Sashe 72
Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taɓe baki yayi yace "to shikkenan duka za'a haɗa ayi, Allah ya baki lada ya albaekaci niyyan ki, amman ko ɗaya ki cire ki ajiye ya zamo miki kaman kadara saboda tasowan emergency tunsa bamu san ne gobe ta ƙunsa ba"
Saboda baiyi mata musu a nata ra'ayin ba yasa shima babu jayayya tace toh. Da hannunsa ya É—auka mata wani wanda ya É—an fi tsada don da hannunshi ya siya mata shi a Dubai tun lokacin tana amarya.
******
9:05am
Tsaye nake a gaban cooker ina tafasa tea mai kayan ƙamshi, ta baya naji an rungumo ni tare da placing light kiss a kafaɗana dake a buɗe,
Ko ba'a faÉ—a ba nasan mutum É—aya ne zai iya min haka a duk duniya.
Murmushi na ɗaura a saman fuskana na juyo tare da sauƙe kaina ƙasa don wani mugun kunya da nauyin Zayyad nake ji a yanzu,
"Ina kwana babylove"
"Lfy lau, yaya gajiya"
"Gajiya yabi lafiya" na faɗa can ƙasan maƙoshi tare da juyawa naci gaba da antaya abinda nake zubawa cikin tukunya.
"Ai na tabbatar da ke É—in mai lafiya ce so nasan dole kin gaji amm....."
Da sauri na rintse idanuna jin na takalo ma kaina jangwangwam, "Babylove dan Allah kayi shiru.. Please" na faÉ—a still idanuna a rufe.
Dariya yayi da ganin haka yace "Allah ya tsaga ma ɗan adam baki don yayi magana ne amman ni sai ace nayi shiru? Anyways me kike dafawa ne bayan kinsan anytime odern mu zai uya ƙarasowa? Bani son kina wahalar min da kanki a nan idan kina son gajiya ne just take care of me.. i will make you tired".
Girgiza kai nayi ni bansan lokacin da Zayyad ya zamo haka ba, magana ba magana ba sai ya hau fassara kan al'amari.
"Na sani, nayi kewar shayin gida ne nake son in haÉ—a irin shi na samu na É—an watstsake jini"
"Ohh sorry na tara miki gajiya kou?"
Ban kula shi muka ja maganar da nisa ba don nasan abinda yake so kenan, ya ƙaraso jikin gas ɗin yana leƙa abinda ke cikin tukunyar a ɗan tsorace,
"Woooh! What's with these bubbles? Baki jin tsoron zai ƙona ki "
"Tafasan ruwan ne zanji tsoro baby kaman ba mace ba? Idan da kuma tuka tuwo ne ba zaka iya gani ba, da zafin shi haka za'a dinga jujjuya shi"
Jinjina kai yayi looking impressed " kinsan ni ban taɓa shiga kitchen ba, koda wani abu ne na uzuri ya kaini saidai na tsaya a bakin ƙofa...aunty bata taɓa barina na shiga tana tsoron kada idan naje kusa da wuta ciwona ya tashi wani abu ya same ni a dalilin haka"
"Allah ya saka ma aunty da aljannah da ta kula da kai bata barka ka cutu ba, she is truly a good mother and a role model"
na juya zan bar mishi wurin don zuwa na maida sugar a wurin zaman shi ya dauke ni cak ta baya hannayen shi a kan cikina yana juya ni a hankali a tsakar kitchen ɗin tun ina ƙanƙame jikina har na sake na ɗaura kaina a gefen wuyan shi tare da lumshe idanunna ina shaƙar turaren shi mai daɗin ƙamshi zuciyata tana daɗa tsananta bugu,
"Kin cike min gurbin zuciyata Saudat... Thank you" murmushi nayi da jin haka, ina jin daɗi a ko wani lokaci idan Zayyad ya buɗe cikinsa yana faɗa min kalamai nasu daɗi, suna matuƙar sakani nishaɗi "ina ƙaunar ki babes, yanzu kece komai nawa"
Hannuna na saka a gefen fuskar shi ina shafawa, cikin raÉ—a nace "na gode da ka bani dama, thanks for choosing me babylove... I love You"
"Yauma mu koma bakin ruwan nan ko? I want to swim"
Da sauri na buɗe idanuna jin ƙaran tafasan tea dina a kan gas wanda har ruwan ciki ya kusa ƙarewa, nayi saurin sauƙa daga jikin shi ina girgiza kai naje na kashe cookern na sauƙe tukunyan a kai.
