Sashe 21
Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Ya Umar yayi ya ce, ''to ALLAH ya kiyaye."
Ameen dai Umar.
Yanzu zaka iya fara zuwa aiki daganan zuwa Monday.
Alhamdulillah ngd sosai Alhaji, ALLAH yak'ara bud'i na alkairi.
Ameen Umar..
Daga nan Ya Umar yatafi sai kuma gidan inna.
Babu kowa a tsakar gidan, sai kaji da su Inna ke kiwo sunata kaida kawo. Yakuma yin sallama ak'ofar d'akin da takalma suke birjik har wajen k'afa shidda. Kusan atare suka amsa. Sannan yashiga.
Sannu da zuwa suka shiga yimasa da gaisheshi, yayinda shikuma idonsa kebin Harris da kallon mamaki. Dama yana zuwa gidannan?.
Shima kansa Harris d'in yalura da kallon da yayan nasa kemasa, Dan haka yay k'asa da Kansa alamun jin kunya.
Inna duk tana kallonsu. Ya Umar yaje kusada inna ya durk'usa cikeda ladabi ya gaidata.
Cikin fara'a ta amsa masa da tambayar lafiyar iyali?. Ya ce, komai Alhamdulillah. Asma'u ma na gaishesu.
Muna amsawa.
Kallonsa yamaida ga Anty Saratu, ya ce, "sarkin yawo kenan, kekam kina iya sati d'aya bakizo gidannanba?..
Kanta ak'asa ta ce, " ya Umar wlhy har sati uku inayifa."
Harara ya balla mata, a'a har shekara kinayi, inna ba kwana hud'u dasuka wuce Nazo gidannan natarar da yarinyarnan ba agidannan?.
Dariya inna tayi, wlhy hakane Umar, nima yanzu babu jimawa nagama mata fad'an yawo, dan ba abune mai k'yauba.
Ya Umar yakuma harararta, mijin nakine sakarai dayake barinki, ke ko saboda yara yawon baya damunki?. To daga yau karna sake ganinki agidannan sainan da wata uku. Idan bahakaba kuma ranki zai 6aci matuk'a.
Gyad'a kai tayi dukda hukuncin NASA bawai yamata dad'i baneba, Dan Anty Saratu akwai d'ambazan yawo kamar taci k'afar kare. (Shima mijin NATA bayaso, amma saboda yana matuk'ar sonta saiyake barinta)..
Daga nan hira akad'an ta6a, wadda ya Umar bawani saka musu baki yakeyiba sosai, garama idan inna tayi magana.
Zuwa can ya ce, "inna Nazo wajenkine."
To yaron arzik'i, nima kuwa dama ina nemanka.
Saratu da Hasiya, fatee kufita. Amma Harris yatsaya.
d'agowa ya Umar yayi ya kalli Harris d'in da yay k'asa da Kansa, Dan bak'aramar kunyar ya Umar yakejiba.
Bayan fitarsu Inna ta kalli ya Umar. Umaru! Inaso kabani Aron hankalinka nan, mufara maganar da Harris yazo da ita, dukda nasan bakazomin da sakaren maganaba kaima, amma na Harris ma yanada matuk'ar muhimmanci.
To inna ina saurarenku.
Inna ta kalli Harris daya marairaice fuska tamkar zaiyi kuka. Harisu taso kazo nan.
Jiki a sanyaye Harris yataso, yazo kusada ya Umar yazauna. Inna ta nuna masa ya Umar da ido.
Zamansa ya gyara muryarsa na rawa ya ce, "yaya Dan Girman ALLAH kayi hak'uri, ka yafemin duk abinda namaka. Wlhy na tabbata duk gidammu babu mai mana Abu tsakani da ALLAH kamarkai. Abunda yafaru abayama sharrin shaid'anne. Ka gafarceni, insha ALLAH bazan sakeba. Wlhy yanzu ina tareda kai 100%.......
Ya Umar yakatseshi da fad'in wai Harris miya farune? Nifa bakamin komaiba wlhy.
A'a yaya namaka wlhy, Dan ALLAH karkace ban maka komaiba, idan kace haka zan d'auka bazaka yafeminba.
Hummm shikenan Harris nayafe maka, harma sauran, damani banrik'e kowa acikinkuba, saidai inason kuringa fahimtar miye rayuwa akowane yanayi tazo gareku.
