← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 44

Sashe 27

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Muktar yana zaune amota yana kallon masu aikin Fentin, fitowarsa kenan daga wajen bayan yagama duddubawa.
Sallamar da akai masace tasakashi d'agowa, matasan samarine su biyu, d'aya aciki ya ce, "sunana Tasi'u, wannan kuma Salman, idan bazaka damuba kazomuje can mana, suka nuna majalissarsu, munga kullum kazo saidai kaita zama a mota, wanan ba girmanka baneba.
Murmushi Muktar yayi, Dan dukansu yaganosu abokan Umar ne.
OK babu damuwa ngd sosaifa. 'Yafad'a yana fitowa'.
Yana kallon sanda Salman da Tasi'u suka kalli juna suna murmushi. aransa ya ce, " Niba Umar baneba, wuju-wuju zan muku wallhy.
Har majalissar suka k'arasa, dukyabama sauran hannu suka gaisa, yasami guri a zauna, hira akacigabadayi cikin raha, zuwacan Hafiz ya ce, "kai ammafa wajennan yayi k'yau wlhy, kunyi k'ok'ari wajen gyarashi, daga gani ya lashe miliyoyin nairori gsky.
Murmushi Muktar yayi, wlhy d'an uwa yaci kud'i kam, bak'aramar 6arna wutar taima wajenba, shiyyasa nake tausayama wannda yakeda wajen.
Aidolene a tausaya MASA Cesar Kabeer yana turo baki gaba alamar zund'e, to amma shine yasayar maka da wajen?.
Saida muktar ya kallesa sannan yasaki wani murmushin mugunta, eh shine ya sayarmana, amma da sainaji kamar ance bokinkine.
Kamar antsikari Dr jafar ya ce, " eh adakam abokinmune amma yanzu ko Inda yake bama musaniba, ranar wani abokinmu harda zuwa nemansa, inagadai baisan yanzu yazama karfaba.....
Gabad'aya suka bushe da dariya amma banda muktar daya tsaya kallonsu, k'asan zuciyarsa kam yanajin wani d'aci. Shimamakima yakeyi yanda Dr Jafar d'in bai ganeshiba.
Haka sukaita tattaunawa da zagin ya Umar, shidai Muktar suna bashi mamaki, sai gab da magriba yamusu sallama yatafi gida cikeda mamakin halin d'an Adam.
Koda wasa Muktar baita6a bama ya Umar labarin yanda sukayi dasu Hafiz ba, amma kullum yana nusashsheshi akan yadage da addu'ar Neman tsari, Dan tabbas yana zagaye da mak'iya, kuma komai zasu iya aikatawa akansa idan sunga ALLAH Yakuma d'aukakashi.
Sosai YA UMAR yakar6i shawarar Muktar, haka suka duk'ufa addu'a shida matarsa, yanzu sundage tashi duk dare suyita nafilfili da mik'a kukansu ga ubangijin talikai, ga azumin litinin da alhamis sunatayi, sadakama ba'a barsu abayaba.
Duk hidimarnan da akeyi babu Wanda yasan abinda ke faruwa a family d'in ya Umar. Inna Ce kawai tasan komai.
Itama kuma tayi gum abinta.
Ranar ya Umar yaje gaigaida iyayensa, yana zaune ak'asan kafet yayinda mama take saman kujera, sai cika take tana batsewa. Kan ya Umar na ak'asa.
Mufida da Rafi'a sunama islamiyya.
Cikin masifa mama ta ce, "Umar ni wacece awajenka?.
Saida yad'ago yad'an kalleta sannan ya ce, " mahaifiyatace!."
Inafa mahaifiyarka Umaru!, aidaka d'aukeni matsayin mahaifiyarka dabaka saida shagunankaba harka kasa fad'amin. Wato kamaidani lasha money ko?.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, murya a sark'e ya ce, "kiyi hak'uri mama, koda nasayar aii bama abani kud'inba, sunce saisun gama gyarashi sun tabbatar babu matsala sannan subani kud'in, shiyyasa Nima na 6oye miki, nafison da anbani kud'in sainazo na nuna miki saikinfi yin farinciki.
Mama tagyara zama tana k'ara washe hakwara, eh kumafa da gskyarka Umaru, dama kaga gashi ansaka bikin mufida wata biyu kenan, yanzu saura wata uku, ninasan mak'on Abubakar bazai barsa yaymata kaya masu tsadaba alkur'an kuwa. Inadai fata kafin bikin kud'in namu sun fito ko?.
Kai kawai ya Umar ya iya jinjina mata saboda 6acin rai, uwa uwace babu mai canjata, shibaisan wane irin haline da mamaba........?.
Maganartace takuma katse masa tunani.
Yauwa Umaru ALLAH yayi maka albarka, ammafa kayi hak'uri ankgaya maka maganar bikin Mufida amakare, wlhy Abubakar ne yahana afad'a maka, kasandai halinsa na nunkufurci......
Da Sauri ya Umar ya ce, " babu komai mama, nibara nawuce, inaso nad'anyi wani aikine.
To...to....to Umarina, amma bazaka tsaya ko d'an wani Abu kaciba?, inada wani dambun nama kuwa zauna kaci.
Mama kibarsa kawai, ina saurine aii.
A'a aiba'ayi hakaba, bara na k'ulla ka kaima d'iyata Asma'u. Tana maganar tana shiga d'aki.
Ya Umar yagoge wasu 'yan kwalla da suka tarumasa agefen idonsa:- dawanine yafad'a masa akwai iyaye masu irin halin mahaifiyarsu walhy dasai ya k'aryata, da'a film yagani saiyace wasan kwaikwayone, da a Novel yakaranta dasaiyace k'aryace kawai da wasa da hankalin mutane irinna marubuta. To amma gashi ra'ai-ra'aini yana gani. Ya ALLAH ka shiryi irin wad'annan iyaye!.......
Yauwa Umarina gashi, mama tamik'o masa bak'ar leda wadda aka k'unshe k'aramar roba a ciki.
Kar6a yayi yaymata godiya sannan yatafi.
Yana fita mama tafara rawar murna, kai ALLAH mungode maka kud'in zasu shigo, wlhy dama inata tunani akan yanda zanyi shagalin bikinnan Dan nasan Abubakar da shagen mak'o, k'ark'ari yabani dubu hamsin, amma kinga Umar konawa nace inaso wlhy yaronnan zai bani.
Kai talaucima baiyiba wlhy, aigarama daya saida shagunan koba komai aii zamud'an shana kwana biyu.

