← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 44

Sashe 10

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Zayyan yazo Asma'u tafito bayan ya aika kiranta, batayi zaton shibane Dan haka tafito cikin fushi, yayinda tayi tozali da Zayyan yaci wani uban wanka yana jingine da motarsa saita rikice Dan farinciki, cikeda zumud'i tak'araso garesa tana fad'in zayyan da gsk Kaine?, kokuwa mafarkin Dana saba yine?.
Zayyan yad'ago yana kallonta babu yabo babu fallasa, tun anan jikin Asma'u yayi sanyi Dan ganin halin ko in kula da Zayyan ya nuna agareta, jiki a sanyaye tace sannu da zuwa, bai amsaba amma yamik'a mata IV.
Cikeda mamaki ta amsa tanamai Kallonsa, tayi k'arfin halin fad'in zayyan wannanfa?.
Yatsine fuska yayi ya ce, "IV d'in aurenane nanda kwana 30 kacal, kiyi hak'uri tunda natafi ban sake nemankiba, wlhy nayi gamon katarne da tsaleliyar budurwa a can yayin karatuna, gata 'Yar masu kud'i, ke idai tak'aice miki ta kereki a komai na rayuwa, tun shekara uku dasuka wuce nadawo k'asarnan ALLAH bai bani ikon zuwaba saiyau, naga kuma bai daceba ace ansha bikina baki saniba shiyasa nakawo miki katin gayyata, nabarki lfy...
Yana gama fad'a yashige motarsa yabar anguwar tareda bud'a mata k'asa.
Ai Asma'u saikawai tayanke jiki tafad'i, ya Umar ne dayazo gaida inna yaganta kwance ak'ofar gida, da farko masifa yafara mata amma dayaga bata koda motsi sai tsoro yakamasa, yagirgizata amma shiru kakeji, anahaka saiga baba dasu hasiya, arikice suma suke tambayar lfy kuwa?.
Nima wlhy baba ban saniba, a haka na Tatar da ita, dasukaga magana bazata musuba suka kwasheta sai asibitinsu Dr jafar.
Natak'aita muku zance saida Asma'u tayi kwanta biyu assume sannan ta farfad'o, tashin hankali kuwa ba'a maganarsa wajen family d'inta.
Bayan kamar sati d'aya Asma'u tadawo daidai aka tambayeta sanadi?, tafad'i yanda sukayi da Zayyan.
Ransu inna ya6aci matuk'a harya kai ga inna tasamu ciwon hawan jini itama, ga Asma'u jikinta yak'i dad'i yauda lfy gobe babu.
Wannan 6acin ran yasa ya Umar cewa ad'aura masa aure da Asma'u kafin ranar d'aurin Auren Zayyan.
Kowa yayi na'am da wannan batu a family, Dan haka bayan kwanta uku da faruwar haka aka d'aura auren Asma'u da ya Umar batareda tasaniba, saidaga bayan shima ba'a fad'a mata mijinba.
____________________
Hummm randa wannan lamari yafaru ya Umar yaga tsantsar tashin hankali agidansa, Dan Lubna tamkar zata kunna musu wuta su k'one, zage-zage da tsine-tsine dangin ya Umar sunshashi, tundaga ranar zaman lfy ya k'aura agidan, bayan kwana Uku Asma'u ta tatare agidan Dan ba'ayi wani shagalin bikiba, amma dukda haka saida abokansa suka shirya musu denner, bayan kawo Asma'u aka halarci wannan denner wadda ta tata hankalin Asma'u dataga waye aka aura mata amatsayin miji na har abada, shin murna zatayi kokuwa bak'inciki?, batada za6in ko d'aya sai aikin kuka a 6oye har aka tashi denner, daganan kowa yakama gabansa, ya Umar Yad'auki Asma'u suka tafi gida, har 6angarenta yarakata, suna shiga yajuyo batareda yace da ita uffanba.
6angaren Lubna yadawo Inda yatarar da shika-shikan bala'i Dan ranar kwana sukayi babu barci harya shashshek'a mata mari biyu, taci kuka sosai tamkar ranta zai fita.
A6angaren Asma'u ma bawai barcin tasamuba, kwana tayi kuka ita kad'ai.

____________________
Tsawon kwana uku Sam babu zaman lafiya agidan Yaya Umar, Lubna ta tada hankalin kowa agidan, adaren kwana na hud'u kuma wani tashin hankalin yazoga ya Umar customs suka rik'e masa kaya babu gaira babu dalili, ya Umar yarasa inda zai saka kansa, yabi duk wata hanyar daya dace kayansa su k'u6ta abin ya gagara, haka ya hak'ura, ba'a k'ulla wataba ranar aka wayi gari kuma wai shagonsa yayi gobara komai ya k'one ba a mori komaiba, wannan tashin hankalin ne yahad'u yayma ya Umar yawa, komai yazo yak'are, har aka koro masa yara daga makaranta, yazo ya saida gidansa, ga kowa ya gujesa ciki harda matarsa Lubna, ammasa k'arfa-k'arfa akan 'ya'yansa, hargashi da tsintar kansa agadon asibiti batareda ya shiryama kansa hakanba.

