← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 73

Sashe 14

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmmm eviritim (everything) a gidan nan is fasfet (perfect), hankali na ya tafi kallon fasfet ban san har munzo jikin main door na part É—in ba, hankalin aunty Nasreen bayi wuri na ita ta saka kanta a gaba a tunanin ta ina abin da ya kamata ne sai jina nayi dimm, na bugu da jikin mutum,

for a moment na tsaya ina tunanin anya wannan mace ce? A maimakon na kauce a hanyar ko na bada haƙuri amman ina tsaye ina tunani saida wani dogon tsakin da ya ja ya dawo dani cikin hayyaci na na ɗaga idanuna na zuba mishi,

Ya ƙanƙance idanu cikin masifa ga jiki na manne da nashi dan har yanzu ban tabbatar ko karo mukayi ba ballantana na san me zanyi gaba,

"Sh***t, who is this stupid girl? Ya tambaya a tsawace, ni dai banga kowa a wurin ba, bansan da wa yake magana ba, amman duk inda aka ambaci sitifid (stupid) na san zagi ne, wato zagi na yayi don kawai na bangaje shi ba tare da sani na ba? Dan cin mutunci ma zagin da turanci??

Saurin matsawa nayi daga jikin shi, yayi saurin wucewa tare da sake jan wani tsakin sannan ya juya ya tafi har ya shiga part É—in dake gefen wanda zamu shiga ina kallon bayan shi, wannan wani irin zafin rai ne? Na tambayi kaina, shi wannan wani irin mutum ne mai tsanani sai kace wani mala'ika?

"Haba Saudat! Ina hankalin ki yake ne zaki jawo mana magana? Yanzu da ya dake ki fa yanda ranshi yake a bacen nan kuma baki iya bada haƙuri ba?"

"Tabɗijam, sitifid fa yace mun babban zagin da yafi ko wanne a duniya kuma kice na bashi haƙuri? Wallahi da saidai ya dake ni amman duk wanda yace min sitifid ba zan bashi haƙuri ba"

Girgiza kai kawai tayi muka sake kinkiman jakan kayan mu mukayi ciki dashi, babu kowa a parlorn bayan su biyu, sun lunƙuma cikin kujera ɗaya da laptop a cinyar ta tana nuna ma mai waya a hannu wani abu,

Sallamar da mukayi tare da niman wurin zama ne ya jawo hankalin ruma dake riƙe da laptop tana zaune kusa da zaytoon, da fara'a a fuskar su suka tarbe mu muka gaisa sannan Ruma ta nufi ɗakin Hajiya da niyan kira mana ita, Zaytoon kuma ta saka maids kawo mana abun sha,

Ina zaune ne a wurin amman hankali na ya tafi yawo kallo kawai nake zubawa tare da saƙe_saƙe a cikin zuciya ta, saida Hajiya ta kira sunana kafin nayi firgit ita kallon ta idanuna a waje kaman anyi min ƙarya,

Murmushi tayi tace "Saudat ranan kinyi min rowan kwana yanzu rowan magana kike mun?"

Murmushi kawai nayi na gaidata ina mamakin yanda tayi saurin gane ta bayan haÉ—uwar mu ta farko ma a tsatsaye mukayi shi muka tafi kusan shekara É—aya da ya wuce kenan ma,

"Lafiya ƙlau, kinga har sunan ki saida auntyn naki ta tuna min da ƙyar ma na gane ki, fatan yau zama mana zakiyi ba tafiya ba"

Dariya naji inajin daÉ—in yanda matan take da kirki sosai, ranar ma da nazo haka ta dinga jana a jiki,
"Kaya muka kawo aunty Yusrah ne ta aiko mu anjima kaÉ—an zamu tafi"

"A'a ban yarda ba gaskiya, yau tunda kika zo kwana zaki mun, ga ƙawa nan ma nayi miki" ta faɗa tana nuna Ruma,

Ɗaga ido nayi na kalli haɗaɗɗjyar yarinyar da aka kira da ƙawa na, hada idon da zamuyi ta sakar mun kyakkyawar murmushin da yasa beauty point ɗinta suka lotsa, ta ajiye system ɗinta a saman centre table tazo gefe na ta zauna tare da saka hannun ta cikin nawa tana dariya tace

"Aunty Zaytoon to Kinga yarinyar da tafi ya Zayyad kyau kullum sai ki saka shi ya dinga jin kai ma mutane, kira shi yazo ya ganta"

"Ai yanzun nan ya fita inaga bayi jin daɗi ne, har kuwa yana cewa zai tsaya ya taya ni zaɓe tunda ya fini sanin kan gayu da abu mai kyau amman sai fitar shi kawai na gani bai faɗa min dalili ba"

Ohhkkk! Wato Zayyad shine sitifid É—innan da ya fita? Tun da ya zage ni nima daga yanzu zagin shi zan dinga yi kuma daga yanzu shima sitifid ne, kuma insha Allah duk randa na sake haÉ—uwa dashi koda zai dake ni sai nace mishi I am mad, nasan shima zagin zai mishi zafi,

Ina zaune ina faman tsilli tsilli da ido suka cika parlorn damm suna zaban kaya, kusan zannuwa 30 amman a cikin su akwai wa'inda basu samu ba da na ƙirga yawan su basu wuce 8 ba, a lokacin ya Safwan ya fara rangaɗa ma Nasreen kira ta fito su tafi,

"To gashi kuma muna sabon list dan kayan sunyi kyau sosai kinga yaran suna son ire_iren su, ba zaki É—an jira mu gama ba sai ki tafi mata dashi?"

