← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 44

Sashe 31

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

*_page→57-58_*

..........Bikin Mufida ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro.
Ya Umar dai baice dasu komaiba, ko kwayar shinkafa baikai gidanba, dukda mama tamasa magana.
Cemata yayi baida kud'i, kuma ba yaya Abubakar duk yace zaiyibane?.
Shiru tayi dantasan inda maganar tasa tadosa.

Har ana gobe d'aurin aure babu wani abin arzik'i daya sauka gidan.
Babu kayan miya bare nama kokuma wanidai Abu daya danganci abinci har hud'u na yamma kuwa.
Ana nan zaune jigum-jigum.
Kowadai yasan al'adar makwafta da danginka nakusa sukan shigo domin rage aiki ana gobe d'aurin aure.
Gakuma gida cike damk'an da dangi na nesa wad'anda tun ajiya suka fara sauka gidan.
Ana nan zaune jigum-jigum kowa yana raba idanu yaga ta inda abinda ake jiran zai 6ullo. Cikin amincin ALLAH saiga yi anfara shigowa da kayan gado na Mufida.
Nan take kallo yakoma sama, mamaki al'ajabi yacika mutane, kayan gadone irinna da-da d'innan, kuma kallo d'aya zaka musu kagane tsofaffine akaima kwaskwarima kawai. abin mamakin baigama k'arewaba saida aka dire rabin kwandon tumatur, da attarugu da tattasai acikin yellow d'in leda mai layi-layi, sai alayyahu buhu guda maicin arba'in🙊.
Saikuma ga garin tuwon dabai wuce kwano ashirinba, gefe kuma da shinkafa 'Yar Hausa mai tsakkuwar tsiyarnan dabata wuce kwano ashirinba itama.
Kowa yayi cirko-cirko yana kallon ikon ALLAH, Saiga ya Abubakar yashigo saiwani bud'awa yakeyi yana washe hakwara, shi a adole yayi abin arzik'i yau.
Sai gaida mutane yakeyi washeda baki, amma ganin kallon dasuke masa saikuma jikinsa yayi d'an sanyi.
Yakai dubansa kan mama da inna, sumadai kallonsa sukeyi cikeda mamaki, amma a can k'an zuciyar inna tana fad'in ALLAH ya k'ara.
Inda suke yak'araso, har yanzu bakinsa awashe yake, dukda jikinsa yayi la'asar. Mama inna! gafa kayannan sun iso, kunata kirana mutane suna jira sufara aiki ko?, wlhy inacikin kasuwa nayi matuk'ar busy, gashi dak'yar nasami motar data d'akko yakayan gadonnan, kiranma dakukemin yasakani azamar tahowa, kaji na nan za'a kawo guda Biyar manya-manyanema wlhy.
Inadai fata komai zai wadatar da kowa?, kuzo kuduba kayan gadonma, kafintan ya iya aiki wlh...........
Hannu mama tayi saurin d'aga masa dan surutunsa yafara addabar kunnenta.
Hawaye suka zubo bisa kumatunta, cikin shashshekar kuka ta ce, "Amma Abubakar kaji haushin rayuwarka, kaje, nidai kawulak'anta ko? babu komai ngd.
ALLAH sarki Umaru ALLAH yayi maka albarka. Basai mutum yamutuba ake tuna alkairinsa.
Dama duk Wanda yagaza godema ALLAH na tabbata zai godema azabarsa.
Banga laifinkaba abubakar saidai nawa, yau ga abinda halina ya jazamin, ALLAH kamin ni'ima maimakon nagodemaka saina butulce, ya ALLAH ka gafarceni, natuba ALLAH, wlhy natuba.
BakI ya Abubakar yata6e waike mama miya kawo wad'annan surutan ne haka?.
Ubankane yakawosu matsiyaci kawai.......
Bata k'arasaba inna ta to she mata Baki tareda janyeta suka koma baya saboda idon mutane, ya Abubakar baifasa bin bayansuba. Shima ya Umar saiya biyo bayan ya Abubakar dan shigowarsa gidan kenan shima, amma yaga dukkanin kayan dake zube a tsakar gidan, harma yayi gamo damai kawo kaji ak'ofar gidan.

Lafiya kuwa inna? Maganar ya Umar tadaki kunnuwansu.
Atare suka d'ago suna kallonsa, mama tasake fashewa da kuka tana koroma ya Umar bayani dalla-dallah.
Shiru yayi yana saurarenta, tausayinta yacikama masa ciki, kafin ya ce, " wani abu saiga Abba yashigo shima afusace.
Ganindai komai zai kwa6e agaban mutane inna ta ce, ''sushiga d'akin Abba.