_______ _______ _____
*_Mun dawo labari_*
Firgigit Asma'u tadawo daga tafiya dogon tunaninta na tsawon shekaru dasuka shud'e abaya, takai dubanta ga agogon dake d'akin karfe 2:47am, idanunta tazaro tana mai mamakin doguwar tafiya datayi atunani batareda tasan dare yayi nisa hakaba, ahankali tasauke idonta akan ya Umar dake barci, fuskarsa tayi fayau, ya k'ara haske dukda kasancewarsa bak'i sosai, yarame sosai sai dogon hanci, tashare hawayen dasuka cika mata fuska sannan tamik'e, bayin dake d'akin tashiga kasancewar ya Umar kad'ai aka kwantar aciki Dan baya buk'atar hayaniya, alwala tayo tazo ta shimfid'a sallaya tayi nafilfilinta tareda karatun alkur'ani mai girma, tayi addu'oin samun lafiya ga mijinta sosai sanan tashafa ta kwanta awajen saman sallayar barci yay awon gaba da ita...........

*_(((S)))......2017_*
*_Luv you all my sweet Fan's_*
[11/27/2017, 5:23 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*

*_page→19-20_*

_Washe gari_
Amakare Asma'u ta tashi kasancewar bata kwanta da wuriba,, ta tashi da addu'a abakinta, ganin yanda haske ya gauraye d'akin yasata zaro idanu waje, ta kalli agogo k'arfe 7:06am, zummbur tatshi Dan gabatar da sallah, agaggauce tayi sallar, tana idarwa saiga doctor Al-Ameen ya shigo, suka gaisa ya tambayeta mai jiki?.
Da sauk'i doctor, Asma'u tafad'a tana d'an murmushi.
Shima murmushin yayi ya ce, "Alhmdllh, yad'an duddubashi sannan Yakuma kallon Asma'u, Hajiya insha ALLAHU nanda awa d'aya zuwa biyu zai iya farkawa.
Alhmdllh doctor, mungode sosai.
Karki damu hajiya, mugodema ALLAH kawai, fita yayi.
Ita kuma ta tsurama ya Umar daketa barcinsa idanu cikeda shauk'in so.
_ya Umar bak'ine kuma k'yak'yk'yawa masha ALLAH, bazamu kirasa dogoba haka kuma ba gajere bane yana dai tsaka tsaki, yanada cikar hallita mai k'yawun haiba dan bai kasance siririba, yanada d'an jikinsa dai-dai misali, mutumne mai yawan hak'uri da kawaici, bakomaine abin magana awajensaba, bashida yawan hayaniya amma akwai yawan fara'a ga wanda yasani, bayason raini arayuwarsa, yanadason 'yan uwansa da mahaifiyarsa, so ya Umar dai yakai akirasa cikakke kuma nutsatstsen namiji abinson kowace mace._
Asma'u tasaki wani k'asaitaccen murmushi Wanda batasan tanayiba, gsky tana bala'in son ya Umar, harma tana ganin tafi kowa sonsa aduniya.....
Da sauri tad'ago danjin an dafa kafad'arta, Rafi'a tagani, sukaima juna dariya, Rafi'a ta ce, " haba Anty Asma'u irin wannan tafiya haka?, ya Umarfa nakine.
Murmushi Asma'u tayi, ta ce, "wai yaushe kikazone?.
Nakai Minti biyar akanki wlhy, amma ko kad'an bakisan da shigowataba, kina cikin shauk'in so.
Kai wai Rafi'a yaushe kika koyi rashin kunya ne?.
Hhhhh daga fad'ar gsky auntynmu, wai ni inama Anty Lubna ne, kobatasan bashida lfya bane?.
Wlhy Rafi'a ban saniba nima, rabonta da gidan tun washegarin randa kukaje datazo itada iyayenta.
Tofa ALLAH ya k'yauta, kardai ace itama butulcin zata masa?.
Asma'u ta ce, "Hmmm Rafi'a kenan, aii mutanen duniya sun wuce yanda kike tsammaninsu wlhy, yanzu jiya kinsan kuwa mina Tatar a asibitinnan bayan dawowata daga saida waya?, bakiga mun canja likitaba?.
Nagani, kuma tunjiya naso tambaya amma tashin hankalin halinda ya Umar yake ciki ya hanani tambaya, miya farune?.
Asma'u tashare hawayen fuskarta sannan ta ce, " lokacin Dana dawo a waje na tadda su ya Umar, makwafcinmu ya tallafesa yana kwance ak'asa, da hanzari nak'arasa garesu Dan azatonama ya Umar ya rasune, cikin kid'ima na tambayi koya mutu?."
Makwafcinmu ya CE, "a'a da ransa, wai Doctor jafarne yafito dasu waje saboda mun dad'e bamu dawoba.
Kaina kawai na jinjina Dan bak'incikinsa bashine agabanaba, lfyar ya Fharuk nake dubawa, na ce, " babu damuwa mu maidashi nasamo kud'in.
Dak'yar ya Fharuk yad'agamana hannu alamar a'a karmu maidashi, na marairaice murya INA fad'i haba ya Umar daka dai daure mun maidaka tunda lfyarka Muke nema.....
Makwafcinmu ne yakatseni da fad'in gaskiya Hajiya koni ban goyi bayan hakaba, Dan bakiga wulak'anci da cin zarafin da likitancan yamanaba, mutane sukaita kallonmu, dazaki amince akwai wani d'an uwana shima likitane anan dasai na kirashi.
Da Saudi nace kirashi kawai.
Bayan yakirashi babu dad'ewa saiga Doctor Al-ameen, cikin mamaki ya ce, "wannan ba Alhaji Umar bane?.
Mukace shine, agaggauce makwafcinmu yabashi labari, ran doctor Al-ameen ya 6aci matuk'a, babu 6ata lokaci yasa aka kawo gadon d'aukar Mara lafiya aka d'auki ya Umar, namatsa kusadashi INA MASA godiya, na ce, " ammafa bamu biya kud'in komaiba.
Harya fara tafiya yajuyo gareni ya ce, "haba Hajiya aiba kud'i yakamata mufara damuwa dasuba lfyarsa, kije ki ajiye mufara fuskantar matsalarsa, wlhy Rafi'a har kukan dad'i nayi danjin furicin likatannan.

