← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 44

Sashe 2

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna Shiga Asma'u tarufesu da fad'a akan itafa batason tashin hankali, danhaka komi sukaimata karsuce zasu sake kulasu.
Shiru sukai mata kowa tana turo Baki, dansu hak'urin Asma'u haushi yake basu.

Sai magriba ya Umar yadawo gidan, suna zaune bayan sun idar da sallah yashigo.
Suduka rissinawa sukai suna gaisheshi, ya amsa babu yabo babu fallasa.
Ya ce, ''kutashi namaidaku gida.
To, suna fad'a kowa tana mik'ewa daneman mayafinta, kowa yashirya sukaima Asma'u sallama, hawaye tafara da rok'onsu Dan ALLAH su ringa zuwa mata akai-akai.
Hak'uri sukabata sukace zasuringa zuwa, dama makarantace take hanasu.
Ya Umar duk yana jinsu, ganin sunk'i tahowa yadoka musu tsawa, kai banason rainifa........
Bama su bari yak'arasaba suka fita dad'an gudunsu.
Asma'u tacusa kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka saboda kewar 'yan uwan nata, koba komai yau taji dad'in ganinsu, sunyi hira taji farinciki aranta.
Bata kuma saka ya Umar a idontaba har wayewar gari, dama bazuwa kwana d'akinta yakeyiba, itakuma bata zuwa d'akinsa Dan duk hak'urinta tanada matuk'ar zuciya, dukda tasan basonta yakeyiba hasalima taimakonta yayi, amma ai baidace yarik'a mata hakaba kodan darajar zumincin dake tsakaninsu......
Share hawayenta tayi tamik'e zuwa kichin domin had'a breakfast.

Ruwan shayi kawai tadafa da Lipton da kayan k'amshi Dan bataga wani abuba a stor d'in gidan.
A tsakkiyar falon tazo ta ajiye kofuna da filas d'in shayin Dan ya Umar bayacin abinci akan dinning.
Tana cikin d'an gyara kayan yafito daga d'akinsa sanye cikin farar jallabiya.
Rissinawa tayi ta gaisheshi, saud'aya ya amsa yafice.
Mintuna kad'an yadawo d'aukeda bak'ar Leda ahannnusa, Asma'u na zaune a babban falon tana jiran dawowarsa danta tambayesa yanda za'ayi.
Ledar yamik'a mata, hannu biyu tasa takar6a tana masa sannu.
Kujera yasamu daga d'an nesa da ita yazauna, itakuma tabud'e ledar, biredine aciki sai madara irin 'Yar sacet d'innan guda uku, sai sukari da bota ta Leda.............

*_luv you oll_*
*_(((S))).......2017_*
[11/20/2017, 6:20 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻typing..........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

_Sadaukarwa_
*_miss Xoxo na_*
*_Zarah bukar_*
*_Ayusha muh'd_*

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO....😜._*

*_page→3_*

....... Ganin yanda kayan shayin yake yasata rarrabama kowa akofi ta ajiye, gamawarta babu dad'ewa saiga su Amrah sun fito da gudu.
Jikin babasu suka fad'a suna fad'in daddy?.
Ya ce, "na'am twin's d'ina kuntashi lfy?.
Lfy lau, daddy yaushe zamu koma gidanmu?, nan gidan babu dad'i sai zafi babu AC.
Murmushi kawai yamusu, yakama hannunsu suka sakko k'asa inda Asma'u tahad'ama kowa shayi.
Dai-dai nan Lubna tafito, taci kwalliyarta cikin pink d'in shadda sai zabga k'amshi takeyi.
Afrah data kur6i shayi tayi saurin zuboshi ak'asa tareda cillama Asma'u bread d'in data bata bayan tashafeshi da bota, nidai bazan sha tea d'innanba momy babu dad'ifa, ni dankali da kwai nakeso.
Galala Asma'u tayi tana kallonta, ganin haka itama Amrah tayi cilli da nata gefe.
Ya Umar duk yana jinsu amma yay kunnen uwar shegu dasu sai danna shayinsa da bread yakeyi hankali kwance.
Lubna ta harareshi, tokaji sufa bazasu iya shan wannan tea d'inba maikamada ruwan wankin kai, koni wlhy bangoyi bayan sushaba tundasu ba dabbobi bane.
d'ago idanunsa dasukayi d'anja yayi yana kallonta, baice komaiba yamaida kamsa yacigaba dayin break d'insa.
Asma'u ma tea d'inta taja tahausha batareda tasake kallon inda Lubna da yaranta sukeba.
Aiko ganin haka yasa Lubna fara zubar da ruwan masifa da tijara, sai zabgama Ya Umar gori takeyi.
Wai aii babantane dama silar arzik'in nasa, wlhy tayi nadamar aurensa Dan aurensa bai amfaneta da komaiba sai fad'awa tarkon wahala, dan haka dolene yasaketa ita bazata zauna dashiba taringa shan ruwan wankin kai amatsayin shayi.........
Haka taita zabga ruwan masifa babu Wanda ya kulata barema ya tanka mata, Asma'u tana gamawa ta tattara komai takoma d'akinta.
Shima mik'ewa yayi yashige nasa d'akin.
Itama ganin babu sarki sai ALLAH taja hannun Afrah da Amrah suka bar gidan.

