← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 44

Sashe 11

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu dad'ewa Asma'u tadawo, abinda tafara tambaya shine ya Fharuk yatashi?.
Mufida tayi dariya, ta ce, "Asma'u amaryar ya Umar, yatashi yana nan zaune kekad'ai yakeson gani.
Fuska Asma'u tarufe tana dariya, ALLAH yasoma mama da inna sunacan zaune agefe su kad'ai, Anty sa'a ta ce, " jeki kigansa kinji ma'u, k'yale Mufida.
Ba musu Asma'u tashiga d'akin, babu kowa Dan haka ta kakka6e gadon tagyara sannan tazauna jiransa.
Tana nan zaune aka bud'e k'ofar bathroom d'in, d'ago idanunta tayi sai suka had'a ido da ya Umar, tai saurin kauda kanta Dan ganinsa dagashi sai tawul, cikin tafiyar mara lfy dabayajin k'arfi yak'araso kan gadon, saida ya zauna sannan ya kalleta, kanta ak'asa ta ce, "ya jikin?.
Kallonta yakumayi tareda fad'in da sauk'i, yayd'an tsaki wai ina Harris d'in?.
Asma'u ta ce, " yaje gida yadawo."
Shiru yayi, zuwacan kuma ya CE, "sakama k'ofarnan key zan shirya kar wani yashigo, jikin Asma'u a sanyaye tamik'e amma saita fara k'ok'arin fita, ya ce, " ina zakije kuma?.
Uhmm dama zanjiraka awaje, idan ka kammala saina dawo, yad'an d'aure fuska sannan ya ce, "dawo.
Babu musu Asma'u tadawo tazauna inda take ada.
Man shafawa yamik'a mata, kar6a tayi tana mai satar kallonsa, duk yayi wani cid'in-cid'in da fuska, ya ce, " d'an shafamin mannan hannuna duksunyi sanyi saboda k'arin ruwa..
Yanda yake magana a cikunshe babu alamar wasa yasa Asma'u mik'ewa da mai ahannnunta, ta lakata amma saitata murzashi Dan takasa ta6a jikinsa, ganin yanda taketa mulmula man takasa ta6ashi saiya mik'a mata hannunsa, cikeda kunya tafara shafa masa, jitake tamkar k'asa tatsage tashiga ciki Dan kunya, shikam gogan naku ko a jikinsa shi dad'inma shafa man yakeji, jiyake tamkar tana masa tafiyar tsutsa, idonsa a lumshe harta gama.
Tashi yayi yana shiryawa, Asma'u kam tazauna kanta ak'asa.
Saida yagama shiryawa sannan tajawo kulolin abinci tazuba masa, yana zaume yana kallonta harta gama, tad'ora masa filet d'in abincin a bak'in gado, shiru yayi bai d'aukaba baikuma yi maganaba, ganin haka yasa ta ce, "ga abinci.
Fuska ya yatsine dawane hannun zanci?, nacemiki hannuna yanamin ciwo.
Cikeda mamaki take kallonsa, wannan wane irin sabon salone daga ya Umar kuma?, yana nufin itace zata bashi abincinma?.......
Yakatsemata tunani da fad'in jeki kiramin mama ko inna subani tunda ke bazaki iyab.....
Bata bari yak'arasaba ta d'auki abincin tamatso tana bashi, yanda take basa abincin takasa kallonsa saita bashi dariya, amma baiyiba yadaure ya gimtse, tana cikin bashi abincin aka kwankwasa k'ofa, tashi tayi taje ta bud'e, su mamane da matan anguwarsu sunzo dubashi.
Babu kunya yamik'ama Asma'u filet d'in abinci wai tacigaba da bashi, wayyo ALLAH Asma'u tamkar zata fasa ihu, babu yanda zatayi tacigaba da bashi harya k'oshi, tazuba ruwa a cup tamik'a masa, yanzudai kar6a yayi yasha da Kansa...........

*_Luv you all_*
*_(((S)))......2017_*
[11/28/2017, 3:27 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*

*Amma saga yau na sakad'a Xoxo da hajja ce & zeety, 🤔kona had'a da Rano?, umm baradai nabarta kawai.*🤥
_muhud'u writer's Asso..... Kenan._😜😂

