← Book details Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 44

Sashe 16

Karayar Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........Tunda tayi sallar asuba takoma ta k'udundune a bargo.
Shikam ya Umar tundaga masallaci baima dawo gidanba yana shago, agogo ya kalla dake cikin shagon har 9:37am amma Asma'u bata lek'oba, sallamar wani saurayi tak'atse masa tunani, ya amsa yana mik'a masa hannu suka gaisa, saurayin yace abashi Sabulun wanki, d'akkowa Ya Umar yayi yabashi, saikuma ga wasu yara, doledai ya hak'ura yacigaba dabama mutane abinda sukeso, haka shagon yake wuni cikin shige da fici namasu siyayya.
Har 11 tayi baisamu damar shiga gidanba, gashi Asma'u ma bata lek'oba, yanaji azuciyarsa badai lafiyaba.
Can zuwa 11:30 mutane sukad'an lafa saiya rufe shagon yashiga gida.
Har yanzu Asma'u nak'udundune abargo, sai rawar sanyi take faman yi da sambatun zazza6i, dama ita haka take indai tana zazza6i tatayin sambatu kenan.
Da sallama ya Umar yashigo, ganin Asma'u a kwance cikin bargo sai gabansa yafad'i, k'arasawa yayi cikin d'akin sosai yana fad'in lafiya kuwa?.
Asma'u dabatasan yanayiba sai rawar sanyi takeyi tana sambatu dakiran baba, inna, Fatee, Rafi'a, hasiya, kuzo kutaimakeni, wayyo ya Fharuk zan mutu kazo plzz.....
Ganin yanda take abirkice yak'arasa da sauri yazauna bakin katifar, husna lafiya kuwa? Yay maganar yana yaye k'aton bargon data lilli6a ajikinta, wani hucin zafin zazza6i yabigeshi, da sauri tarik'o hannunsa tana fad'in wayyo Yaya rufeni sanyi nakeji sheeeeee!!!!.
Lilli6eta yayi tareda fad'in sannu, amma miyasa baki fad'aminba tun d'azun? Haba mutum yata zama da ciwone?.
Mik'ewa yayi zai fita tarik'o hannunsa tana kuka, wayyo ya Fharuk kaina kamar zai fashe, k'irjinama haka, kataimakeni wayyo.
Tausayi tabashi sosai, dawowa yayi yazauna akusada ita, tad'ago da dak'yar tad'ora kanta saman cinyarsa, kokad'an bataso yatashi data Kusada ita, (dama itakam wanan salon zazza6inta kenan, saitaji wani akusada ita). Ya Umar yad'an rintse ido danjin yanda zafin zazza6inta ya ratsamasa jiki, tausayinta yakuma kamashi, kanta yashafa ahankali, husna kikwanta zanje nama muktar maganane kozai samo mana doctor d'in dazai dubaki.
Uhm uhm Yaya banason allura wlhy, kabarni kawai.
Yaya zan barki husna! Kinta6a ganin anbar mutum cikin ciwone? Kiniji yanda jikinki yayzafi kuwa?........
Kafin tace wani abu sai sukaji sallaman Rafi'a.
Ya Umar ne ya amsa, tatsaya ak'ofar d'aki danjin muryarsa, jin shiru nawani lokaci ya ce, "shigo mana."
K'arasowa tayi cikin d'akin, ta gaida ya Umar sanan ta tambayi miya sami Asma'u?.
Batada lfyne, yauwa shiga nan makwaftanmu kima muktar magana kozai samo mana doctor dazaizo gida?.
To Yaya, ammafa masu sayen Abu suna jiranka a k'ofar shago.
O!. kinga kar6a key d'in, idan kinmasa magana saiki bud'e ki zauna, kafin nagama.
OK, tana kar6ar key d'in tafice da sauri.

Mintina k'alilan saiga Muktar yazo, dak'yar ya Umar yasamu Asma'u tabarsa yatashi, fitowa yayi wajen Mukhtar, hannu yabasa suka gaisa sanan yamasa bayanin ga doctor Al-ameen nan zuwa.
OK Abokina ngd sosaifa, ALLAH yabar zuminci.
Abokina aii babu godiya tsakaninmu, munrigada munzama d'aya, ciwon madam kodai munsami baby ne?.
Dariya ya Umar yayi yana fad'in abokina baby kuma? A INA?. Hhhh babu wani baby abokina, zazza6ine kawai wlhy.
To shikenan ALLAH ya k'ara sauk'i, cikinma muna addu'ar zuwansa nan kusa.
Murmushi kawai ya Umar yayi batareda yace komaiba.

