← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 44

Sashe 34

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_Asma'un ya Umar! ALLAH yasa afito lafiya kihaifama ya Umar d'inmu d'a ko 'ya maikama dashi😥._*
Ameen

_kowa yay shiru na second 1 Dan nuna jimami😂_

*_(((S)))........2017_*
*_Luv u all._*
[1/1, 3:05 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

*_page→63-64_*

..........Sai wajen 1:30pm su Dr Al-ameen suka fito, kowa yana yarce gumi. 'Yan uwa sukayi Kansu suna tambayar Asma'u harma da abinda ta Haifa.
Hannu kad'ai Dr Al-ameen ya iya d'aga musu, cikin hanzari yashige office d'insa. Ya Umar dake binsa abaya ya ce, "Dr matatafa?.
Karka damu, muna fatan nasara, amma muna neman jini da gaggawa.
Dr kud'ebi nawa kawai. Ya Umar yay maganar cikeda hanzari.
Wasu Abubuwa Dr Al-ameen ya d'auka suka fice, kai tsaye wajen d'ibar jini suka nufa. Cikin amincin ALLAH jinin yazo d'aya kuwa, d'iba akayi aka tace sannan cikin hanzari Nurse d'in tad'auka ta kaima Dr Al-ameen......

Yamzuma saida suka kwashe kusan minti 40 sannan suka fito. Yanzukam akwai canji dan fuskokinsu a sake suke.
Duk mik'ewa sukayi ayanzunma, tunkafin suce wani Abu Dr Al-ameen ya ce, "Alhmdllh congratulations, ansami baby boy." 'Yay maganar yana matsawa gefe, Nurse d'in dake d'aukeda babyn ta bayyana.'
Gaba d'aya sukayi cahhh akan Nurse d'in, kowa nafad'in Alhmdllh.
tamik'a musu k'aton jaririn Wanda kallo d'aya zaka masa ka gane dolene yabama mamarsa wahala saboda girmansa. 'Yar rige-rigen d'auka akeyi, ALLAH dai yabama mama nasarar amsarsa.
Ya Umar kam wajen Dr Al-ameen yamatsa, Dr matatafa?.
Murmushi Dr Al-ameen yayi masa tareda dafa kafad'arsa kwantar da hankalinka baban baby, madam ma tana lafiya, yanzu haka anashirin maidata d'akin hutune danta huta.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, Ahankali yafurta Alhmdllhi Ala kulli halin. Dr zan iya ganinta kuwa?.
Babu damuwa muje narakaka dai ka ganta, inaga hankalinka zaifi kwanciya.
Ya Umar baice komaiba sai murmushin dakan k'awata fuskarsa dayayi.
Atare suka shiga d'akin da akakai Asma'un, su hud'une ad'akin, ya Umar yama sauran sannu sannan yak'arasa gaban gadon da aka kwantar da Asma'u.
d'aure take da bedsheet fari sal, said'an d'igo-d'igon jini dayad'an 6atashi, amma ansaka mata k'aramin hijjabi shima fari, idanunta biyu kuma tana iya magana, Nurse natsaye agefenta tana saka mata jinin da aka d'iba ajikin ya Umar Dan k'ara mata.
Ya Umar yak'arasa gaban gadon, yaja farar kujerar dake gefe ya zauna, hannun Asma'u yakamo yarimtse anasa, my Asmah sannu kinji.
Bata iya amsashiba, saidai idonta na kansa, sai hura hanci takeyi. Yamatso sosai yashafa kanta yana fad'in ALLAH yayi miki albarka kinji. Kad'an tad'aga masa kanta, muryarta can k'asa-k'asa take magana. Bayajinta, Dan haka yamatso da kunnensa kusada bakinta.
Ta ce, ''Yaya k'afata nanan kuwa? dubamini."
Murmushi yamata, yakuma shafa kan nata, k'afarki nanan My Husna. bakijintane?.
Yanzuma saida yamatsar da kunnensa sannan yaji mitake fad'a. ALLAH jinake kamar babu k'afar.
Ya Umar ya kalli Dr Al-ameen dake tsaye yana gyarama Nurse d'in yanda zatayi.
Dr kaji wai jitake kamar k'afarta bata a jikinta. Ko akwai matsalane?.
No, babu wata matsala, allurar da akamatace takawo hakan, zuwa safiya zatajita daidai insha ALLAH.
Ya Umar ya ce, "tokinji."
Nanma kanta tajinjina tanad'an lumshe ido.
Dr Al-ameen ya ce, "mubarta inaga zatayi barcine".
Ok ya Umar yafad'a yana mannama Asma'u kisses agoshi. Sannan suka fice.