*_page→20-22_*

..........Alhmdllh jikin ya Umar yana yin k'yau, yaji sauk'i sosai, saidai abinda ba'a rasaba.
Dangi kam balaifi suna d'an zuwa ganinsa, musamman wad'anda zuciyarsu bata manta da d'umbin alkairinsaba sanda yakeda kud'i.
'Yan uwansa dai suna mamakin rashin zuwan Lubna asibitin, kuma duk Wanda ya tambayesa saiyayi kicin-kicin da fuska alamar baya buk'atar maganar, ganin haka kowa ya daina tambayarsa Lubna.
Yauma duk suna asibitin har kawu kabiru da babansu Asma'u, 'Yar hira akeyi da raha irinta family idan an had'u, ya Umar kam shiru baya cewa da kowa k'ala, Harris ya kalli ya Abubakar ya nuna masa ya Umar da baki (zind'e kenan, kuma babu k'yau😏.)
Baki ya Abubakar yata6e shima suka had'a ido da matarsa Haleesat.
Asma'u duk tana kula da abinda sukeyi, hakama Anty Sa'a, hawaye yacika idon Asma'u tamik'e ahankali tafice.
Ya Umar dake kallon duk wani motsin kowa, har abindasu ya Abubakar sukeyi masa, yabi Asma'u data fita tana kuka da kallo, ahankali yalumshe idanunsa yanamai jin tausayinta, shima sakkowa yayi daga gadon yanufi hanyar fita.......
Inna ta ce, "Umar ina zuwa kuma?.
d'an shafa kansa yayi, idonsa ak'asa ya ce, " inna zand'an tattaka ne, na gaji da kwanciyarne".
To aii dakayi magana sai ko Harris ya taimaka maka, kaida bakajin k'warin jikinka".
A'a inna yayi zamansa zan iyama, nafison nayi dakaina.
To shikenan, jeka, idan kagajidai kadawo kaji.
Kansa ya jinjina mata tana murmushi, sannan yafice.

Asma'u na zaune akujerun dake jere a tsakkiyar reception d'in asibitin, kanta a duk'e yake shiyyasa ya Umar baiga halin datake a cikiba, takawa yayi zuwa gareta.
Da sauri tad'ago danjin mutum ya zauna a Kusada ita.
Had'a ido sukayi da ya Umar, sai kawai tad'auke kanta, tamaida k'asa tana k'ara share hawayen dasuka silalo mata yanzun, girgiza kansa yayi tareda kamo hannunta ya rumtse anasa, yaarrrrr tsigar jikinta ta tatashi, yauce rana ta farko da ya Umar yata6a rik'e hannunta amatsayinta na matarsa, ta rumtse idanunta harda cije le6e.......
Bata gama dawowa dai-daiba taji muryarsa na kuwwar fad'in Husna!.
K'ara rintse idanunta tayi sosai takuma kasa amsashi.
Shima baya buk'atar amsar tata Dan haka yacigaba da fad'in, Husna shin bazaki zama jaruma baneba?, kina ganin rayuwa zata cigaba da tafiya komai da kuka?, Husna bamusan randa rayuwa zata canja bafa, kenan hawayenki basuda ranar k'afewa?, kinga d'ago ki kalleni.
Shiru Asma'u takasa d'agowa, amma tana sauraren dukkan maganganunsa.
Ya kuma fad'in husna kalleni mana.
d'agowa tayi cikeda kasala, suna had'a ido tayi azamar janye nata, yad'aga baki zaiyi magana Anty Sa'a tak'araso wajen.....
A'a d'an k'anina mikuma kukeyi anan wajen?.
Baice komaiba saidai nuna mata Asma'u da kanta ke k'asa yayi.
Anty Sa'a tad'anyi murmushin takaice tareda zama Kusada Asma'un suka sakata tsakkiya itada ya Umar.
Itama dafa kafad'arta tayi, cikin sigar lallashi ta ce, "Asma'u kik'ara zama mai hak'uri da jarumta dukda nasan kinadasu, kicigaba da yima mijinki kuma yayanki addu'oin fatan alkairi, kizama mai k'arfafa MASA gwiwa kinji?.
Karki sake damuwa da abinda wasu suke masa barema harya sakaki kuka, ALLAH daya basa shiyya kar6i abinsa badan baya son Umar ba, sanda ya azurtasa baiyi shawara da kowaba, hakama yayin amshewa, suma basufi karfin ya kar6e daga garesuba.
_antambayi Mazon ALLAH (s,a,w) waye talaka?._
_sai ya ce, "Wanda zaitashi ranar k'iyama babu komai na aikin alkairi a gidauniyar ayyukansa._
To Ashe talaucin duniya bashine talauciba, dukiyar duniya ba itace arzik'iba, Dan *_KARAYAR ARZEEK'I_* ta riski Umar ba hakan na nufin ALLAH baya sonsa baneba, ya jarbceshine Dan kawai yaga nauyin imaninsa, wannan itace *Kaddararsa* Dan haka bashida ikon tsallakewa, inhar d'an Adam bazai iya gujema kaddarar ranar mutuwarsaba, to tabbas bai Isa gujema duk wata k'addara a yayin rayuwarsaba, kibar kuka kinji.
Jin jina kai Asma'u tayi, cikin raunin murya ta ce, " Anty sa'a ngd da tunatarwarki agareni, ALLAH yak'ara bamu jarumtar cinye jarabawarsa, Ameen ya rabbi Asma'u, ALLAH ya albarkaci rayuwar aurenku.
Murmushi Asma'u tayi, azuciyarta ta ce, "Ameen Anty Sa'a".
Ta juya tad'an kalli ya Umar, muryarta kasa-kasa ta ce, " ya Fharuk kayi hak'uri da d'aga hankalinka danayi harka taso kafito, insha ALLAH wannan shine na farko kuma na k'arshe.
Mik'ewa yayi yana fad'in ni bakimin laifin komaiba dama.
Daga Asma'u har Anty Sa'a da kallo suka bishi harya shige d'akin dayake jinya.
Asma'u tajuyo tana kallon Anty Sa'a, kanta a langwa6e ta ce, "ya Umar yanada wuyar sha'ani anty".
Murmushi Anty Sa'a tayi tareda fad'in duk taurinsa kece zakisakashi yayi sanyi k'anwata, nakumasan zaki iya saboda jarumtarki...
Itama tana kaiwa k'arshe ta tatashi tabar wajen.
Da kallo Asma'u tabita harta shige, ta sauke ajiyar zuciya tana wani murmushi da juya maganar Anty sa'a a zuciyarta, indai hakane to tabbas zata zama zaruma wajen maida ya Omar sanyi kamar yanda Anty Sa'a tafad'a, tabbas tanason ya Umar sosai kuma zata zauna dashi aduk halin dayake ciki, itama mik'ewa tayi tashiga d'akin
Da sallama tashiga, wad'anda sukaji suka amsa, tanemi waje kusada Fatee ta zauna, data d'ago ido saita kama ya Umar na kallonta, Anty sa'a na kallonsu tana dariya ciki-ciki.....