"A'a har yanzu fah bawai na daina jin tsoron ruwan bane, phobia sai a hankali yake tafiya a ɗan ɗaga min ƙafa zuwa wani lokaci idan tsoron ya ragu sai mu koma"
Tunda na juyo na fara mishi magana ya ƙura ma lips ɗina dake ƙyallin lipgloss idanu
"Tsoron ruwan kike yi har yanzu da gaske ko kuma tsoron wanda zai shigar dake ruwan?" Ya faɗa tare da ɗage giran shi ɗaya, yana daɗa takowa zuwa inda nake tsaye "idan ma da gaske ruwan ne you know nasan yanda zan kula dake...ba zakiji tsoro ba i promise" ya ƙarasa tare da manna lips dinshi saman nawa.......
.....banyi KUSKUREN zaɓen Zayyad a matsayin namijin da nakeso na karashe rayuwata dashi ba, ko zan iya cewa banyi KUSKUREN roƙon Allah ya bani Zayyad ba, dukda ina kaunar shi a zuciyata amman na zaɓi na roƙi Allah yanin zabin alkhairi, ya bani miji na gari wanda zai kula dani ya bani farincikin da ban samuba a gidan aurena na farko, shiyasa banyi mamaki ba da canzawar al'amarin ƙaddara ta lokaci ɗaya saboda nasan Allah mai iko ne a kan dukkan komai, kuma mai canza abinda yaso a lokacin da yaso, sannan a duk lokacin da yaso zartar da al'amari zaice kasance ne...sai ya kasance.
Zayyad mutum ne mai kulawa, kyautatawa, adalci, haƙuri, da kuma tarin soyayya a tare dashi, sannan nima ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin nayi masa biyayya, na kyautata mishi.... honestly lokacin da nake ƙuntace a wuroɓokki a wannan ɗaki mai duhu da zafi a ƙasƙance a wulaƙance ga tarin azaba daga wurin wanda yake a matsayin shugaba wanda ya kamata ya zamo adali a gareni.....ban taɓa tsammanin akwai ranar da zan kuɓuta ba, ban taɓa tunanin akwai ranar da zan fito na canza matsuguni harda matsayi ba, amman duk wanda ke cikin wani matsala ya yarda ya fawwala ma Allah komai tabbas wata rana abubuwa zasu sauya domin babu yanayi mai tabbatuwa a duniyar nan walau na daɗi walau akasin shi ko shi duniyar ma gaba ɗayanta ba matabbata bace.
Sai gashi nima Allah yayi min sauyi da mutumin da ko yaushe yake ƙoƙarin tabbatar da ina cikin farinciki koda a lokacin da bayi cikin ƙoshin lafiya bayi barina cikin ƙunci, he always make sure that I'm smiling.
Watannin mu shida muna faman jinya a Maldives, nasan ba zakuyi mamaki ba idan nace yanzu haka ina ɗauke da cikin wata 5 dukda shi patient ne amman bayi wasa, har ga Allah banso ɗaukan ciki da wuri haka ba amman kuma da labarin abin ya riske shi naga irin farincikin da ya shiga sai naji hankali na ya kwanta nima na shiga cikin farinciki ko babu komai yanzu Allah ya kawo min lokacin da zanga gudan jini na, shima ba da ƙasƙantaccen bawa irin yarima ba, da sarkin dake mulkin zuciyata a Yanzu bawan Allah na gari mai kiyaye dokokin shi.
