← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 44

Sashe 20

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yayi daga kan sallayar yakoma kan katifar ya zauna saitin fuskar Asma'u. Sosai ya tsira mata idanu tamkar yau yafara ganinta, jiyake wata k'aunarta naratsa 6argonsa da jinin jikinsa. "ada yaso Lubna harma yake ganin bazai ta6a son wata mace bayan itaba, amma zuwa wannan ranar labarin yasha banban, dankuwa jiyake abayama baiyi wata soyayyaba, yanzune zaisan miye soyayyar, yanzune zai amayar da ita inda yadace, yanzune zaisan miye farinciki acikin soyayya. Ahankali yakai hannunsa saman d'an bakin Asma'u daketa barcinta. Zagaya d'an yatsansa yakeyi akai cikeda shauk'i.
Sannu ahankali Asma'u tafara motsawa harta bud'e kumburarrun idanunta akansa. Suna had'a ido tamaida nata idanun tarumtse gam.
Murmushi yayi tareda fad'in haba my Husna! bud'e idanun mana. bud'e ki kalleni da k'yau ni nakine ke kad'ai, zan kasance dake har Abadan Hayatee na.
Wani sanyin dad'ine ya kwarara azuciyar Asma'u, itakam yau wace irin godiya zatama Ubangijin talikai mai sassauya al'amura. Yanzunan ya Umar ne dabakinsa yake furta mata kalmomin nan? Ya Umar d'innan mai tsada da aji mijin Anty Lubna? Ya Umar d'innan da sonsa yazama garkuwar farincikinta tun tana k'arama? Ya Umar d'innan da takema kallon Wanda yafi k'arfinta abaya? Ya Umar d'innan daya mallake zuciyarta da dukkanin komai nata batareda yasan tanayiba? Ya ALLAH kaine Sarki mafi Girman iko da Rahma, ALLAH Kaine kake bayarwa ka k'ara batareda ka k'osaba.........hawaye sosai keta kwarara a kumatunta.
Ya Umar yakuma matsawa gareta zuciyarsa dukba dad'i, azatonsa har yanzu kukan abinda yay mata takeyi. Rungumeta yayi tsam ajikinsa, murya a raunane ya ce, "kiyi hak'uri my Husna! nasan ban k'yautaba amma ki gafarceni." ALLAH yay miki albarka, kisaka azuciyarki Umar Fharuk nataredake har Abadan. Yanda kika saka ruhina da zuciyata acikin farinci kema ALLAH ya dauwamar danaki Ruhin a farinciki. I love you so much my Husna.
Aii Asma'u batasan sanda tak'ara k'ank'amesaba tana zubda hawayen farinciki. Shikuma yana aikin shafa kanta da lallashi.
Saida tayi mai isarta sanna yad'auketa cak zuwa bathroom.
Ananfa akeyinta Dan Asma'u bazata iya tsayawa ya Fharuk yamata wankaba.
Tun yana had'a ruwan zafin daya d'akko daga kichin tagwada fita daga bathroom d'in, amma kamar yasan mitake nufi ya dinkare ko'ina na k'ofar.
Da d'an zafi sosai yahad'a ruwan zafin sannan yadawo da kallonsa ga Asma'u. Suna had'a ido tayi k'asa da kanta tana hawaye. Murmushi yayi ahankali yamatso gareta, murya k'asa-k'asa ya ce, " my Husna kincika shagwa6a. Kodai nakira Inna ko mama?.
Sosai tawaro idanu akansa. Saikuma wasu hawayen suka kuma gangarowa.
Tunawa batayi sallar Asubaba yasakashi sungumarta yasaka arobar daya had'a ruwan zafin, dama daga Ita sai riga iya guywa.
Wani zallo tayi tareda k'ank'amesa tana kuka. Wayyo ya Fharuk wlhy akwai zafi. Innata kice yabarni wayyo ALLAHNA.
Sake dannata yayi da k'yau yana murmushin wannan kuka. Afili ya ce, "Husna karfa kisaka gaban inna yayta fad'uwa, tun jiya kiketa kiranta. Ya Isa haka kada ki k'aremin sunan Innata!.
Zuwa yanzu tad'an daina mutsu-mutsun tashi, saidai hawayen dasuka kasa k'arewa. Saida ruwan yahuce yakuma zuba ruwan zafi, baibartaba saida ya tabbatar tagasu dak'yau sannan ya ce, "kin iya wankan tsarki?.
Kanta tad'aga masa kawai, har yanzu hawaye takeyi. Baifitaba har saida yaga yanda tayi, ya tabbatar tayi dai-dai sannan yanad'ota a tawul ya d'akkota kamar wata jinjira.
Akatifar yadireta, yagoge mata jikinta yasaka mata kayan data ware domin yin sallah. K'ara d'aukarta yayi yakai inda abin sallar yake.
Baibar wajenba saida ta kabbara sallar.
Dawowa yayi inda katifar take, yacire bargon. Ido yazaro waje Dan ganin yanda zanin gadon yad'an 6aci kad'an. Mamakine yakamashi, dama bakowace macece ake ganin jini a Daren farkontaba? Yasan Lubna tagirmi Asma'u amma ita jinin data zubarma har tsoro yabashi a lokacin. Saikuma gashi Asma'u ita babu sosai. Ubangiji mai iko, matanma akwai banbanci atsakaninsu kenan?.

