← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 44

Sashe 36

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana zaune abakin gado, dagashi sai tawul, da'alama yanzu yafito daga wanka. Mai yad'auka yad'an shafa sama-sama saboda zafi. Yana cikin fesa turare Asma'u tashigo da sallma.
Fuskarsa d'aukeda murmushi ya amsa mata. Yamik'e tsaye yana saka gajeren wando. Yayinda Asma'u ta zauna abakin gadon tana kwantar da fodeyo.
Ya Umar yagama saka wandon yadawo bakin gadon shima, Rankwafawa yayi yayma Fodeyo kiss akumatu yana fad'in my son rigima, ya shafa kan yaron daketa barcinsa, yanzu gaka kana barcinka? Sai anjima kahanamu barci ko?.
Asma'u dake kallonsu tayi d'an tsaki, kabari wlhy ya Fharuk, yaronnan yana d'aukar hankalinmu, shi yasha barcinsa da rana, mukuma yahanamu dadaddare.
Ya Umar yazauna akusada ita yana rungumota jikinsa, acikin kunnenta ya ce, "sorry momy zamu daina wata rana aii?."
Baki ta tunzuro gaba, o bama zaka masa fad'aba? Saidai ka goyida bayansa kenan?.
Dariya tabashi sosai, Dan haka yadara, yakuma matseta sosai yana dariyarsa, kai my Husna kinada abin dariya wlhy. Yanzu miye abin fad'a ga Fodeyo Dan ALLAH.
hummm zaka fad'i haka kuwa, tunda bakai yake hanawa barcinba, wani lokacinma saiyayi wajen Rabin kukan kake zuwa.
Hannayensa yasa yaruk'o fuskarta suna kallon juna. lumshe idanunta tayi Dan hango buk'ata kwance a idon mijin nata. Aii tama yabama k'ok'arinsa sosai wannan karon, Dan rabonta dashi tun ana jibi zata haihu. Kusan sati uku kenan......
Jin bakinsa akan nata yasaka tunaninta tsayawa cak waje d'aya.

Hummm su ya Umar fa andad'e ba'a gamuba🤐.

Ganin zai zarce gona da iri yasakata rik'e hannunsa. Shima saiya dakata da zagayen dayakeyi da hannunsa ajikita d'in, Dan yatuna akwai d'inki tareda ita. Wasa yaciga dayi da bakinta harya d'an rage zafi sanan yazube akatifar yana maida numfashi. Ahankali tazame itama ta kwanta gefensa, 'yan dabaru take masa irin namu na mata dakakanyi idan kana al'ada. Luf yayi dan sak'wanninta na isa agareshi.
Saida ta tabbatar yasami nutsuwa sannan tabarsa, gefe takoma tana kallonsa, yayinda shikuma ya duk'unk'une waje d'aya yana sauke numfashi.
Yad'an bata dariya amma tadake dankarta tsokanosa.
Bayan kamar minti 10 yad'ago yana kallonta da rinannun idanunsa, ahankali ya ce, "ngd my Husna, ALLAH yayimiki albarka.
Murmushi tamasa mai kwantar da hankali, tareda wani salon kallo, saikuma tarufe idonta, Dan taji kunya.
Yasauke ajiyar zuciya yana murmushin shima, mik'ewa yayi ya ce, " ina zuwa."
Ganin yanufi hanyar bayi ta ce, ''yaya mukam tafiya zamuyi kafin mama tafarga bama nan."
Juyowa yayi ya kalleta, babu wani mama taga bakwa nan, to tayaya kuka fito yanzu.
Yaya wlhy barcifa takeyi, kuma nasan zata iya tashi tunda bata kwanta gaba d'ayaba.
Dawowa yayi yana dariya, ya d'auki fodiyo ya manna masa kiss, my son kafad'ama kakarka iyayenkafa suna buk'atar jin d'umin juna.
Idanu Asma'u tazaro waje tareda mik'ewa zumbur, yaya wa kake gayama hakan?.
Dabaki yanuna mata fodeyo.
Kanta kawai ta jinjina tana fad'in kaga banishi mutafi, saida safe.
Bai bata fodeyon ba, amma yad'an rage fara'a, towai saurin mikeyine? Koma maganar dana kiraki Dan ita bamuyibafa, jiba agogo ko tara batayiba.
Asma'u ta langa6e kai gefe, kai yaya ka tausaya mini plss, ALLAH inajin kunyar mama ainun.
To naji muje falo muyi maganar saiki tafi.
Babu yanda zatayi dole tabishi falon dantaji maganar dazasuyi d'in...........

*_(((S))).....2018_*
*_I love you so much my fans_*
[1/2, 7:48 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

*_page→67-68_*

..........Su Uncle Abdullahi sunyi bincike akan mazajen nasu Suhaima, duk dadai binciken yad'an nuna musu matsaloli.
Dan haka suka kira mom dasu Lubna suka shaida musu. Lubna da suhaima suka bad'ama idonsu toka babu kunya sukace sudai zasu auresu ahaka. Babu yanda su Uncle habeb suka iya dasu Dan aganinsu auren yafi yawon gararin dasukeyi.
Cikin sati d'aya komai ya kammala, antsaida biki sati biyu kacal. Sai alokacin Ameer yaji labari, masifa yaytayi, ya ce, "kuma babu abinda ya shalleshi. Ransa a6ace yatashi yana fad'in mom dama nazo na sanar miki jiddah ta haihu d'azun, amma 'yar batazo bada raiba.
Baki mom ta ta6e ta ce, " ALLAH ya k'yauta gaba."
K'ala baice da itaba yakad'e rigarsa yafice.
Suhaima & Lubna suka raka bayansa da harara suna zagi. Mom bata hanasuba, Dan itama yanzu haushi. ameer d'in takeji ainun, musamman yanda ya janye kansa daga garesu, komai saidai matarsa.........

