← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 73

Sashe 7

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Furera ce ƙawata Yarima ya keta mata haddi amman babu wanda ya san da hakan, har itama fureran bata sani ba, don saida suka fitar da ita daga hayyacin ta shi da abokin shi kafin suka far mata,

Tsayawa mahaifin ta yayi sakare yana kallon halin da ƴarshi take ciki, ganin haka yasa ya Aminu ya ajiye ta a ƙasa a wurin bata ko motsi kaman gawa, kafin ya samu daman magana yaji sauƙan sanduna a kanshi ta ko ina,

Duk yanda yake roƙonsu su tsaya su saurare shi basu kula ba saida sukayi mishi lilis, sannan suka jashi a wulaƙance har kofar gida wasu ɓarayi daga cikin wanda suka dake shi suka haɗa da kuɗin jikin shi suka ƙwamushe,

Haka Malam ArÉ—o ya fito ya samu É—anshi cikin wani hali, ga mutane da sanduna da makamai a kanshi a hakan ma saida sukayi mishi warning cewa idan Furera ta buÉ—e ido ta faÉ—i cewa da hannun shi a cikin abinda ya same ta abin ba zai musu kyau ba,

Ina zaune da tray ɗin abincin a gabana na cure wuri guda saboda sanyin da ƙasan yake dashi kuma ya haramta min zama wani wuri da ba zan ɗauki wannan sanyin ba sai yace ina muradin haɗa matsayi na da nashi ne,

A birkice ya shigo ɗakin ganin haka yasa nima nayi saurin miƙewa na nufe shi da nufin tambayar shi abinda ya faru amman jinin da na gani ya ɓata jikin shi yasa na tsaya Turus ina kallo, kardai ace yau ma kumawa yayi? Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, mai yarima yake son maida kanshi ne?

Duk ranan da akayi musu sarin kayan maye to sukan je ne su sami wuri su kebe su sha suyi tatil sai a adana sauran wanda zai kaisu ƙarshen wata kafin a bazu gari kuma komai ta fanjama fanjam!!

Wannan shine karo na biyu da yarima ya shigo min cikin wannan yanayin kuma bani da ikon tuhuman shi,

A gaggauce ya cire kayan ya sauya da wani sannan ya jife ni dashi tare da bani umarnin na tsaftace mishi su, ya zauna hankalin shi kwance ya fara kwasan girkin da aka ajiye mishi dan bayi da wani tsoro ya san babu abinda zaije ya dawo tunda yana da mai gari a matsayin uban shi,

Haka na tattari kayan na fice cikin daren na kama wanke kayan inayi ina zubar da hawaye, nikam naga ta kaina na haɗu da ƙaddarar rayuwa saidai kuma ban sani ba ashe babban ƙaddarar rayuwa tana gaba...........🤦🏻‍♀️

*Ku ƙaro sharhi, na ƙaro typing*🧘🏻‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

حَسْبِيَ اللَّهُ لَآ إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ

(Hasbiyallahu laa ilaaha illaa huwa aalaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim)
×7 da safe /×7da yamma

_(Seven times)(Allah will grant whoever recites this Seven times in the morning or evening whatever he desires from this world or the next.)_

05🧝🏻‍♀️
Lokacin da Furera ta farka aka tambaye ta waye ya mata fyade bata ɓata lokaci ba tace musu Ya Aminu ne, amman ta faɗi hakan ne saboda dalilai guda biyu,

Na farko don ta rufa wa kanta asiri, domin taje wannan wurin ne don ta haɗu da miji na Yarima saboda tabi ta matsa mishi kan zancen ya aure ta ta zamo matar shi ta biyu amman hakan ba mai yiwuwa bane saboda aure na dashi ko rabin shekara baiyi ba idan yayi zancen ƙara aure ma mahaifin shi ba zai yarda ba, kuma ga bulus yana gani ba zai bari ya wuce shi ba,

Shiyasa ya bari sai ranar da zasuyi service na miyagun ƙwayoyi su hau kan babban network, ya kwatanta ma Furera jikin wannan kangon taje ta jira shi, suna zuwa shi da ɗaya daga cikin masu take masa baya suka watsa mata abinda yayi saura ta fita hayyacin ta.....

Ta san idan ta buÉ—i baki tace bata san waye ba aka bi diddigi aka gane cewa ita takai kanta wurin to zata shiga babban Matsala, sannan taji lokacin da ake dukan ya aminu bayan ya É—auko ta suna faÉ—a mishi duk abinda ya same ta ya kuka da kanshi don sai sun raba shi da rayuwar shi, shiyasa kawai tace shine,

Sannan dalilin ta na biyu kuma don ta É—au fansar auran yarima da nayi bayan na san ta daÉ—e tana son shi,

A karo na farko da munafurcin ɗan Laraba yayi mana amfani kenan, Furere tana gama bada statement ɗin ta mutane sukayi caaa za'a zo a tsire ya Aminu sai kace a lokacin aka fara fyade a garin, abinda ban sani ba ashe Yarima ya lallaɓa ya faɗa wa mahaifinshi shi yayi wannan aika aikan shiyasa Mai Gari shima ya shiga maganar dumu_dumu ya ƙara assasa mishi wuta Saboda ya samu a hukunta yayana maganar ta mutu,