Zuwa yanzu kowa yad'auki baby daketa barcinsa, suna zuwa mufida amarya ta mik'ama ya Umar babyn tana fad'in Yaya ga bak'on duniya.
Murmushinsa ya fad'ad'a, yakar6i yaron maicikeda lafiya, kiss uku ya manna masa afuska sannan yarungume abinsa yanajin wani farinciki na ratsa dukkan ga6o6in jikinsa.
Yakai minti kamar 5 ahaka, kowa yanata kallonsa cikeda tausayi, sunsan yanadason yara, amma aka rabashi danasa.
Bakinsa ya manna akunnen yaron yaymasa hud'uba, a la66ansa ya furta ALLAH ya raya *_Usman Fhodeeyo_*.

🤗nikad'ai najishi, Dan haka na ce, " Ameen ya Umar🤓.

Babu Wanda aka bari yashiga gunta har magriba, bayan magribane kuma ya Umar ya ce, "duksu tafi hakanan."
Badan sunsoba suka fara shirin tafiya, Anty Saratu, Anty Sa'a, mufida, Anty Saddiqa, fatee, Rafi'a, hasiya.
Mama kad'ai za'a bari anan, Rafi'a da hasiya ance subi fatee gidan inna, Dan ita batazoba, tama mama kara.
Kowa yaje yaga Asma'u dahar yanzu take barcinta sannan suka tattafi.

9:30pm
Mama ta kalli ya Umar da Harris, muktar, Sadam, yazeed da matarsa dasukazo suma tun bayan magriba, ta ce, "yakamata kutafi hakanan dare yayi, bakamar su yazeed kuda kuka baro yarama.
Yazeed yay murmushi mama aisuna tareda mai aiki babu damuwa.
Eh dukda hakadai yakamata kutafi, ALLAH yasaka da alkairi, yabada ladan zuminci.
Gaba d'aya suka amsa da Ameen.
Muktar yamik'ama mama jaririn daketa barcinsa nannad'e a showal. Sallama sukai mata suka fice, amma dana kalli fuskar ya Umar sainaga bahaka yasoba. Amma babu yanda ya iya, dan maza basa jinyar mata awajen, saidai mace 'Yar uwarka. Shima namiji haka.
Saidasu yazeed suka tafi sanan suma suka shiga mita suka tafi......
Ya Umar duk saiyaji gidan babu dad'i, amma fuskarsa cike take da fara'a na farincikin k'yautar da ALLAH yamasa yau. Aikam kusan kwana yayi yana sallah da mik'a godiyarsa ga sarkin sarakuna.

★★★

Washe gari tundaga sallar asuba ya Umar ya koma gida yay wanka a gaggauce yay shirin tafiya asibitin, kai tsaye asibitin yanufa. Saida yafara zuwa suka gaisa da Dr Al-ameen sanan yatafi d'akin da aka kwantar da Asma'u.
Tana zaune akan gadon, tajingina da filon wata Nurse tana taimaka mata wajen bama babyn nono.
Mama kuma na zaune akan kujera tana shan shayi (su mama babu juriyar yunwa😉lol).
Kamshin turarensa yacika d'akin, Asma'u dabatasan da shigiwarsaba tad'ago kanta. Murmushi yamata Wanda yasakata jin wani sanyi aranta, saima tadainajin zafin shan nonon da yaron keyi.
Rissinawa yayi yagaida mama sannan yakoma yabi sauran gadajen suma yana gaishesu.
Abakin gadon yazauna kusada k'afafun Asma'u, yad'auki yaronsa da'aka kwantar agefe bayan yasha nono yak'oshi. My Husna! Ya jiki?.
Cikin sanyin murya ta ce, "Alhmdllh, ina kwana?."
Lfy lau, kuntashi lfy?.
Kanta ta jinjina batareda tayi maganaba.
Ya Umar yamaida kallonsa kan mama yana fad'in mama babu dai wata matsala ko?.
A'a wlhy, lafiya lau muka kwana, shima yaron yanata barcinsa, yanzuma yatashi babu jimawa yad'an fara kuka, saikuma ga Nurse take kowa? tace yunwa yakeji abashi nono yasha, shinema kasamesu suna bashi.
To Alhmdllh, ALLAH yak'ara lafiya.
Ameen ya rabbi.
Ya Umar yakuma kallon Asma'u data zuba musu ido shida babyn cikeda sha'awa. Maman baby k'afar tadawone?..
Fuskarta tarufe tana fad'in kai ya Fharuk babu wani Maman baby.
Dariya yayi k'asa-k'asa dan yagane tanajin kunyar mamane.
Suna nan zaune Dr Al-ameen yashigo, saida yafara duba sauran marasa lafiyar d'akin, sumadai duk theater's aka musu, sanan yak'araso gadon Asma'u. Kan yaron dake hannun ya Umar yashafa yana fad'in my son katashi lfy a sabuwar duniyarmu?..
Ya Umar yay dariya, gashinan k'alau yanata k'yalla idanu.
Dr Al-ameen yak'arasa kusada Asma'u yana fad'in aii yaran yanzu da wayonsu ake haihuwarsu. Ya gaida mama sanan yayma Asma'u ya jiki?. Ta ce, "da sauk'i, saidai bayanta namata ciwo kad'an-kad'an da kanta.
Sannu yamata sanan yasaka Nurse d'in dake binsa amma bata d'azu baceba, takuma d'aurama Asma'u k'arin ruwa. Mama ta ce, "Ameenu bazataci komaiba ita Ma'un?.
A'a mama sai zuwa yamma za'a bata ruwan Lipton tasha kawai.
To ALLAH yakaimu lafiya.
Daga nan Asma'u takoma barci, dan anaso tahuta saboda kanta datace yana mata ciwo. Mama da ya Umar kam suka cigaba da hirarsu.
Kafin wani lokaci asibitin yacika da dangi, yaukam harda inna da baba da Abba akazo, matar ya Abubakar ma tazo, shima hardashi..........