_____________________
Kwana biyu tsakani aka sallamai ya Umar suka tattara sai gida, duk dangi sun musu rakiyya zuwa gidan nasu.
Wani abun mamaki tundaga babban falo suka fara gani, kaf abinda ke falon an kwasheshi babu komai sai agogon dake manne abango, kallon-kallo aka koma kowa yayi cirko-cirko kamar zakaru na shirin fad'a, Asma'u ce tayi k'arfin halin d'aga k'afafunta tashiga cikin falon sosai tana kalle-kalle.
Babu Wanda ya iya cewa Uffan aduk taron, Dan Ya Umar baibama kowa damar hakanba, hasalima d'akinsa yashige yabarsu anan, a falon nasama abin mamakin ya tarar Dan nanma komai babu sai agogo dawata kujera guda d'aya dayakan zauna domin hutawa, sai tebiri agefenta Wanda yakan d'ora abubuwa, dak'yar yaja k'afarsa zuwa cikin bedroom d'in zuciyarsa cikeda tunani kala-kala, nanma dai bata canja zani ba Dan babu komi sai katifa da jibgin sutturunsa akai, saikuma tarkacen daba'a rasaba, jin hajijiya na neman d'ibarsa ya dafe bangon d'akin, cikin zuciyarsa yake tunanin wayayi masa wannan aikin?, badai za'a danganta ta'asarnan da 6arayiba Dan babu abinda 6arawo zaiyi da katakai, zuciyarsa tafara rawa akan ina Asma'u tasamu kud'in biya masa asibiti?, can wata zuciyar ta ce, "ita ta saida kayan gidan kenan?. Damm gabansa ya fad'i yay shiru batareda iya koda kwakwkwaran motsiba, yama rasa wane tunani zaiyi akan Lamarin........

A 6an garen Asma'u madai tunani take yaushe ya Umar yay cinikin kayan gidansu?, kanta bai ida kwancewaba saida tashiga nata d'akin, babu komai an kwashe sai katifa, hattada akwatinanta na lefe ankwashesu kaf, sai kayan datazo dasu daga gida aka zube a katifa, innalillahi wa'inna ialaihirraji'un kawai take iya amabata, yaraf tazube bisa katifar tana sauke numfashi, wai miya shiga kan ya Umar ne haka?, Dan kawai *KARAYAR ARZEEK'I* ta riskeka sai komai daka mallaka yazama hajar rabawa a kasuwa?, haba wannan wace iriyar rayuwace?.......
Chapter 11 · 0% Book details