Babu dad'ewa saiga doctor Al-ameen ya iso, suna gaisawa ya Umar yamasa iso zuwa cikin d'akin Asma'u. Har yanzun kuka takeyi da surutanta, ya Umar yazauna Kusada ita, yayida doctor Al'ameen ke a zaune bisa wani tum-tum da lubna bata d'aukaba, Mukhtar kam na tsaye daga k'ofa.
Tambayoyi yamata tana basa amsa, amma fad'i take pls doctor kada kamin allurafa.
d'an dariya doctor Al-ameen yayi, ya ce, "madam kina tsoron allurane?."
Kanta ta jinjina alamar a'a, cikin muryar Mara lafiya ta ce, "doctor banasone kawai."
Gashi kuma dolene amiki ita, Dan teiport nadamunki sosai. K'an k'ame hannun ya Umar tayi sosai tana fad'in pls Yaya kace karyamin banaso. Harararta yayi danshi surutun yafara bashi haushi, yanada kishi sosai.
Magun guna yabata sanan ya ce, "zai mata alluran dabata so d'in. Hawaye tafara zubarwa Rana k'ara k'ank'ame ya Umar tamkar zata koma cikin jikinshi. Kamo hannunta yayi yamik'ama doctor Al-ameen Wanda yake rik'e da igiya dansan d'aura mata yanemo jijiya. Igiyar ya d'aura mata, cikin sa'a aka samo jijiyar. Hawaye takeyi sosai Rana k'ara k'ank'ame ya Umar.
Tana ganin yanufota da allurar yak'ara sautin kukanta, taso tabama Umar dariya amma saiya gimtse, doctor da Muktar kam saida suka murmusa. Wata uwar harara da ya Umar ya galla matace tasakata nutsuwa waje d'aya, amma hawayen basu daina zubaba. Tanaji tana gani akamata allurarnan, har aka gama tana k'ank'ame da ya Umar.
Doctor ya kalli ya Umar ya ce, " Alhaji insha ALLAH zazza6in zai sauk'a, taci abinci tasha maganidai, ammafa idan har zuwa yamma akwai Matsala saika kirani.
Okey doctor ngd sosai ya Umar yafad'a yana bashi hannu, saida suka rakashi har motarsa sanan ya Umar yadawo Muktar kuma yashiga gidansa.

Babu dad'ewa saiga matan Muktar Sadiqqa tashigo gidan, lokacin ya Umar na k'ok'arin had'ama Asma'u shayi.
Gaisuwa sukayi da ya Umar, ta tambayeshi mai jiki, sanan ta ajiye kular abinci data kawo. A'a Maman Faisal abokina yatadoki ko?.
Lah babu komai wlhy, aii kawai kama koma shagon saina lura da ita, abincima nanan na ajiye a shop d'in. A'a aii hidimar tayi yawa Maman Faisal. Wlhy babu wani yawa Indai ba rainawa kayiba.
Mik'ewa ya Umar yayi yana dariya, ni na' Isa?, aii sadai nace ALLAH yasaka da alkairi yabar zuminci kawai.
To Ameen.
Yana fita saddiqa tashiga hidimar bama Asma'u abinci, saiga Rafi'a da ya Umar ya kar6eta ya ce, "tashigo gida.
Atare suka gyara gidan tsaf, bayan Asma'u taci abinci Saddiqa tasakata tayi wanka tasha magani, sanda tafito angyara d'akin tsaf, saikawai tasaka wasu kayan takuma kwanciya sai barci.

Saida suka gama komai sannan Maman Faisal tawuce gida, Rafi'a kam saida tamusu abincin dare takuma gyara gidan tsaf sannan tawuce gida Dan tanaso taje islamiyya.
Ya Umar yanata zagayata danyaga yajikin, amma har yamma bata farkaba.
Sai bayan isha'i daya shigo yataradda ta tashi.
Kintashi?.
Kanta tad'aga masa, har yanzun tana cikin bargo. To yajikinnaki?, da sauk'i amma har yanzu inajin sanyi wlhy.
Zai daina shima, tashi kiyi sallah ko?.
Nanma kanta ta jinjina sannan ta yatsina fuska, yaya dama akwai ruwan zafi sainayi dashi, bazan iya da ruwan sanyiba. OK bara naduba ko Rafi'a tazuba a filas.
Rafi'a tawucene?.
Eh tun d'azun tawuce, tanason zuwa islamiyya tace.
Batace komaiba, shima yafita yakawo mata ruwan zafin, dakansa ya taimaka mata zuwa bayi, tsayawa yayi kanta yak'i fita.
Tajuyo tana kallonsa kamar zatayi kuka, kafita to.
Gira yad'age sama tareda d'an langa6e kansa gefe, bazaki iyayi agabana baneba?.
Gyad'a kanta tayi cikeda shagwa6a.
Murmushi yayi, ya jingina da bango harda hard'e hannu ak'irjinsa yana kallonta. Ta marairaice murya tana k'ank'ame jikinta, yaya sanyi nakeji wlhy, kuma zanyi fitsarin atsaye...
d'an zaro idonsa yayi waje, ya CE, "da gsk?."
ALLAH kuwa.
Murmushi yayi mata sannan yafice batareda yace komaiba.