Kafin masu yanke hukunci suzo ɗan Laraba ya ɗibo ƙafa yaje gidan mu ya faɗa ma baba abinda yake faruwa, a take baba ya tarkasa tarukucen ya Aminu ya saka shi ya haura ta katanga ya gudu daga ƙauyen mu gaba ɗaya dan tseratar da kanshi daga laifin da bai aikata ba, kuma har yanzu bai dawo ba,

(Shine yayan jaÉ—e wanda ya fi iya aikin likitancin gargajiya da kuma bada magani wanda aka ce an kore shi daga garin a littafin Matar Kulle)

Suna zuwa babu niman izini babu komai suka ɗuru cikin gidanmu suna niman Ya aminu basu same shi ba, babu wanda ya taɓa mahaifina don duk taurin kansu ya zamo musu gagara badau domin kaf ƙauyen babu wanda idan rashin lafiya ta taso shi bayi zuwa wurin shi musamman idan annoba ta shigo kaman su muran tsuntsaye da gudda maza da agana da dai sauransu,

Dukda kuwa suna da asibiti amman ƙarama ce sosai bai wuce girman dispensary ba, kuma babu likitoci babu kayan aiki ga tsawwalawa da nurses ɗin wurin suke yi,

Amman sunyi ma jaÉ—e dukan fitan hankali bayan sun tafi dashi sun kulle shi da gargaÉ—in sai an kai musu ya Aminu kafin su rabu dashi, ran baba yayi mishi zafi sosai amman haka ya barsu da halin su ko hanyar gidan mai gari bai taka ba tunda aka fara case É—in, da kansu suka gaji da ajiye shi suka sake shi ya tafi,

Amman da aka kwana biyu suka ga ya Aminu bai dawo ba sai suka fara mana ɓarna, idan aka fita kiwo da dabbobin mu sai su kashe wasu ko kuma su sace na sacewa, a haka da ɗaɗɗaya suka fara ƙarewa kullum muna cikin asara, saida aka hallakar da kusan rabi kafin baba ya haƙura da kiwon baki ɗaya ya tarkasa su duka ya siyar suka koma noma, shima dai dan sunga abinda yake nomawan ba wani yawa gare shi bane suka bar mishi don bai wuce abinda zasu ci na shekara ba,

Ranar wata litinin da safe na fito haɗa ma Yarima ruwan wanka wanda ke kwance har wurin ƙarfe 10 yana baccin asara ko sallan asuba baiyi ba, mahaifiyar Furere ta shigo gidan, ban lura da ita ba saboda batayi sallama ba ta kutso kai, na wuce bakin murhu zan sauke tukunya daga kan wuta sai ji nayi an tunkuɗa ni na bugu da jikin bango ruwan zafin dake tukunyar hannu na ya tuntsure wani ya ɓyallu a jiki na,

Taimakon da Allah yayi mun ɗaya ruwan bai tafasa ba domin yarima baƙin rago ne ko ruwan zafi sai yayi masa raki, amman duk da haka naji zafin shi sosai a saman fata na,

Hakan bai isheta ba a cikin kitchen É—in ta rufe ni da duka, tana jimÉ—a na tana min Allah ya isa da taga mutanen gidan sun fito suga abinda ke faruwa saboda ihun da nakeyi sai ta saka kukan munafurci amman duk da haka bata bar tima na ba,

Duk cikin su babu wanda yayi yunƙurin ceto na, na gama kwashe ƙasa da kunkuniya dake jikin garu a kayana nayi duƙun_duƙun lokaci ɗaya, saida maman Furere ta gaji dan kanta ta rabu dani, ko ita da tayi dukan sai haki takeyi ballantana ni wanda aka daka?

"Shegiya, mayya, tsinannu kawai, Allah ya wadaran zur'iar ku gaba ɗaya don kun zamo mana masifa da annoba a gari, ƙarshen ku ba zaiyi kyau ba wallahi kun nakasa rayuwar yarinyar da ta gama amincewa dake, to wannan hukuncin da nayi miki ba komai bane a kan wanda zanyi miki nan gaba idan har Aminu bai fito ya miƙa kanshi ba, ki faɗa ma iyayen ki ni Safara'u nace sai naga bayan Aminu duk inda ya shiga ya fita wallahi sai nayi ajalin sa" tana gama faɗan haka fuu tayi waje,

Tunda ta fara magana har ta gama babu wanda ya tanka ta, saida ta fita yadikon Yarima (kishiyar mahaifiyar shi) wanda kowa a gidan yayi mata shaidan rashin kirki ta ƙaraso inda nake ɗuƙe ina kuka ta ɗago fiska na tukunna ta kwashe ni da mari tana gwada ni da yatsar ta manuniya kaman zata tsole min ido,

"Tunda muke babu wanda ya taɓa shigowa cikin gidan nan yayi mana hargowa ko tashin hankali amman gashi saboda ke yau an shigo har gidan mulki an tada mana hankali to kema hankalin ki ba zai kwanta ba daga yanzu ki fara ƙirga kwanakin ƙuncin ki cikin gidan nan sai kin yaba ma aya zaƙin ta"

A taƙaice dai ba shigowar baba Safara'u bane ya samo wannan ƙiyayyar tsakanin mu ba, gaba ɗaya bansan mai nayi ma yadikon Yarima ta ɗauki karan tsana ta ɗaura min ba duk da Yariman ma ba sonshi take ba amman bata iya nunawa tana tsoron saka ƙafa ɗaya da magajin gari don ko uwar da ta haife shi ne ta saka shi a gaba sai ta fuskanci bacin rai,
Chapter 7 · 0% Book details