← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 44

Sashe 35

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

*_page→65-66_*

..........Shiru momy tayi tamkarma bataji abinda Lubna tafad'aba.
Lubna tak'ara maimaitawa, Dan atunaninta mom batajitane.
Mom zanyi aure kwanannan nacefa.
Mom ta sauke ajiyarzuwa tareda maida dukkan hankalinta akan Lubna da Suhaima. Baby kinsandai banason shashanci, idan kinsan wanan maganar taki ba gsky baceba karki sake maimaitamin ita anan.
Suhaima da Lubna suka kalli juna suna murmushi, mom ALLAH kuwa da gsk baby takeyi, aure zatayi.
Murmushi mom tasaki awanan karon, Dan tagaji da gantalin da 'ya'yan natakeyi ana gulmarsu a anguwar. Ta ce, "Alhmdllh, aii aure shine mutuncin d'iya mace, naji dad'i sosai, kema Suhaima saiki fiddo da mijin ahad'a gaba d'aya ayi, nikaina mamarku auren zanyi Dan kare mutuncin kaina.
Atare Suhaima da Lubna suka had'a baki wajen fad'in mom aurefa kikace!?.
Mom tayi 'Yar dariya, kai kajimin yara, shin nawuce da aurenne?.
A'a mom, amma yakamata kima dad kara gsky, kik'arasa rayuwarki haka, tunda dai duk abinda kike nema ALLAH yabaki. Shiru tayi batace komaiba, zuwa can kuma tayi ajiyar zuciya, shikenan zan duba naga mai yuwuwa, shima Ameer idan yazo zamuyi maganar dashi. Amma ke baby waye mijin?.
Lubna tayi d'an tsaki, abokin wancan fak'irinne nada, Umar!.
Abokin Umar kuma baby?.
Eh mom, ammafa ada, Dan yanzu ko hanya basa had'awa dashi, Dan babu yanda za'ayi mai Arzeek'i da fak'iri suzauna a inuwa d'aya.
To, amma kina gani babu matsala baby?.
Wlhy babu wata matsala mom, Dan nikam ina sonsa, kuma kodan nak'ara haddasa bak'in ciki arayuwar Umar saina auri Hafiz.
Shike nan, ALLAH ya Sanya alkairi, saiki gaya masa yayi k'ok'ari su Gana da uncle d'inku Abdullahi, Dan banaso aja dogon lokaci, idanma san samune ayi bikin nanda k'arshen wata.
Lubna ta turo baki gaba, kai mom bagwara yaje wajen uncle habeb ba, kinsandai mugun halin uncle Abdullahi nan, 'ya'yansama bawani dad'insa sukejiba, sai ak'idar tsiya, shi adole (Ustaz).
Humm baby kenan, amma idan baki mantaba aii Abdullahi shine babba, yanagaba da mahaifinkima bare habibu. Nidai mom dukda haka uncle habeeb naza6a, yau kwana tarafa kenan Uncle Abdullahi yazo yagama mana cin mutuncin agidannan, kuma hardake, amma shine harkin manta, zaki d'au ragamar 'ya'yanki kibasa.
Baby aiba cin mutunci yamanaba, gsky yafad'a, kumanikam koda bazan d'auka dukaba zan d'auki tayin aure, kema Suhaima kifito danaki ahad'a duka kawai. Daga Suhaima har Lubna baki suka cuno gaba, ciki-ciki Suhaima ta ce, "nima aii Ramadan yace zaituro iyayensa."
Alhmdllh, amma naji dad'i sosai, insha ALLAH zan sanarma su habebun dakaina.
Daga nan taron ya watse, baima Lubna da Suhaima dad'iba....

Washe garin ranar mom dakanta ta shirya taje har gida suka tattauna da uncle Abdullahi. Yanuna jin dad'insa sosai, shima uncle habeb sun sanar masa. Shima sosai ya nuna farin cikinsa, Dan sungaji da zagin da'ake musu agari akan gararin da yaran sukeyi. (Sukuma harga ALLAH ba laifinsu baneba, suna iya bakin k'ok'arinsu). Amma ko kad'an su Lubna basa saurarensu, Dan tun mahaifinsu nada rai bawani ganin girman Uncles d'in nasu sukeyiba, tunda sunsan babansu dukya fisu kud'i. Hasalima alfarmarsa sukeci.
Sun yanke hukunci akan sati mai zuwa zasusa akawo kud'i, amma saisunyi bincike akan yaran tukunna.
Mom tamusu godiya sannan tatafi............