*_bayan sati d'aya_*
Da safe aka rad'a sunan yaron bayan an idar da sallar asubahi a masallaci. Yaro yaci sunan Usman mahaifinsu ya Umar (ALLAH ya gafarta masa, ameen) amma za'ana kiransa Fhodeeyo. To ALLAH ya albarkaci rayuwar Duk wani jariri ko jinjira ameen.

Har yanzu Asma'u na asibiti ba'a sallamesuba, amma suna sakaran sallama ayau d'innan, Dan Alhmdllh jikinnata yayi k'yau. Batada k'an jiki, kuma kowadai yasan CS d'in yanzu ba'a wani dad'ewa a asibiti musamman idan anhad'u damai jarumta.
Tana zaune akan gadon abinci takeci (Dan yanzun tanacin abinci), yaron kuma yana hannun Anty Sa'a, mama da Anty Saratu da mufida sunata hirarsu.
Ya Umar yashigo shida yazeed da Muktar, saida suka gaida d'ayar matar data rage ad'akin, Dan yanzu su biyune kawai, ansallami sauran biyun.
K'arasowa sukayi, kowa ya ajiye ledar hannunsa sannan suka rissina suna gaida mama. Su Anty sa'a ma suka gaishesu, itama Asma'u haka, suka tambayeta ya jiki?. Ta ce, "Alhmdllh.
Mufida tatashi tajawo musu kujerun dake d'akin suka zauna.
Jaririn aka basu, har anmasa wankansa, yana cikin kayan sanyi masu laushi jajaye. Yazeed daya d'aukeshi ya ce, ''masha ALLAH Fhodeeyo".
Mama tawashe baki Dan farincikin sunan dayaci, ta ce, "lallai Ashe wanan mijin na katakone bana robaba?."
Dariya aka sanya duka, mama tad'ora dafad'in to ALLAH yaraya Usmanu.
Ameen suka amsa.
Muktar ya ce, "mama aidama na k'arfenema koda baici sunanba."
A'a rabanifa muktar, indafa baici sunanba tona robane, amma yanzu kun k'ara masa girma yazama na katako baikai na k'arfenba. Dan nasan bazaiyo jarumtar nawa Usmanun ba.
A'a mama karfa ki fidda rai, nangabafa shine mai kama miki sanda, Cewar mufida.
ALLAH ya tsareni mama tafad'a tana kaima mufida duka.
Kaucewa mufida tayi suna dariya.
Asma'u data d'ago ido saita kama ya Umar na kallonta. Baki ta murgud'a masa daga k'arshe. Ya nuna Kansa wai shi takema murgud'e?.
K'ara murgud'a masa bakin tayi sanan tad'aga kai alamar eh.
Shima Kansa ya jinjina wai aii zasu had'une.
Mufida da Anty Saratu dake kallonsu suka tuntsure da dariya.
Mama ta ce, "kai kukuma lafiyarku kuwa?.
Cikin dariya sukace k'alau mama, wata drama muke kallone.
Kudai kuka Sani mama tafad'a tana maida hankalinta wajen hirarsu yazeed da Anty sa'a.

Da yamma aka sallamesu. Kowa yayi farincikin faruwar haka kuwa, bakamar Asma'u, jitake kamar tayita tsallen murna.
Da mama ta ce, "awuce da ita gidanta, amma ya Umar yayta rok'onta akan a'a shidai sutafi gidansu, har itama mamar saita zauna kodan tasakama gidan albarka.
Da wanan dad'in bakin nasa mama ta ameence aka wuce da Asma'u gidan ya Umar.
Sun Tatar da gidan tsaf, dansu Rafi'a sunje sun gyara, nanfa makwafta sukaita shigowa dubata da jariri.............

*_(((S))).......2017_*
*_I love you all_*
[1/1, 3:05 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........
Chapter 34 · 0% Book details