Rafi'a ta share hawayen fuskarta itama ta ce, " ALLAH sarki ya Umar kana ganin rayuwa, bakomai ALLAH yana tareda masu hak'uri aii, ALLAH yabaka ikon jurewa.
Asma'u ta ce, "Ameen dai Rafi'a.
Rafi'a ta ce, "ga abinci nan inji mama.
Wayyo mama munsata aiki.
Baki Rafi'a ta ta6e ta ce, " kebar Maman nan itama haushi take bani, inaji inama ace ba ita ta haifemub......
Da sauri Asma'u ta rufe bakin Rafi'a, a'a karki fad'i haka Rafi'a, duk lalacewar mahaifi mahaifine, mubita da k'yak'yk'yawar addu'a kawai kinji.
Rafi'a batace komaiba saima hawaye dasuka cika mata idanu.

_Bayan 3h..._
Zuwa sannan asibitin yacika da dangi,harsu inna sunzo, amma duk doctor ya tsaidasu awaje Dan yana saran farkawar Ya Umar.
Cikin ikon ALLAH kuwa agogo na nuna k'arfe 10:00am sai ya Umar yafarka, dagashi sai Harri's a d'akin Dan Asma'u taje gida tayi wanka, cikin gaggawa Harris yafita zuwaga likita, yana sanar masa suka iso tare, bak'aramin farinciki Dr Al-ameen yayiba Dan ganin Ya Umar ya farka cikin hankalinsa, Dr al-ameen yad'an k'ara duddubashi sannan yafito yasanarma su mama.
Gaba d'ayansu suka shiga d'akin ya Umar na zaune jingine jikin gado, mama tazauna akusadashi tareda kamo hannunsa ta ce, "Umarina sannu kaji?.
Murmushi yamata, Dan bayason yin magana, suma su Rafi'a, Anty sa'a, Anty Saratu, inna, mufida, hasiya, Fatee dadai sauran 'yan uwa suka shiga yimasa sannu, kansa kawai yake iya d'aga musu, aransa ya ce, "ko ina wannan yarinyar?.'"
Bayan kamar minti talatin doctor yashigo ya ce, "suyi hak'uri sukuma bashi waje ya huta, duk fita suka kumayi akabar Harris kad'ai, doctor ya ce, " kataimaka masa yaje bayi danyayi wanka sannan yaci abinci yasha magani.
To doctor mungode sosai.
Doctor nafita Harris yataimakama Ya Umar yarakashi har cikin bayi, saida yaji yafara wankan sannan yafito waje indasu inna suke.
Chapter 10 · 0% Book details