*_hattara samari, kudaina d'aukar cewa dolene sai kunga jini adaren farkon matanku zaku yarda takawo budurci cikakke gareku. Mata kala-kalane, bakowacce bace ake ganin jini adaren farkonta. Mutanen da, suna aurar dayara suna k'ananane, shekara 12-13-14 kaga kuwa wad'annan yarane d'anyu dolene a iya ganin jinin. Kuma alokacin matan basa yawan yin abubuwan dazai saka burcinsu yin rauni._*
*_ayanzunkam bahaka bane, mafi yawanci ana aurar da mata 18-19-20-21-22+ ne, gakuma abubuwan 'yan matan kanyi dake saka buducinsu yin rauni batareda sun saniba. Yawan d'aukar Abu mai nauyi, horo da ake bama yara a makaranta, hawa mashin, tsallaka kwata, yawan tsalle-tsalle, musamman dayanzu 'yammata suka lalata kansu wajen rawa. Irin wad'annan abubuwan da dama dawad'andama ban lissafoba duk suna saka budurci yin rauni koda mace takasance ma'bociyar kamewa. Mata saimu kula. Kukuma maza Ku fahimcemu, bawai ganin jini face-face agado bane alamar mace takawo cikakken budurci gidan miji. ALLAH yasa mugane, ameen._*

Yaye zanin gadon ya Umar yayi zuciyarsa fes babu wani wasiwasi akan Asma'u, domin kuwa shine sheda akan tsam yasameta, bama k'aramar wahala yashaba wajen fasata. Lallai yakamata sauran maza irinsa su fahimci haka suma.
Asma'u kam tuni ta idar harta kwanta awajen.
wani zanin gadon yasake, dukda wannand'in bai 6aci dayawaba, amma baidace abarsaba. Yana canjawa ya d'akkota yamaida saman katifar dan barci takeyi sosai.
Zanin gadon yakai bayi yasaka a bokiti ya wanke tas yaje waje ya shanya. Yana gamawa yadawo d'akin yakwanta tareda rungume abarsa suka koma barci mai dad'i.