_Humm kai jama'a wanan wace irin uwace? kamata yayi tayi bak'inciki dayima ya Umar fad'a akan miyasa ya sayar, amma kuduba murna takeyi akan zasu sami kud'i, bata kallon halin dayake ciki da Wanda zaishiga nan gaba, a'a ita burinta kud'i, gashi tanata bin matakan dazata raba zumincin 'ya'yanta, yau ta nuna tafison wanan, gobe kuma tafison wancan, kaiconmu da masu hali irinna mama, wlhy iyaye kugyara, shikenan da 'ya'yanka sunfara girma saika d'auki duk nauyinka ka maida akansu, wlhy hakan yana kawo raini tsakanin 'ya'ya da iyaye. Indai d'a yakasance nakwarai kuma d'an halak bazai manta da halaccin iyayeba, bazai manta da gwagwarmaya irinna iyayeba musamnamma uwa, kahanata barci tun kana acikinta, kahanata cin abinda take so tun kana acikinta, kahanata sukuni tun kana acikinta, ta haifeka cikin magagin wahala, ta raineka, idan bakada lafiya kana kuka tanayi, idan kaji yunwa tabaka kaci koda ita bataciba, tagoyaka, ta wanke kashinka, idan anta6aka ranta ya6aci, konawa tasamu zata kashesu akanka dankayi farinciki, katuna gwagwarmayar da mahaifinka yakeyi wajen nema muku abinda zakuci da kud'in makarantarku Dana asibiti._
_Amma dan rashin tunani harka iya kasa k'yautata musu sai sun rok'eka, kai wlhy kaicon wad'annan 'ya'ya. Iyaye mugyara, 'ya'ya mugyara Dan ALLAH._
Chapter 27 · 0% Book details