Bayan wasu 'yan mintina Umar Fharuk yafito tsaf sanye cikin k'ananun kaya sai zabga k'amshi yakeyi.

Araina nace bawan ALLAHnnan ya iya d'aukar wanka wlhy.

d'akin Lubna yashiga, amma saiyaga wayam, baice komaiba yafito yashiga na Asma'u.
Tana falo kwance a doguwar kujera, chart takeyi abinta sai faman murmushi take zubawa.
Sallama yay mata sannan yazauna kujerar dake fuskantarta.
Itama tashi tayi zaune ta ce, "sannu.
Bai amsaba amma idonsa na kanta, Ita saima duk kunya takamata, ganin haka yasashi d'auke kai daga gareta, ya ce, " zanje shagunana Dan inaso afara gyaransa muga kuma abinda ALLAH zaiyi, idan kud'in sunkai angama gyaran to ko haya saina bada, idan kuma basu kaiba saimuga kuma abinda yadace ayi.
Jin yayi shiru tagane cewa yagama maganarsa, cikin sanyinta ta ce, "ALLAH ya tabbatar da alkairi aciki, Yakuma mayar da alkairi fiye da abinda aka rasa.
Yaji dad'in addu'arta danhaka ya amsa da ameen yana mik'ewa.
Saina dawo, yay maganar yana fita.
Itama tace ALLAH yatsare takoma ta kwanta.