Zaune suke suduka a falon Abba, wannnan karon harda Harris da mufida da Rafi'a.
Inna ce tayi magana duk tana bin kowannensu da kallo.....
Ita gsky d'ayace, kuma daga k'inta said 6ata, lallai inamai jaddada muku Abubakar bashida wani laifi, laifinkune wanan, tunda tun farko kune kuka d'ora yarannan akan wannan mummunar tarbiyyar.
Kuna Nuna banbanci akan 'ya'yanku saboda wane yanadashi, wane bashidashi. Kund'auki dukiya tamkar itace jigon rayuwa. Kudubafa halin da Umaru yashiga a watannin baya, amma acikinku babu Wanda yata6a waiwayarsa yasan yaya yaci, balle ya yaciyar da iyalinsa. Bak'aramin tashin hankali yaronnan yashigaba, badan mai tawakkali bane Aida yanzu an mance kamanninsa ko?.
Amma maimakon kujawoshi jikinku, kuringa kwantar masa da hankali, saikukayi watsi da labarinsa kuka kama Abubakar mai kud'i kuka rik'e ko?.
Wannan wace iriyar rayuwace haka?, aurenfa mufida aka saka agidanna amma Umaru baison komaiba akai saboda son zuciya irin naku. Kuji tsoron had'uwarku da ALLAH mana, kufa iyayene masu tarbiyyantarwa bamasu ruguzarwaba, ALLAH fa baya d'orama bawansa abinda bazai iyaba.
Shin ku'a tunaninku kunada wata dabara ta gujema talauci kenan?.
Hummm shidai Ubangiji aiba abokina wasan wani shege bane.
Ai yanzu ba tsinar Abubakar zaku hauyiba, hak'uri zakuyi da abinda yakawo ayi bikin haka, arurruma akaita kowa yahuta......
A'a inna idan ya Abubakar zaibani rancen koda dubu d'ari biyarne sai ayi komai yanda suke buk'atar d'in......
Carab ya Abubakar ya kar6e zancen, a INA naga wata dubu d'ari Biyar in? Kokuwa kud'in kasuwata zan gird'e nabaka rance saboda kanaso ayi biki waje-waje?.
Wlhy Umar kafita idona narufe, yanzu wannan siyayyar dakuke rainawa tawajen dubu d'aricefa. Ko kayan gadonnan hallidu kafinta a dubu arba'in da Biyar yayimini su babu Ragin ko sisi wlhy.
Ince yanzudai inna tagama wa'azi akan rashin godiyar ALLAH ko?....
Ba godemakane ba a yiba ya Abubakar, kawaidai INA buk'atar rancenne.
To banidashi d'an jonin masifa, kaid'in baca akayi ka saida mall d'inkaba? Ina kakai kud'in? In ba neman alagidigo da hankalin mutaneba kakeyi?.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, ya marairaice murya, (amma a can k'asan zuciyarsa dariyace ke bal'in cinsa, daurewa kawai yayi ya gimtseta) ya Abubakar bawai inayin Alagidigo da hankalinku baneba, har yanzu wad'anda suka sayi wajennan basu bani kud'in baneba.
Amma munyi alk'awarin nanda wata shida zasu bani adunk'ule, dan banason kud'i gutsin-gutsin.........
Kai dallah sauraramin, wlhy Umar kafita sabgata nasha iska, inbanda raini taya zanyi nad'auki dukiyata nabaka har tsawon wata shida, nikuma nazauna fanko, saboda inajin tsoronka, angaya maka nid'in sallamammene ko shashasha?........
Mamace tak'atse musu zance cikin raunin murya, kabarsa Umaru Shiba sallamamme baneba, nasan babu yanda za'ayi nunkufurci irinna Abubakar yabarsa baka bashi.....kuka yahanata k'arasawa.
Abbah dai yayi shiru, dan tsorone fal ransa, idanfa Umar baisamu kud'innanba dolene shizai nemosu, tundadai mufida diyar cikinsace, atsarima shiya halatta yayimata kayan d'akin. Wani haushin Abubakarne ya kuma tunik'e zuciyarsa.
Agefe kuma dariya na cin zuciyar inna da Harris, dan sunsan ya Umar yanayin pretending ne kawai.
Rafi'a da mufida kam sai ballama ya Abubakar harara sukeyi, karma mufida taji labari, dan zuciyarta akuntace take, wai itace za'akai gidan miji da kayan gado nawajen halladu kafinta?.
Ita bamatasan yanda ya Abubakar ya tsanetaba. Tafashe dakuka Wanda yadawo da hankalin kowa akanta, cikin kuka ta ce, "Abba aidai kai kanada kud'in yimini, kowadai yasan halin da ya Umar yake aciki? Inhar ba'a tausaya masaba to ai ba'a tsine masaba. Niko wlhy Indai kayan wajen halladu kafinta za'a kaini dashi to na hak'ura da auren, ta tashi fuuuuu tafita tana kuka.
Babu wanda ya iya cewa komai, daga nan ma suma taron ya watse.
Ya Umar ma gidansa yakoma yay kwanciyarsa, dama kansa namasa ciwo.
Asma'u kam tana gidan bikin, bama tasan wainar da'ake toyawaba.
Sudai makwafta suka hau gyara abinda yasamu, masu gulma nayi masu tu'ajjibi nayi, harda masu dariyar mugunta dan kowa yasan mugun halin mama a anguwar.
Zuwa bayan isha'i aka kammala miyar dataji uban alayyahu ko kayan miyar ba'a gani saboda yawan alayyahun.
Tun adaren aka kusa shanye rabin miyar ma, mama tamkar tayi hauka dan bak'in ciki, tarasa inda zata tsoma kanta taji sanyi, gashi batada ko sisi, dan bata ta6a tunani ajiye wasu kud'iba saboda aurennan, tasaki jiki komai Abubakar zaiyi.
Abba madai hankalinsa atashe yake, dukda shida yanada 'yan kud'insa amma mak'o da ganin k'yashi yahanashi fiddosu afita kunya.