Wlhy ya Umar nagane kam yanzu. Jiya naje wajen ya Abubakar akan yabani naira dubu goma na kar6o result d'ina. Amma shine ya hauni da masifa wai bashidashi, shima somuke mu karyashi kamar yanda muka karyaka *_KARAYAR ARZEEK'I_* tasameka. Yanzufa nauyin kayan d'akin Mufida yana kansa. Shi wlhy bazai iya da fitinarmuba mudasu mama........
Ya Umar Yakuma katseshi da Sauri, Harris ban ganeba, ansakama mufida ranar aurene? Da har aka fara maganar kayan d'akinta?.
Inna da Harris suka kalli juna cikin mamaki.... Har had'a baki sukeyi wajen fad'in kana nufin baka saniba?.
Ahankali ya Umar yakad'a kansa tamkar k'aramin yaro.
Sallallami inna tafara tana tafa hannu, oni binta wannan wace irin rayuwace haka?. su yaya Kabiru suka d'auki duniyane?.
Ammafa ranar da'aka kawo kud'in danaje ban gankaba saida na tambayi Maman taku, shine ta ce, "anfad'a maka amma kace aiki yamaka yawa Abubakar ya wakilceku tunda shine babba.
Shekaran jiya kuma daza'a saka ranama saida nayi magana, naga babukai babu iyalinka, nanma tace anfad'a maka harma kazo, anasaka rana wai katafi saboda Asma'u batajin fad'in jikinta.
Wani huci mai zafi ya Umar yashiga furzowa daga bakinsa, idanunsa sun kad'a sunyi jajur, yay ka d'a kansa yana ambatar *_" innalillahi wa'inna ilaihirraji'u."_*
Ganin haka mama takwalama Hasiya kira. Ta ce, "takawo ruwa mai sanyi.
Saida ya Umar yasha sosai sannan hawaye suka fara gangarowa akumatunsa masu zafi kuwa.
Babu Wanda yahanashi, Dan hawayen zasu saka zuciyarsa yin sanyi tarage nauyin datayi.
Harris ma hawayen yakeyi, danshima yafara fuskantar matsala irinta ya Umar awajen mama da Abba. Kullum saita masa gori baita6a yimusu komaiba itada abba.
Inna ta ce, " ya isa haka, kuyi hak'uri, kucigaba dama iyayenku addu'a kunji. Komai zaizama labari.
Ya Umar yasauke ajiyar zuciya yana fad'in babu komai mama, yawuce, amma yanzu wane wata aka saka bikin Hamidan?.
Nanda wata biyarne Umaru kaji.
Murmushi yayi ya ce, "ALLAH yakaimu inna. Kuma insha ALLAH bazan nuna musu nasan komaiba, kaima Harris karka nunama kowa ka sanarmin.
Harris ya jinjina masa kai kawai.
Daga nan mama tamusu nasiha da nuna musu muhimmancin zuminci da kula dajuna, had'inkai suzama tsintsiya mad'aurinki d'aya.
Suduka nasihar tashigesu dak'yau.
Sukaitama mama godiya.
Ya Umar kuma yafad'a musu shima alkairin daya samu ayaud'in daduk abinda yafaru. Farin ciki sosai suka shigayi, Harris harda rungume ya Umar, shima yarungume d'an uwansa suna farinciki. Bayan sun nutsu ya Umar yace to Dan ALLAH su binne maganar anan kar kowa yaji.
Inna ta ce, " hakan yayi Umaru!, koni ban goyi bayan wani yaji zancennanba. Harrisu kakula kaji.
Insha ALLAH inna babu maiji wlhy. Amma yaya tunda zaka fara aiki zandawo tsare shagon, basai Asma'u tazaunaba.
Murmushi ya Umar yayi, dama bayason zaman Asma'u ashagon Dan yanada tsananin kishi sosai. Godiya sosai da farinciki ya Umar yanuna akan abinda Harris yamasa. Daga nan hira mai dad'i suka cigaba dayi har zuwa wani lokaci sukaima inna sallama suka tafi.
Daga nan gidansu suka nufa.
Duk afalo suka iskesu har ya Abubakar da matarsa, anbaje alawa da biskit anata rabo.