%%%%%%%%%%%%
Umar nafita daga nan gidansu yanufa, gidan babu laifi mai k'yaune Dan tuni Umar yagyarashi tsaf, komai na more rayuwa saida yazubama iyayensa shi, horn yayi maigadi yabud'e masa gate, saida suka gaisa sannan ya ida shiga ciki, yasamu guri yay fakin.
Da sallama yashigo falon, Rafi'a ce kawai ta amsa cikeda farinciki, amma mama da Mufida da Harris sun amsane babu yabo babu fallasa.
Waje yasamu yazauna ak'asa yana gaida mama.
Dak'yar ta amsa masa, bai damuba yajuya yana amsa gaisuwar Rafi'a, harara ya gallama Harris da mufida Ku baku iya gaisuwa bane?, wai yaushe kuka rainanine?.......
Kafin suyi magana mama ta cafe, a'a yabazasu rainakaba? Tunda kagaza yimusu maganin abinda yadamesu.
Ajiyar zuciya yasauke, idanunsa harsun canja kala, ya ce, ''kiyi hak'uri mama abubuwane sai ahankali, kinsan dai halin Dana tsinci kaina aciki, inda Dane kobasu tambayaba zan basu, amma wlhy yanzu banida sh......
Kai dakatamin!!!, mama takatsesa cikeda tsawa, harni zaka bud'e baki kacema bakadashi, koma kunyar yin k'arya bakaji?, shekaranjiyafa kasiyar da gidanka miliyoyin kud'i amma har bakinka yafurta bakadashi, duk dai Wanda yagaza godema ALLAH to zai godema azabarsa.
Wani yawun 6acinrai ya had'iye, muryarsa cikeda girmamawa agareta ya ce, "kiyi hak'uri mama, wlhy kud'in gidannan acikinsu aka cire aka sayi gidan damuka koma, sauranne kuma zanje nayi gyaran shaguna nana, bammayi zaton kud'in zasu kaini ko inaba.
Hummm tonaji baban tsari tashi kabani guri, kama gyara duniya dasu ba shagunaba, itadai rayuwa duk Wanda yakedashi yagaza taimakon d'an uwansa aiyayi asara....
Da sauri Umar yad'ago yana kallon mahaifiyar tasu, idonsa yayi jajur, Rafi'a ma kuka takeyi, tana mamakin hali irinnan mahaifiyar tasu, kwatakwata mutumce dabata godiyar ALLAH, atunaninta ya Umar yafi k'arfin cin fuskarta kodan k'ok'arinsa nason k'yautata mata, duk cikinsu babu mai hak'urinsa dakuma kula da iyayensu, amma tunda iftila'in nan yasamesa 'yan gidan suka fara canja masa........
Maganar ya Umar ce takatse mata tunaninta, rissainawa yayi ya ce, " sai anjima, ALLAH ya huci zuciyarki, yakalli su Harris ya ce, "zantura muku insha ALLAH.
baki suka washe suduka harda mama, ko kaifa d'an nan to ALLAH yayi albarka kaji, ameen yafad'a ala6ansa.
Suma su mufida sai zabga godiya sukeyi, shidai ficewarsa yayi.
Koda yashiga mota saiya fice daga gidna, tafiya yakeyi amma zuciyarsa namasa zafi, gefen titi yasamu yay fakin, yakifa kansa jikin sitiyari yana duk addu'ar datazo bakinsa, wlhy yana mamakin hali irinna mahaifiyarsu, alokacin da yakedashi tafi kowa sonsa da tattalinsa, kullum addu'a take masa dafatan alkairi dagamawa da duniya lfy, amma abin mamaki tunda komai yak'are masa saita fara canjawa, yanzu babu Wanda tatsana samadashi, batada magana saita ya Abubakar da Anty Sa'a da Harris da mufida, suma Kansu 'yan uwansa sun canja masa gaba d'aya, anty sa'a ce kawai da Rafi'a suke sonsa, yasa handky yana share hawayen dake kwarara a kumatunsa.
Yakai tsawon lokaci awajen sannan yabirka motar yanufi kasuwa.
Alhmdllh aiki yayi nisa Dan anata kwashe tokar gobarar data k'ona shagunan, ganin komai natafiya dai-dai saiya shiga mota yanufi majalissar abokansu.

%%%%%%%%%%%%
Zazzaune suke sunata kwasar hira da dariya, motar Umar tatsaya.
Motsowwww ga k'aban nan cewar Hafiz.
Waye k'aba?, Salman yatambaya idonsa akan hafiz?.
Umar mana, kokai bakada ganewane, cewar Tasi'u.
Al'kasim yata6e baki kaini wlhy fa banason yana ra6armu karya goga mana talauci.
Ashe kagane d'an uwa, yanzufa d'angidan dayake mana tak'ama dashifa ya saidashi.
Kai Dan ALLAH kabeer dagaske kakeyi?.
Wlhy kuwa Hafiz da gsk, nima jafar take bani labari jiya, kunsan shi kunya bazata bari yafad'a manaba.
Tofa, yanzu to ina Yakoma?.
Wani kangon gida yasiya... Dariya suka shek'e da ita, Al'kasim ya ce, "su k'aba anji yaji........
Umar dake tsaye duk yana jinsu yagirgiza kansa tareda musu sallama............
Afurgice suke kallonsa, duksun tsargu kardai yaji firar tasu?, dansu basusan yama iso inda sukeba.
Kowa yakama 'yan kame-kame.
Hannu yamik'a musu suka gaggaisa fuskarsa d'aukeda murmushi, suna gama gaisawa ko zama baiyiba ya ce, " bara nawuce, Dama nabiyo gaishekune.......

*_(((S)))....2017_*
*_luv you all my fan's_*😻
[11/20/2017, 6:20 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻typing..........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

_Sadaukarwa_
*_miss Xoxo na_*
*_Zarah bukar_*
*_Ayusha muh'd_*

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO....😜._*

*_page→4_*

..........ah mungode angon Asma'u da uwargida Lubna.
Baice komaiba sai murmushin takaici dayayi yajuya yashiga motarsa, suduka binsa sukayi da kallo, kai jama'a Kodai yaji mimuke fad'a?.
Kai baiwani jimuba, idanma yaji saime kune kukejin tsoronsa.
Mtsowwww miye abin tsoro a can?, mutumin da duk talauci ya gwaguyeshi, ni gwarama dabai zaunaba......
Chapter 2 · 0% Book details