Tana idar da sallan takuma zuwa zata kwanta, rik'o hannunta yayi yana fad'in no zauna ki huta.
Wayyo ya sanyi fa.
Toni wannan sanyi namiyene? Dayak'i tafiya. Bara nakira doctor namasa bayani......
Kafin Asma'u ta ce, wani Abu saiga Faisal (babban yaron Muktar), rissinawa yayi ya gaidasu, yayma Asma'u sannu, sanan ya ce, "uncle Abba ya ce, "kakawo key d'in shop yazauna, kaikuma kazauna wajen aunty.
To yarona ALLAH yayimaku albarka kaji, gashi kacemasa ngd.
Rissinawa yayi yakar6a yafita.
Shikuma yashiga kiran doctor. Bayan sun gaisa yaymasa bayanin harfa yanzu Asma'u tanajin sanyi.
'Yar dariya doctor yayi, ya ce, "wanan aikinkane Alhaji, indai babu zazza6in to Alhmdllh, maganar sanyi kam tana buk'atar d'umin jikinkane kawai.
Da sauri Asma'u da ya Umar suka kalli juna Dan yasaka wayarne a Hans Free.
taja bargo ta kwanta, shikuma yad'auke idonsa daga kanta yamaida hankalinsa akan maganar doctor.
Okey doctor babu damuwa ngd sosai, saida safe.
ALLAH yakaimu Alhaji, agaidamin da madam.
Okey zataji, agaida iyali.
Koda ya Umar ya kammala wayan baikalli Asma'u ba yatashi yafice, itako tak'ara k'udundune kanta a bargo, tamkar wadda ake shirin sacewa.

Waje yaje wajen Muktar, saida sukad'anyi magana ta mintuna sannan yadawo gidan.
Kaitsaye d'akinsa yanufa, yay wanka tareda shirin barci tsaf sannan yakoma d'akin Asma'u.
Harma tafara barci ita.
Yad'an dad'e akanta yana k'are mata kallo cikeda tunani kala-kala tamkar bayason abinda yay niyyar yi agareta na bata taimakon da doctor yabashi shawarar.
Tsawon mintuna sannan yazauna abakin katifar tareda d'aga bargon yashiga ahankali.
Jawota yayi ya manna da jikinsa, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tareda rinmtse idanunsa. Itakam sai kawai tagyara kwanciyarta danjinta cikin wani lallausan jiki, gawani d'umin mai dad'i da k'amshi. Barcin yaci k'arfinta shiyyasa ko farkawama batayiba.
Amma ga mutumin naku ba haka baneba, jinsa yakeyi tamkar bashiba, tuni yasan shi mutumne mai yawan buk'ata shiyyasa yake tausayin fara kusantar Asma'u, amma yazaiyi? Zuciyarsa takasa daurewa, akwana biyunnan hak'uri kawai yakeyi. Yanason kasancewa da matarsa amma yana gudun karkuma ta rainashi. Yakuma k'ank'ame ta sosai tamkar za'a kwaceta daga gareshi, jin anrik'eta tamau yasakata motsawa, shima saiya sassauta mata.
Addu'a yamusu ta barci, tanata barcinta amma shi yagagara yin nasa saboda kwad'ayin kasancewa da ita................

*_"ngd duknaga sak'on gaisuwarku, harma damasu kirana, harma wad'anda basu sami damaba, dukna gode ALLAH yabar zuminci, nama warke, ammafa ina jiran kazar😋😋🤷🏽‍♀😄"_*.
Luv you all💋💯

*_Luv you all_*
*_(((S))).......2017_*
[12/9/2017, 8:40 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........

💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎

*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*

*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_

*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*

*_page→33-34_*
Chapter 16 · 0% Book details