Murmushi Nasreen tayi tare da miƙewa, tana tashi nima tsugul na miƙe,
"Ai ni ba gidan ta zan koma ba, zan wuce gida ne Saudat ne zata shiga shiga abun hawa ta kai mata, tace ma a faɗa muku ta sauƙa yau da asuba an samu ɗa namiji"

"Alhamdulillah! Masha Allah!! Allah ya raya shi da imani amman bai kamata yarinya ƙarama kamar wannan a saka ta a public transport ba idan ta ɓata fa?"

Duba jiki na fara yi kaman mai niman wani abu, ina son ganin abinda wannan hajiyar ta gani a jiki na ne take kira na yarinya, ai inaga ko ƙauyen wuroɓokki aka saka ni a mota na tafi ba zan ɓata ba ballantana nan da wani unguwa kaɗai,

"Amman kada ki damu ki tafi abinki kawai zan saka a maida ita har gida"

Godiya tayi mata ta tafi ta barni, and i was like, "how she do is me?" (How could she do this to me) abinda naji aunty Yusrah tana faÉ—a wani lokaci idan aka yi mata ba daidai ba,

Ina kallo ba don naso ba aunty Nasreen ta tafi na zauna ina jiran su gama, ina jin irin mugun kallon da take watsa min a jiki na, bansan me yasa tun da na shigo take harara ta ba,

ni banma taɓa ganin ta ba don last zuwa na gidan nan tare da aunty Yusrah duk ƴammatan nan basu nan, gidan empty yake babu kowa bayan hajiya part ɗin su stipid kanma a rufe yake an faɗa mana cewa gaba ɗayan su sun tafi Umrah,

To a ina ta taɓa gani na har wani mummunan abu ya taɓa shiga tsakani na da ita da take bina da kallon banza? Saidai ban sani ba ashe baƙin hali da kallon banza a jinin Nana yake indai ta washe ka a kallon farko to taka ta ƙare a wurin ta,

Haka suka gama abinda zasuyi ina zaune kallon banzan nana ya hana ni sukuni na rakuɓe a wuri ɗaya ina kallon ta ta ƙasan ido, duk sona da ciye_ciye amman ina kallon kayan daɗi haka na barsu,

duk wayo da dabaran da hajiya tayi min don na yarda na kwana firr naƙi, har kiran aunty Yusrah tayi ta faɗa mata cewa sai gobe zan dawo tace babu matsala ta yarda amman nikam nace ban jiba ban gani ba ai babu kowa a wurin ta wanda zai dinga mata aikace_aikace,

Daga ƙarshe dai ba don taso ba ta ɗaga driver ya maida ni gida, har mota Ruma da zaytoon suka min rakiya na shiga, yayin da numfashi na ya tsaya cak wani mahaukacin sanyi yana ratsa ni har ta ƙarƙashin ƙafafuwa na,

Saurin naɗe ƙafafuwa na nayi, nayi zaman tahiya amman duk da haka sanyi nake ji sosai,

lokacin da aka isa gida jina nake yi kaman na zamo ƙanƙara amman ana sauƙe ni na fara fankama ganin hankalin magulmatan unguwan ya dawo kan motar suna son gani waye kuma zai fito daga motar, har na shuge cikin gida ina jin idanuwan su a kaina,

   ******

Motar mu na fita ya ƙaraso wurin kaman zaiyi magana a dakatar damu kuma sai ya fasa, to meye ma dalilin bada haƙuri tunda bashi yayi min laifi ba?

Wataƙil ma hala abun da ya faɗa min bai ɓata min rai ba amman duk da haka bai kamata ya furta min wa'innan kalmomin ba, koda banji haushi ba zaiyi ta jin nauyin su a zuciyan sa,

Juyawa yayi cike da damuwa yaga su zaytoon sun tsaya suna ƙare masa kallo har yanzu basu tafi ba,
Ƙaƙalo murmushi yayi yace "yaya ne sisters? Kuna buƙatar wani abu ne?"

Ɓata fuska zaytoon tayi cikin wasa tace "kai zamu tambaya ko kana buƙatar wani abu ne bayan ka tafi baka zaɓa min kayan ba har an gama kwashewa yanzu ko ɗaya bani dashi,

Dariya yayi yana jan kumatun ta yace "ayyah ai bansan cewa kina jiran zaɓin haɗaɗɗe bane da na bar duk abinda nake yi nazo na zaɓa miki, amman yaushe zasu kawo wasu?"

"Ban sani ba amman kafin a fara azumi zasu kawo kaga gobe ko jibi kenan"
Sauƙe ajiyan zuciya yayi tare da faɗin Allah ya kaimu, a ranshi yana jin daɗin zai saku daman bani haƙuri,

*********
1:24am

Kunna bedside lamp tayi tana leƙa fuskar shi har yanzu murmushi yake yi ta rasa na menene ɗaya,

"Dadyn Arif" ta kira sunan shi a hankali,
Juyowa yayi ya zuba mata idanuwa ba kamar kullum ba yau da faffaɗa kuma ƙayataccen murmushi a saman fuskar shi,

"me ya same ka ne ka kasa yin bacci kuma wannan murmushin..... Ko dai riba ya ninku ne??"

Ƙarakin tsaki yaja amman murmushin bai bar saman fuskar shi ba yace, kina da matsala Sadiya, waye ya faɗa miki kuɗi ko yaushe yake kawo farin ciki? Wani abu na musamman yau na gani wanda zuciyata ya daɗe yana tsumayen sa...........🤦🏻‍♀️

_Masu cewa Sulaiman ya kama girman sa ance na faɗa muku da babban murya BA'A TSUFA MA SOYAYYA😅😅_

#vote
#share
#comment

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
Chapter 14 · 0% Book details