ulle tana fad'in bara nashiga kichin yaya..
Kichin kuma? Mizakiyi akichin?.
Yaya abinci mana, da ranafa banyi komaiba Dan naga bakanan.
La'ila misu Harris sukaci to?.
Anty Saddiqa takawo musu abinci.
To kekumafa?.
Ni kawai nasha garin kwaki.
Garin kwaki kuma?.
Eh wlhy Yaya shinake sha'awar sha.
K'arasowa yayi daf da ita, Yakama hannunta suka zauna atabarmar, sai binjikinta yakeyi da kallo kamar mai Neman wani abun. Husna anya kuwa kinada lfy?.
Yaya lafiyata k'alau wlhy.
Kin tabbata babu abinda yake damunkine?.
Kanta tad'aga masa alamar eh.
Shiru yayi yana nazarinta, zuwa can ya ce, "kinga shirya muje wajen Dr Al-ameen.
Asma'u tazaro ido waje, Yaya wlhy lafiyata k'alau, kuma awanan daren zamuje wajen Dr Al-ameen? Aii yanzuma yatashi aiki.
Shiru yayi yana nazarin maganarta, zuwa can kuma ya sauke ajiyar zuciya to ALLAH yakaimu safiya.
To Ameen, saidaifa nidai lafiyata k'alau.
Inafa kikaga lafiya my Husna? Wai kinga yanda kike ramewa kuwa?.
Hannu tasaka tana shafa wuyanta, azuciyarta ta ce, "rama kam aii fitinarkace takawota, amma afili saitace yanayine kawai Yaya.
Baice komaiba, yadai jawota jikinsa ya matse.

*_washe gari_*
Tunda wuri ya Umar yasaka Asma'u tashirya badan tasoba, shima shirinsa yayi cikin d'anyar shadda green mai duhu, yayi k'yau ainun.
Yafito sai zabga k'amshi yakeyi, itama haka Asma'u tana k'amshi mai sanyi bawai irin nasaba.
Kai my Husna ALLAH kuwa jikina ciwo yakemin har yanzun.
Dariya Asma'u tayi, kai Yaya dagayin d'an aiki duk ka cikamu da raki tun jiya. Sharafa da wanke-wankene sai d'ibar ruwa, amma jiya saida namaka tausa, kayi wanka da ruwa mai zafi kuma.
Kibari kawai har yanzu ban dawo garauba gsky, inagama sai Dr Al-ameen yabani maganin ciwon jiki.
Dariya sosai Asma'u take masa.
Shikuma yatsuke fuska wai yaji haushi.................😄

*_(((S)))........2017_*.
*_I love you all_*
[12/22/2017, 9:00 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

_ina kike my k'anwa Marak'isiyya?, wanan shafin nakine, gaisuwa agareki da fatan alkairi, ALLAH ya tabbatar da farinciki agareki my sweet lil d'ina💋_*
*_page→53-54_*

..........Lokaci k'an k'ani suka isa Asibitin, ko kad'an ya Umar baya buk'atar had'uwa da Dr Jafar, Dan haka yasa sukabi tabaya shida Asma'u.
Saidai kumar abin fad'a suna karya kwana saiga Dr jafar shida wasu Norses.
Ya Umar Harya d'auke kansa saikuma yaga rashin dacewar hakan, gyara tafiyarsa yayi yadawo kan hanya sosai, sa6anin da daya koma gefe.
Shima kansa Dr jafar baiyi niyyar gaisawa da ya Umar ba, amma ganin ya Umar yanufoshi ga wani kwarjini daya masa saiya dake shima.
Sallama ya Umar yamasa, da k'yar Dr jafar ya amsa, ya Umar yayi murmushi yana mik'a masa hannu, haj Jafar talaka baya ganinku?.
Wata dariyar k'eta Dr jafar yayi tareda fad'in mu mun Isa? Aikune manya-manya maganin k'ana-k'ana.
Dariya sosai ya Umar yayi wadda har zuciyarsa yayita, yazame hannunsa daga na Dr jafar yana fad'in to mungode, ya aikin?.
Alhmdllh Dr jafar yafad'a cikin 'yar kunya.
Asma'u kam tana gefe ko kallo baima ishetaba, Dan yana jerin manyan wad'anda tatsana wlhy. Koda yad'ago suka had'a ido, yawashe baki zai gaisheta saita daka masa wata uwar harara.
Ruf yarufe bakinsa yakasa magana.
Abin nasu yaso bama ya Umar dariya, amma saiya gimtse yayima Dr jafar sallama yabi bayan Asma'u dahar takusa shan kwana.
Harara Dr jafar yaraka bayan ya Umar da ita.

Nikam bilynku na ce, "ohodai ihu bayan hari kenan."🤷🏽‍♀😜
Chapter 28 · 0% Book details