Adaren mama da inna sunkira ya Umar yafi sau hamshin-hamsin amma yak'i yad'aga, hakama Abba yakirashi yafi ak'irga amma bai d'agaba.
Hankalinsu dukya tashi, musamman ma inna.
Ita duk zatonta ya Umar yayi pretending ne, fitar dayayi zaije yayo sayayyane, amma har shad'ayan dare babushi babu alamarsa.
Ya Umar kam yana kwance agidansa, kuma duk kiran dasuka masa yana kallo ya sharesu.
Duk kiran daya shigo saiyayi murmushi sannan ya ce, "inna mama Abba kufayi hak'u wannan ba Umar d'in dakuka Sani bane, na yanzu ya canja, yasan dad'in dukiya shima, ni babu abinda zan muku, koma wajen d'aurin auren babu mai ganina.
Wannan zai zamemuku izina aii.
Inna ki gafarceni wannan karon kema bazan saurarekiba.
Dayagaji dajin wringing d'in wayar saikawai yamaida wayar salient........

*_washe gari_*
Har kusan 11 babu wani canji agidan, mutane sun sami abun tsogumi sai gulma sukeyi, harda cikin 'yan uwan mama danasu inna.
Zuwa yanzu mama tayi lak'e-lak'e, tayi kuka da nadama har babu iyaka, tasandai yau kunya zasu shatane bata wasaba kam.
Amaryama kuka takeyi rurus, ko wanka tak'i yarda tayima, ta tubure akan tafasa aurenma gaba d'aya, anyi lallashin duniya tak'i sauraren kowa.
Har shabiyu babu wani bayani, gidakam haryama fara d'inkewa da mutane, wasuma badan ALLAH sukazoba, sunzo ganin kwakwafne tunda tun ajiya labari yafara zaga anguwar.
Mutane na tsaye tsirko-cirko akan mama data suma. Dan tashin hankali, ko abincin daza'aci agidan babu to, d'an Wanda Ya Abubakar yakawo ana gama dafawa tun'a gindin murhu mutane suka kwasheshi. Wannan 6acin ran yasaka mama zubewa.

Ana cikin haka sai akaji k'ugin motoci ak'ofar gida. Kafin mutane suyi wani yunk'uri anfara shigowa da manya-manyan kuloli na abinci. gefe kuma ana shigiwa da kayan gado na gani na fad'a.
Ai sai mama ta tashi tashiga jerin 'yan kallo.
Saida aka shigo da kula kusan d'ari ta abinci, gakuma kayan gado na nunawa a sa'a, saikuma ga kayan kichin suma akwalayensu.
Inna dai data kasa hak'uri saida tamatsa tana tambayarsu waya aikosu?............

Kuyi manage da wannan.

*_(((S)))........2017_*
*_I Love you all_*
[12/28/2017, 6:35 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

*_page→59-60_*
Chapter 31 · 0% Book details