← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 73

Sashe 32

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amman yaa Zayd kana yin duk addu,o,in da na baka?" Na tambaya babu wasa cikin murya na,

Gyaɗa kai yayi ya ƙura min na mujiya yana ƙoƙarin ɓoye abinda yake ji ta hanyar shimfiɗa min simple smile a saman fuskar shi,

"Na safiya da maraice fa, kana yin su duka?"

GyaÉ—a min kai yayi tare da faÉ—in "yeah, kewar rashin ki a cikin gidan nan ne kawai bani kiyaye wa wajan hana zuciyata yi, da kuma tsumayen jiran amsa na.."

"Ya zayd bari na je wurin Fa'iza na karɓo abu ina dawowa" Ruma ta faɗa tare da rufe littafin dake hannun ta wanda ta ɗauko cikin jerin littattafan dake ɗakin da aka ajiye su na musamman don ɗebe ma Zayyad kewa, ta maida shi wurin zaman shi ta fice,

Saida naga ta rufo ƙofar sannan na juyo ina kallon shi daman already ni yake kallo,

"Nayi tsammanin zan iya jira na tsawon lokaci kafin na nemi jin ra'ayin ki a kaina amman na kasa haƙuri, ki faɗamin dan Allah ko na samu wuri a zuciyar ki"

Sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina wasa da zoben hannun na, ina ƙoƙarin danne murmushin dake ƙoƙarin suɓuce min, I can't help but to blush, duk lokacin da na tuna nima wata ce a zuciyar Zayyad a halin yanzu, nakan ji sanyi da daɗi ya mamaye zuciya ta kaman na tashi nayi ta tuma tsalle ina murna, bansan me yasa nake son shi da yawa ba,

"Babe dan Allah kice wani abu this silence is killing me"

"Mmm n..ni..ni b.bani da w..wani amsa..a..yanzu"
Na faÉ—a murya na yana rawa wanda bansan dalili ba, kunyar sa sosai ya kama ni,

"Dan Allah ki nemo, ni ko ƙarya ne kiyi kice kina sona, please!"

"Uhmm Sitifid kenan ai Allah yana kallo na, ƙarya bayi da kyau"

"Me kika ce?"
Ya tambaya yana bina da wani irin kallo don ni karan kaina ban san da sunan da na kira shi ba, siɗin_siɗin na miƙe na bar ɗakin ina ƙunshe dariya na,

Ina fita parlor na ja birki na tsaya don tunda na fito ban lura dasu ba ina ta faman baza murmushin haÉ—uwa da masoyi, idanu na suka shige cikin na babban yaya da ya saka Ruma a gaba ta tsaya kaman sabuwar soja,

duk tambayoyin da yake jero mata bata samu amsa ko É—aya ba, tsoron fitowa na ni kaÉ—ai daga É—akin Zayyad take yi dukda kuwa Sulaiman ya san amfani na gareshi amman kaÉ—an daga aikin shi yanzu ya birkice mana,

A wannan lokacin ban ɗauke idanu na daga cikin nashi ba saidai murmushin dake fuska na ɓatt ya ɓace, na tsaya rama kallo na tunda ai yanzu ni budurwan ƙanin shi ne haka kawai ba zai dinga kallo na kuma ya kalli banza ba,

"Zaki iya tafiya" ya faÉ—a idanun shi still a kaina, ko a jiki na na juya zan tafi da sauri yace "ba keba, ita nake nufi" ya nuna Ruma da yatsa,

Da jin haka ta juya ta fita tana hamdala tunda bai ɗau zafi ba, tana fita yace min "ƙaraso magana zamuyi"

Zuciyana yana lugude up and down na ƙarasa tsakiyar carpet dan zauna da sauri ya dakatar dani tare da nuna min kujeran dake gefen nashi, "zo ki zauna a nan"

_ya Allah kasa ba laifi nayi ba, ka tsare ni daga fushin zazzaɓi_

Cikin takun nutsuwa na ƙarasa wurin da ya nuna min na zauna na sada kaina ƙasa, with every movement i took his heart away yayi kewana fiye da tunanin mai tunani na rashin gani na da yayi kwana biyu,

Ba don karatu na yana da muhimmanci ba da ba zai jira nayi ba zaiyi zancen auren mu, amman ba zaiyi gangancin hakan ba don dariyan Sadiya kaɗai ya ishe shi jin kunya, ya auro gidahuma don yanzu kam ya daina kiran ta daƙiƙiya,

"Wani shiri kika fara yi na makaranta" naji tambayar shi ta faÉ—o a sama,
_ni kuma wani shiri zanyi?_ na tambayi kaina,

"That's what I hate, ina magana ma mutum yayi min banza, talk dan allah"

ÆŠagowa nayi da tsananin mamaki, jin yau maganar shi soft and calm, babu tsauri babu tashin hankali a cikin muryan shi, anya wannan babban yaya ne?

"Kinsan boarding school ne dole kiyi masa shiri dukda dai zaki dinga dawowa gida duk weekend, and idan nace gida ina nufin nan gidan kenan saboda ina lura da al'amuran karatun naki don kinyi baya da yawa Saudat"

Kutt, daman har ya san sunana ko yau ya fara jinsu?

"Ba shiru zaki yi min ba fahh I don't have all day, ki faÉ—a min abinda kike so na makaranta Shikkenan ba cewa nayi ki mutu ba balle ki tsaya kokwanto" ya faÉ—a wannan karon a É—an kausashe,

"Uhm b..babu ni bani buƙatar komai"

"Haka zaki tafi single kenan, baki da kayan sawa babu abinci babu komaii?"