________________________
Suna zaune afalo kasancewar lokacin zafine, ko ina abud'e yake. Mamace takema Asma'u fad'a akan shan kunu dabata sonyi. Itadai Asma'u tayi luk'us Dan tasan batada gsky. sai Hasiya dake dariya k'asa-k'asa, Dan babu lalla6ar dabataima Asma'un ba akan shan kunun d'azu da rana amma tak'i, ai gashinan yanzu yahuce tanasha da tsiya ko.
Harara Asma'u tasakarma Hasiya tana tura baki gaba, mama kinganta ko?.
Nagantafa, cewa mama, amma babu abinda zance da ita tunda kece kika jama kanki. Ku yaran yanzu babu abinda kuka iya sai shan shayi da wainar kwai, yo ALLAH natuba ni nata6a ganin jego haka?. Shidai jegon farko inbaka ingantashiba aibazaka inganta nagababa ko? Kuma kayi wasa ahaka zaka taso sakaka, harma mijin yaringa gudunka, kullum ayita fama akan shan kunu, inbanda lalata bashine zaikawo ruwan nonoba yaro yasha yak'oshi.
Anty Sa'a tafito daga d'akin Asma'u tana dariya, dama tun d'azun suna aciki itada Anty saddiqa da anty Saratu suna saka sababbin punches da ya Umar yasa aka kawo d'azun da safe.
Tun d'azun suna jiyo diramar mama da Asma'u sunata musu dariya acikin d'akin. Yanzuma Anty sa'a tafitone tabama Hasiya kayan Fhodeeyo dazata wanke wad'anda sukad'anyi datti.
Yauwa Hasiya ga kayannan, tashi yamma nayi kok'yayi kigama.
To anty, Hasiya ta amsa tana kar6ar kayan.
Mama ta kalli Anty sa'ar, yo harkun gama jeren?.
A'a mama sauradai kad'an, inagama munkusa tashinku daga falonnan dan munkusa dawowa kansa.
To idan kun kammala ai saimu koma falon Umaru tundashi aii kun gama ko?.
A shikam mungama tun d'azun shida kicin.
Asma'u ta ce, "anty sa'a sannunku."
Yauwa ma'un mama sannu kema, tad'an rissina tana lek'en fuskar Fhodeeyo dake bayan mama. Mama! ALLAH kuwa kamannin fodeyo da Umar sako fitowa sukeyi, yaronnan haske kawai zai nunama Umar.
Mama tayi 'yar dariya, yoni sa'a aii kallon Usmanu nakeyi kamar sanda na haifi Umaru, har d'an banzan kukannan nashi na dare dayake hana mutane barci, haka Umaru ya wahalar dani da kukan dare nida mahaifinku, to d'an kwal uban shima gashinan yayo gado.
Dariya anty sa'a da Asma'u sukayi, Anty sa'a tashafa kan fodeyo, kanata barcinka sai dare yayi kahana mamummu barc.......
Shigowa ya Umar tahanata k'arasa maganar.
Ya rissina yana gaida mama, Asma'u tamasa sannu, suka gaisa da Anty sa'a itama. Yad'ora da fad'in anty sa'a sannunku da aikifa.
Yauwa Umar, ya shagon?.
Alhmdllh wlhy, dama zan tambayekine midami kuke buk'ata na hidimar sunan?.
Ai dukma mun rubuta komai, takardarma na d'akinka.
Okey babu damuwa.
Mama ta ce, "tonifa inaga zuwa gobe zan koma gidan mijina gsky."
Suduka suka kalleta cikin alamun tambaya. Ya Umar daya kasa daurewa ya ce, "haba mama miyasa?."
A'a babu komai Umaru, bazan zauna ananba har ranar suna aii, kumama alhmdllh jikin Asma'u yayi k'yau, inama laifi, yau kwananafa Tara agidanan, ga zaman asibiti damukayi na sati d'aya, aii abin ba hauka baneba.
Ya Umar yay murmushi batareda yace komaiba.
Anty Sa'a ta ce, "shikenan mama, amma kibari sai jibid'in da safe, tundadai sunan sai rana."
A'a insha ALLAHU gobe da daddare zan tafi.
Shiru duk sukayi, Dan sunsan halin kafiyar mama sarai.