★★★

Afalon suka yada zango, ya Umar yazauna saman 2sita, ita kuma Asma'u tanufi kujera mai kallonsa zata zauna.
Hannunta ya kamo, tajuyo tana kallonsa, da ido yay mata nuni da gefensa. Itafa harga ALLAH fitinarsa take gudu bawani abuba, amma babu yanda zatayi dole tazauna kamar yanda ya umarceta.
Juyowa yayi yana kallonta sosai, itama saita nutsun, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi.... Kuma yak'i magana.
Ganin haka Asma'u tad'ago ta kalleshi, muryarta a sanyaye ta ce, ''Yaya ina saurarenka.
Kauda kansa yayi daga gareta yana dariya k'asa-k'asa, zuwa can ya ce, "to abani abinci mana."
Batareda ta tanka masaba tasauka k'asa ta shirya masa abincin, Dan tasan yafison cin abinci ak'asa.
Fodeyo ya mik'a mata sannan ya sauka k'asan.
Anutse yakecin abincinsa, lokaci-lokaci yakan d'ago yakalleta yana murmushi. Itakuma ta zun6ura baki gaba tana nuna masa agogo, dan bata k'aunar mama tagane tannan.
Ga ya Umar yanata wani cin abinci a yangance tamkar mace.
Yana kammalawa tafara gyara wajen, kwanukan ta kwashe tafita dasu zata kai kicin sukai karo da mama a babban falo.
Kallon tuhuma tabi Asma'u dashi, itakuma tayi k'asa da kanta tashige kicin, duk kunya ta rufeta.
K'in fitowa tayi, har saida tajiyo mama tashiga d'akin ya Umar sannan. A hanzarce tashige d'akinta. Hasiya tabita da kallo tana fad'in yaya Asma'u lfy kuwa?.
Bata bata amsaba tashige cikin bathroom.
Dariya ta kufcema Hasiya, ahankali ta Ce, "ALLAH yak'ara muku aii."
Har mama tadawo d'akin d'aukeda fodiyo Asma'u takasa fitowa daga bathroom. Itama mamar batabi ta kantaba ta kwantar da yaron ta kwanta.
Saida Asma'u tagaji Dan kanta sannan tafito cikin sand'a tayi shirin barci ta kwanta, dama mama afalo take kwana..........

*_bayan kwana biyu_*
Bayan kwana biyu akasha suna. Anrakwashe an kwalle kuwa, munsha bidiri harda bired'e.
Mama kuwa tunda daddare tagudu, aka maye gurbinta da inna baito k'anwar maman.
Asma'u taji dad'in hakan, Dan Dama tana tsoron ya Umar gsky. Kar ganin babu kowa agida yamata aika-aika, gata da d'inki ajiki🤪.
Zuwa dare taron suna yatashi lafiya, su Asma'u sun samu alkairi sosai, fodiyo yayi goshi.

★★★
Su Lubna ma anata shirin biki na garari, tamkar wata budurwa🤭.
Hakama mom bikin ake shiri sosai, aranar alhamis aka sakasu a lalle, juma'a sukayi kamu, ranar Asabar d'aurin aure.

____★______★______★_____
Ranar juma'a da daddare ya Umar yana gidansa wajen 8pm. Yabarsu Harris a shago Dan harsun dawo sunbar muktar da yazeed a mall, saikuma ma aikata sababbi da aka zuba masu dutyn dare.
Asma'u da Hasiya, inna baito duk suna afalon, ya Umar da inna baito dai hirarsu sukeyi akan rayuwa. Asma'u da Hasiya kam hankalinsu nakan kallon film d'in Kalan dangi, sai dariya suketa zubawa.
Fodeyo na goye abayan Hasiya, tunda aka masa wankan yamma yaketa barcinsa.
Sallama suka jiyo daga k'ofar falon, ya Umar ya amsa tareda bada Umarnin shigowa, Dan yaji muryar Sadam Ce.
Sadam yashigo ya gaida inna baito, ya gaida ya Umar da Asma'u.
Hasiya ta gaidashi.
Wata farar ✉ ya mik'ama ya Umar, Yaya gashi wanine yakawo yamzu wai abaka.
Ya Umar yakar6i yana jujjuyawa cikeda mamaki, shikam wazai kawo masa letter yanzu?.
Sadam yaymusu sallama yakoma shago.
Ya Umar ya ajiye takarda yacigaba da hirarsa da inna baito. Saidai k'asan zuciyarsa nata zungurarsa akan ya duba. Warwarewa yayi yabud'e saiga IV ya fad'o, yazaroshi yafara dubawa.
Murmushin takaici yad'anyi Dan ganin sunan Luban da Hafiz ajiki, wai harma gobe d'aurin aure su.
Acan k'asan zuciyarsa kam abin ya k'ona masa ransa. Amma yadake, Dan bayaso su Asma'u su fahimci komai.
Tundaga nanma saiyaji hirar ta gunduresa. Sallama yayma inna baito yashige d'akinsa.
Asma'u kam tuni ta karanto damuwa afuskar mijin nata, tunda aka kawo masa takardar dama hankalinta na kansa, so take tabishi dantaji matsalarsa, amma kunyar inna baito ta hanata.
Inna baito babu ruwanta, bakamar mamaba, bakomai take saka musu idoba. Saidai idan taga rawar kan Asma'u tayi yawa saita taka mata birki, ta hanyar tuna mata takula da kantafa. Wannan yakansa Asma'u kama kanta.
Chapter 36 · 0% Book details