Ya Umar yagaida mama cikeda fara'a, ko kad'an bai nuna musu komaiba, ya Abubakar ma suka gaisa, suma hamida da Rafi'a suka gaisheshi. Matar ya Abubakar sai wani cika da batsewa takeyi ita adole matar mai kud'i. Kota kanta baibiba yamuk'e yamusu sallama.
Kowa yayi mamakin da yau bai zauna hiraba, tunda yaga duk suna nan, (kuma kowa yasan ya Umar dason ahad'u gaba d'aya ayi hira) amma yau sai sukaga sa6anin haka. Gashi ko alawa da biskit d'in gabansu bai tambayi kona miyeba, kuma fuskarsa asake babu wani alamar 6acin rai agareshi.
Sallama yamusu yafice. Mamadai tasha jinin jikinta, hakama ya Abubakar, dama shine yazuga mama wai kar agayama ya Umar, idanma angaya masa mizai musu? Mutumin da bashida ko sisi. Kayan dake shagon nasa basu wuce na dubu 60 ba gabad'ayansu. Da ire-iren wannan musalan yabige hankalin mama da Abba, ya ce, ''kuma shine zaima Hamida kayan d'aki.
Su su Rafi'a basusan ya Umar baisaniba, amma sunsha mamaki dabasuga Asma'u ba awajen saka rana.
Daga nan gidansa yanufa hankali kwance. Yana tsaye abakin titi zai tare adaidaita sahu, harma ya tsayar dawata suna ciniki saiga wata ash d'in mota ta giftasu. Har mai motar yad'an wuce saikuma yadawo baya.
Horn yayma ya Umar, ya Umar bai d'agoba, dan kokad'an baid'auka dashima akeba.
Mai motar nan yasake yin Horn harsau uku.
Ganin haka mai adaidaita yayma ya Umar dake k'ok'arin Shiga magana. Malam dakaifa mai motarcan yake.
Dani kuma? Ya Umar yay maganar yana lek'o kansa Dan tabbatarwa.
Hannu kuwa yaga and'ago masa. Tofa bara naga wanene ina zuwa.
Babu damuwa mai adaidaita yafad'a.
Ya Umar yafito zuwa motar.
Maimota yabud'e yafito yana fad'in *_Umar bin Usman!_* dama rai kanga rai?.
Soasai ya Umar yazaro ido waje, Yazeed! Dama Kaine?.
Cikin farinciki suka rungume juna.
Yazeed ya ce, "Umar ina kashige haka? Nayi nema harna gaji. Natambaya amajillisa su alkasim sunce min suma basusan inda kakeba yanzu, wai tunda mall naka yak'one ka gujesu gaba d'aya.
Murmushi ya Umar yayi kawai, ya ce, " Yazeed wannan bamaganar titi bace, kabari next time Idan mun had'u zamuyita. Amma yaushe kadawo k'asarnan?.
Wlhy tun sati biyu daya wucefa. Tunda nadawo kaina fara nema awashe gari, naje gidanka akace aii katashi, natambayi abokai sukace basu saniba. Naje gidansu Lubna natarar suna biki. Cikin ikon ALLAH yanzu har zan wuce saina hangoka.
ALLAH Sarki Yazeed, yanzu dai ina zamu had'u mai Babur yana jirana.
Wai inama motarka naganka zaka hau adaidaita?.
Murmushi kawai ya Umar yayi ya ce, "Yazeed kaidai babu abin fad'a abakina sai Alhamdulillah.
Yazeed ya jinjina kai, shikenan sallami mai adaidaitar kazo muwuce.
A'a kaje uzurinka, baikamata na katse makaba.
No. Babu Inda zanje wlhy, nakai Zuhrah gidane suna wani taro a family d'insu.
Yazeed yaje dakansa yabama mai adaidaita d'ari biyar sannan ya sallamesa.
Mai adaidaita sai zabga godiya yakeyi yatafi.
Ya Umar kam yashiga motar Yazeed suka tafi suma..............
*_(((S)))........2017_*
*_Luv you all_*
[12/15/2017, 7:37 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
_sak'onki ya iso gareni *Ummu sadeeq* alkairin ALLAH yakai gareki aduk inda kike._
Luv you zam zam😻 .
*_page→43-44_*