A watan mu na takwas muka ɗauki hanyar 9ja lokacin cikina nada wata 7 ya fito ɗan ɗul abinshi gashi nayi ƙiba na ɗanyi duhu saboda sanyi amman jikina fresh alamun na samu hutu na ciko na ƙara kyau masha Allah.
Kunyan haÉ—a ido da aunty Amarya da innata nake ji kaman yanzu na fara aure, naso ma da zaman mu mukayi na aihu abina a can saidai kawai su ganni da yaro ko yarinya amman da na faÉ—a ma Zayyad ra'ayina ban samu amsan komai ba sai kallon da ya jefa min irinna 'yarinya har yanzu yarinta na damunki' ai kuwa cikin satin ya tattaro ni muka dawo.
Tun daga airport kada kuso kuga tarba, murna biyu ya tara wannan dandazon mutanen, da murnan dawowan Zayyad gida cikin ƙoshin lafiya da ɗokin ganin cikin jiki na da tun satin shi guda a duniya labarin shi ya gama bazuwa a cikin dangi.
Tunda mutanen nan suka ga tsulun cikina suka rasa yanda zasu saka ni su saka kansu saboda murna sai kaffa_kaffa suke dani wasu cikin su ji suke kaman idan tafiya ma ba zan iya ba na basu suyi min,
gidan aunty Yusrah aka wuce dani saboda Innata a can ta sauƙa kuma ba daɗewa zatayi ba zata koma, shiyasa aka roƙa min Zayyad da ƙyar shi da aunty amarya suka yarda naje na ƙarasa wuni mata sai da dare ya ɗauko ni mu dawo.
Yanzu haka zaune nake a gaban plate É—in abinci dukda yunwan cikina na kasa cin abinci Inna ta saka ni a gaba sai risgan kuka takeyi kaman Allah ne ya aiko ta.
Numfashi na furzar ga tarin gajiyan da na dibo a zaman jirgi kafafuna sunyi tsami amman bata barni naci abincin va ma ballantana na kwanta na huta,
"Inna dan Allah kiyi haƙuri ki daina kukan nan, ya isa haka please"
Zaran tissue ɗaya tayi daga cikin kwalin shi da na ajiye mata a gabanta ta share hawayen idonta sannan ta ɗago tana kallona wani kukan na shirin kwaçe mata,
"Kukan daÉ—i ne boÉ—É—i dan Allah ka barni nayi, har yanzu banshan wani irin godiya zanyi wa Allah ba da tarin niiman da yayi mana ki kalle ki fah!"
"To shikkenan tunda kuka kikeyi na koshi da abincin bari na tashi na tafi ko zaki bar zubar min da hawaye kada azabar Allah ya sauƙa a kaina" na fara ƙoƙarin tashi
Saurin share hawayen tayi wannan karon da bakin hijabinta ta riƙo ni na dawo na zauna sannan ta saka ni na fara cin abincin har na gama bata sake koda tari ba.
Ƙarfe 8 sharp aunty Amarya ta taso keyar Zayyad yazo ya ɗaukeni, itama yta kasa ta tsare kan ba zamu koma gidanmu ba har sai na aihu, muna zuwa naga ta tarkaso min kalolin abinci bayan naje na gama ciko cikina a gurin aunty Yusrah don har awara da dankali suyan gefen titi saida nasa aka siyo mana mai shegen yawa muka ci duk ba tare da sanin Zayyad ba don nasan ba bari zaiyi ba idan ya sani.
Duk yanda naso fahimtar da ita a ƙoshe nake ta kasa ganewa ta tasa ni a gaba ina tura abincin nan, da na samu ta kauce na janyo ɗanta yazo na ɗura mishi saida ya kusan cinyewa tass na kore shi kafin ta dawo.