*_1:4pm_*
Sai k'arfe d'aya da minti hud'u ALLAH yabasu ikon farkawa kusan atare, amma Asma'u tariga ya Umar tashi, motsin tashintane ma yatadashi.
Tanajin motsin tashinsa ta lafe ita adole barci takeyi.
Murmushi ya Umar yayi tareda yimata cakulkuli.
Dariya sosai tazo mata, dukda zafin datake d'anji idan tayi motsi babba hakan baisaka ta dainaba.
Ganin yanda take dariya yasaka ya Umar dariyar shima. K'ank'amesa tayi sosai tana cigaba da dariyarta dafad'in ya Umar yi hak'uri Dan ALLAH, ALLAH kuwa abinnan babu dad'i.
Daina yimata yayi, yajawota jikinsa ya rungumeta tsam zuciyarsa fal farinciki.
Sunkai 30minutes ahaka yana gaya mata dad'ad'an kalamai wad'anda suka sakata k'ara ganin kimarsa a idonta. Dama can ita bataji haushinsaba, aganintama hakan zai iya zama sanadin dazaisa ya sota. Sa6anin da da ita keta fama da dakon sonsa a zuciyarta.
Bayan wani lokaci yad'auketa cak sai bathroom. Zille-zille tafarayi ita adole bazatayi wanka dashiba.
Shikuma yace bata isaba, aii daga yau tarema zasu ringa wanka, danshi hakan yana cikin tsarinsa. Ganin zata fita yad'ebo ruwa yazuba mata ajiki. Dole tatsaya awajen cak, shikuma yashiga yimata dariyar tsokana. Ta6ara tafara zuba masa shikuma yana lallashi har aka kammala wankan yad'akko kayarsa kamar d'azun.
Da k'yar tasamu ya yarda yatafi d'akinsa yabarta ta shirya itama.
Kowa shirinsa yayi mai k'yau.
Asma'u tad'an daure tagyara d'akinta da babban falo sannan tashiga kicin Dan nema musu abinda zasu saka abakin salati.
Ganin rana tayi sosai sai kawai tad'ora jalof d'in taliya da dankali. Tasaka busashshen kifin da ya Umar yasaya musu shekaran jiya. Cikin 'yan mintuna k'alilan gidan yacika da k'amshi ainun. Dama Asma'u gwanace a wajen abinci.
Ya Umar daya tsaya had'a wasu takardu yay shirinsa tsaf cikin shadda fara tas, dakakkiyar shaddace 'Yar ubansu, yad'inkata tun yana shanawa da naira. Shaddar d'inkin zamanine fetet, tayi masa k'yau aynun, yad'akko bak'ar hula yasaka, yasaka safa da takalmi bak'i sau ciki. Wayyo masu karatu tamkar ba ya Umar dake cikin k'angin rayuwaba. Idan kagansa zaka d'auka har yanzu ajik'e yake da laimar kud'i.
Fitowa yayi yanata bulbula k'amshi, tamkar Wanda yay wankan turare. Yalek'a d'akin Asma'u bata nan. Jin motsi akicin yasakashi nufar can.
Asma'u dake jera abinci akan tire Dan ta kammala komai tajiyo k'amshin turaren ya Umar ya yawaita awajen.
Lumshe idanu tayi ahankali tabud'e akansa, bak'aramin tafiya da ita wankansa yayiba. Shima tayi masa k'yau sosai. K'arasowa yayi cikin kichin d'in ya rungumeta, cikin kunnenta yarad'a mata, haba My Husna! Waya gaya miki amarya na aikin a irin wannan ranar?.
Fuskarta tashiga sinnewa a k'irjinsa ita adole kunya. Yad'ago fuskar tata a acikin tafukan hannunsa, idanunsa suna yawo bisa k'yak'yk'yawar fuskarta. Kiss ya manna mata agishi da hanci, ahankali ya furta ALLAH yay miki albarka my Husna. Ina k'yaunarki sosai.
Saida ta k'ara sinne kanta a k'irjinsa sannan ta ce, "nima haka yaya ina k'yaunarka."
Rungumeta yayi tsam yana juyi da ita Dan murna. Sundad'e ahaka sannan yad'auki tiren abincin sukaje falo.
Tare sukaci abincin dukda Asma'u akunyace take, ko ido batason suhad'a dashi.
Bayan sun kammala yatayata suka gyara wajen sannan ya ce, " bara yaje wajen Alhaji mai kano, dama k'arfe biyu yace yadawo.
Addu'ar fatan nasara da dawowa lafiya tamasa.
Shikuma ya ce, "taje ta kwanta tasake hutawa Dan anjima za'a k'ara irin amsar jiya.........
Aibata bari ya rufe bakinsaba takwasa dagudu zuwa ciki.
Dariya yafita yanayi da jinjina shirme irinnna Asma'u............

*_(((S)))........2017_*
*_Luv you all_*
[12/14/2017, 8:28 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*

*_page→41-42_*

..........Itama daida tashiga ciki gudun nata yabata dariya, Dan haka tayi dariya sosai harda rik'e ciki. ALLAH nagode maka daka nuna min wannan rana mai cikeda tarin farinciki. Wai yau nice da ya Fharuk manne da juna, yana gayamin kalamansa masu dad'i da tsada. Ya ALLAH ka d'orar mana da wanan farinciki har k'arshen rayuwarmu....

Ameen Asma'u.

____________________
Su Lubna ansha shagalin biki, kud'ikam sunyi kuka abikinnan, komai anyishi asarauce. Su Lubna kam ashiga wanan afita wanan. Dama d'inkuna sukayi na garari itada Suhaima.
Zuwa yanzu kam amarya tazo gida. Taroma yatashi kowa yakama gabansa. Su Lubna suna d'aki anata zabga barcin gajiya, gidan tsit kamar babu bil'adam acikinsa.
Sai can nad'an jiyo hayaniyar su twins ad'akinsu.
Can na nufa danna ganema idanuna. Aiko sune suketa tsalle-tsalle agado, duksun hargitsa d'akin. Babu laifi yaran sunyi girma sosai, ga kamanninsu da ya Umar sunfito sasai. Saidai Hassana farace. Usainace dai komai na ya Umar bata bariba, har dariya idan tayi kamar tasa...
Barisu nayi nafito Dan inada abunyi.....

____________________
Alhamdulillahi ya Umar yayima Alhaji Ahmad mai kano bayani gamsashshe akan rabuwarsa da mahaifin Lubna.
Dayake mutumne mai fahimta, saiya gamsu da komai, yakuma bama ya Umar hak'uri.
Kayi hak'uri Umar, da abinda suka aikata maka. Amma inada tabbacin babu laifin Alhaji awannan lamarin, saidai idan matarsace tazugashi. Nasan halinta batada kirki kokad'an, bataso kowa yara6i Alhajin Dan aganinta za'a k'are musu dukiya.
Chapter 20 · 0% Book details