Zuwa yamma lis suka gama gyara gidan fes, puneches d'in sunyi k'yau sosai, dukdadai basukai tsadar nada da Lubna takwasheba, amma wad'annanma babu laifi kam. Na d'akin ya Umar kujerune na leda bak'ake, da labuloli green, hakama carpet shima green, sai madaidaiciyar TV plasma dasuka ajiye zuwa gobe za'a nemo mai sakawa. Hakama cikin bedroom d'in komai kamar na falonne. d'akin Asma'u kuwa, lemon green & Orange ne, itama komai tsaf. A babban falo kuwa kujeru jaa da milk d'in labulayene dakuma ratsin jaa kamar kujerun, nanma kowa yagani dolene ya yaba saidai mak'iyi.
Mamace ta ce, "aidabasu saka na babban falon ba, dasun bari taro yatashi sannan, inba hakaba kuma duk za'a 6atasune. Sunyarda da shawarar mama kuwa, Dan haka sukace zuwa gobe da yamma sai a kwashe Dan yau sungaji ainun.
Bayan anyi magriba harris yazo ya maidasu Anty sa'a amotar da har yanzu Asma'u batasan tawayeba, Dan shima ya Umar d'in yakan had'a wata guda bai shigetabama, yafi hawa mashin lifan daya saya bayan bikin Mufida.

Yauma kamar kullum Hasiya taje takaima ya Umar abinci d'akinsa, akan sentar table d'in tsakkiyar falon ta shiya masa yau, sa6anin da datake jerawa akan tabarma. Sosai falon ya birgeta Dan haka takebin ko ina da kallo. Shigowar ya Umar tasakata saurin waigowa, sannu tamasa ya amsa shima yanabin falon da kallo, Hasiya falon yayi k'yaune?.
Wlhy kuwa yaya ya had'u, yamafi na yaya Asma'u kyau.
Dariya ya Umar yayi yana zama, ya ce, " kidai dage tajiki."
Itama dariyar tayi tana dafe bakinta, aikodai yaya bara nayi shiru, Dan yanzu Abu kad'an zakama yaya Asma'u tahau mutum da masifa.
Murmushi kawai yayi, amma baice komaiba yashige bedroom d'insa. Daga ciki ya ce, "rediyo jeki kiramin Husna, kuma tataho da fodeyo."
Fita Hasiya tayi tana zum6ura baki, dama idan tana zabga surutu haka yake cemata redio. Data tuno wani Abu kuma saitayi dariyar mugunta, tasan dawuya mama tabar Asma'u zuwa wajensa musamman yanzu da daddare, ko kad'an bata barinsu su k'e6e sukad'ai. batasan miyasaba itama.🤷🏽‍♀
Afalo ta iske Asma'u zaune a inda ta barsu, amma yanzu tanama fodeyo shirin barcine. Mama kuma tana kwance a doguwar kujera, harma barci ya d'auketa.
Zama hasiya tayi kusada Asma'u, cikin magana k'asa-k'asa ta ce, ''yaya Asma'u! ya Umar na kiranki, yace kuma kije da fodiyo.
Da sauri Asma'u ta kalli inda mama take, Alama tayima Hasiya data fad'a ahankali. Hasiya tak'unshe baki tana dariya k'asa-k'asa.
Asma'u batace da ita komaiba tak'asa sakama fodeyo famfas, tasaka masa riga mara nauyi saboda yanayin zafin garin, hoda ta shafa masa ta k'uraje, a wuyansa da goshinsa sannan ta nad'eshi a showal ta sa6ashi akafad'a tafice cikin sand'a da waugen mama dabatasan sunayiba.
Hasiya ta guntse baki tana dariyarta.😂
Chapter 35 · 0% Book details