_nifa banma san abinda zance mishi ba, yanzu tsirara ya ganni da zai min maganar kayan sawa ko yaga alaman ciwon yunwa a jiki na?_

"Wayan waye wannan a hannun ki," ya faɗa lokacin da idanun shi suka hasko mishi ƴar ƙaramin wayar da Ruma ta bani mai keypad,

"Nawa ne, Rumaisa ne ta bani"

_Nice, ta iya bada amsa yanda ba sai mutum yasha wahalar tambayoyi masu yawa ba zata bashi gamsashshen amsa_

Ya ciro dalleliyar wayan shi Samsung Galaxy S20 ya miƙa min
"Here, samin digits É—inki a nan"

Tsantsin wayan kaɗai ya sanya min tsoro kada ya suɓuce ya faɗi ya fashe, luckily ya saka a kan dialer so bansha wahalar saka numbern ba na miƙa mishi wayan a hannun shi, bai sake ko tari ba ya tashi ya fita,

Daga nan na wuce part É—in hajiya luckily sulthana bata gidan sai mataimakiyan ta hajiya nana, har aka sha ruwa ban je ko ina ba mukayi tarawih sannan muka kutsu É—akin aunty Zaytoon yin hira wanda yawanci su sukeyi ni nawa ido don yanzu bani gangancin yin kallo a gidan saboda shi,

Ina zaune Ruma tayi pillow da cinya na wayana ya shiga ringing, da saurin na ɗaga ina tunanin Zayyad ne sai kuma naci karo da baƙon number.............🤦🏻‍♀️

Love you my fans😍

#team SS💙
#team SZ❤️

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

*Don't be afraid of making mistakes, as it is the only route that you must follow to reach success*💡

27🧝🏻‍♀️
Ɗaga kan Ruma dake saman cinya na nayi na Miƙa mata wayan,
"Gashi ki amsa, inaga ke ake nema"

"Anya kuwa? Bani kiran kowa fa da layin bayan Æ´an gida kuma suma na faÉ—a musu na daina amfani dashi, bama kowa ne yake da wannan contact É—in ba amman kawo mu gani" ta faÉ—a tare da amsan wayan ta saka a kunnen ta tare da yin sallama,

Sulaiman dake study room yana zaune, ya tasa takardu a gaban shi amman ya kasa komai haka kawai yake jin shi wani iri cikin ɓacin rai, he doesn't have someone to talk to, yanzu kuma ya kira Saudat don yaji muryan ta ko zai samu ranshi yayi mishi sanyi wannan mahaukaciyan yarinyar ta ɗauka zata ƙara ɓata mishi rai,

Haɗe rai yayi kaman tana gaban shi ya ɗaure fuska ɗan murmushin dake saman fuskan shi ya ɓace cikin kaushin murya yace
"Bata wayan ta kafin yanzu ranki ya ɓaci"

Bata sake magana ba tayi saurin miƙa min wayan tare da faɗin "gashi, babban yaya ne" wanda hakan ya jawo hankalin ƴammatan ɗakin dukkan su suka juyo suna kallo na cikin firgici da jin abinda Ruma ta faɗa, don dukkan su sun sha mamakin ƙarfin dalilin da har babban yaya ya sami contact ɗina ya kira ni a wannan lokacin it must be something very big,

Kallon su kaɗai ya dasa min tsoro a cikin raina, kaman wanda tayi wani laifi irin wannan kallon tuhuma haka ? Sun zuba kunnuwa suna sauraron jin ba'asi, jiki na yana rawa na saka wayan a kunne tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi na,

Lumshe idanun shi yayi ya ware akan wrist watch ɗinshi ƙarfe 10 har da mintuna 8,
"Ki tashi a cikin mutane, da ke kaÉ—ai nake son magana ba da gayyan Æ´an uwan ki ba"

Kalkon su nayi ɗaya bayan ɗaya naga har yanzu hankalin su bai bar kaina ba suna jiran jin abinda zan faɗa bayan sallaman da nayi basu ƙi ma nasa musu wayan a handsfree suji komai ba, ga kuma umarnin oga kwata_kwata,

Ignoring their looks na miƙe a hankali na fita daga ɗakin na zauna a parlo amman abinda ban fahimta ba shine yanda akayi mutanen da nake zauna dasu saboda wani dalili na ƙanƙanin lokaci suka zamo ƴan uwana, ko daya ance musulmi ɗan uwan musulmi ne, rasa abinda zan faɗa nayi har saida ya tambaye ni "kin tashi" na amsa da
"Eh" a taƙaice,

Shiru ne ya ratsa tsakanin mu na Æ´an sakwanni kafin nayi saurin gaishe shi "ina wuni" ba tare da saka ran zai amsa ba,

"Lafiya ƙlau"

"Hmm.." na furta saboda rasa abin faÉ—a,

"Uhm.. me yasa Ruma take amsa kiran ki? Ko shima baki iya bane?"

"A'a na iya, banyi tunanin kai ka kira bane"

"Ohh.." ya faÉ—a tare da É—an zaro ido "daman akwai wa'inda kike jiran kiran su ne?"

"A'a ba haka bane" nayi saurin kare kaina "sim É—inta ne a wayan, na É—auka ita ake nima"

"Ok, amman ki kiyaye, yanzu karatun ki shine zaki sa a gaba, bani son wasa Saudat, ban yarda da shagala ki zauna tara ƙawaye kuna abinda bai kamata ba, dukda size ɗinki yafi shekarun ki amman you are too young, just focus! kada ki kuskura wani samari ya ɓata miki daman da kike dashi ya saka ki bar lokaci ya ƙure miki baki amfana da komai ba, a yanzu karatun ne kawai gatan ki idan lokaci yayi zaki samu wanda ya dace dake kin jini?"
Chapter 32 · 0% Book details