← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 73

Sashe 10

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana faÉ—in haka ta ajiye waya da casbin ta a seat É—in da ta tashi ta fice daga dakin,
Sunkuyar da kanshi yayi a yanda yake zaune an tokare bayan shi da filo ya haÉ—a kai da guiwa yana jin zafi sosai a zuciyar shi, rayuwar shi É—aya take da mara amfani tunda bayi amfanan kowa da komai kullum wahala kawai ake yi dashi, harta hankalin wanda suke tare dashi ba a kwance bane kullum suna cikin fargaban ya shiga matsala, basu son ganin kukan shi amman shi ba zai iya hana su kuka ba,

"Ya Allah kaine mai iko a kan kowa da komai ya Allah ka raba ni da matsalar da nake fama dashi, ya Allah ka yafe min kura kurai na ka sanya ni jin daɗin lahira idan duniya ba rabo na bace, ya Allah kaine mai iko akan dukkan komai, kai kake yin yanda kaso da kowa, ya Allah idan wannan matsalar itace jarabawata ka sauƙaƙamin kuma kasa na tsallake ta ya zul jalalu wal ikram" ya faɗa hawaye suna sauƙa daga idanun shi,

******
Da sallama ya shigo parlorn tare da wata mata a gefen shi tana ɗauke da yarinya a hannun ta da ba zata wuce shekara 2 ba, Ruma na hango su da sauri ta ajiye fork din hannun ta taje da gudu ta rungume matar kaman zata kaisu ƙasa,

Da ƙyar ta samu tayi balancing kanta tana dariyan ƙarfin hali yarinya zata ɓarar da ita a gaban surakanan ta,

"Rumaisa wai yaushe zaki yi hankali ne? Baki ganin yarinya a hannun ta ne ba zaki ɗauka mata ita ba sai ki ƙara mata da nauyin ki?"
Lakutan hancin yarinyan tayi tace "wannan mai ƙyuyan ko nace zan ɗauke ta ba yarda zatayi ba ya Nafi'u, sannun ku da zuwa"

Cikin girmamawa ta gaida su da kyar ta samu yarinyar hannun matar shi taje wurinta, suka ƙarasa gaban dining ɗin sukai squatting a ƙasa suna gaida Baba da Hajiya, ɗaya bayan ɗaya yaran dake zaune tare dasu suka fara gaida su yana amsawa tare da tsokanar su,

"Lafiya ƙlau aunty rasai" ya faɗa yana kallon Fa'iza da take faman ture turen baki don tasan wannan zuwan da suka kwaso zuga na tarban Zaytoon ne ita bata san wani dalili bane yasa kowa yake sonta ba kuma hakan na ɓata mata rai sosai, tafi so taga ko ina ana rashin mutunci ko kuma tsakanin mutane babu jituwa yanda zata samu ta caccaki kowa son ranta,

Dariya Batool tayi tare da yima Fa'iza gwalo, tace " ina kwana dadyn husna"

"Lafiya ƙalau kalaye mai kalen magana, baki da aiki kullum sai tsokanar yara kisa su raina ki"

Nana kanma tana jin haka kafin azo kanta ta tashi ta wuce ciki domin ita ƙunci kaman a jinin ta yake, abu kaɗan zakayi mata ta hau ranta ya baci shiyasa wannan wasan da yake tsakanin ta da yayun ta bata son shi don gani take kaman yaɓa mata magana suke yi da gangan,

Ɗaga murya yayi yace "ki dai raba kanki da baƙin hali don baki gaje shi ba"
Ai kuwa tana jin haka ta bankaɗa ƙofar bedroom ɗinta ta shige ciki tare da rufo shi da ƙarfi hawaye na taruwa a idanun ta, cin mutuncin da ta gudan saida ta samu shiyasa ta tsani babban yaya da ya Nafi'u su shigo gidan, gashi Sulaiman kaman maita ko yaushe yana sintiri a tsakani saboda Zayyad,

Murmushi Baba yayi yace, "nana hafsa kenan kwata_kwata baki É—auko halin mai sunan ki ba gashi an saka min ke a gaba"

"ba haka bane baba gyarawa muke son tayi"

"Gyara a hakan? Ai baku biyo ta sigar gyara ba don tozarta mutum bashi yake saka ya gyara munanan halayen shi ba, zaunar da ita zakuyi kuna ankarar da ita kurakuran ta domin ta gyara sannan ku dinga taya ta da addu'a don wannan ba halin zama cikin mutane bane gashi Allah yayi mu cikin dangi"

Sosa ƙeyar shi yayi yana murmushin yaƙe an fetta shi a gaban ƴan ƙannen shi harda su Junior a wurin, ashe irin hakan da suke ma Nana babu daɗi tunda itama akwai na ƙasa da ita a wurin,
"Insha Allah Baba, babban yaya bai shigo bane?"

Ruma ce ta amsa da "ya shigo dazu amman daga sashin anty Amarya ya fita gaba É—aya bai dawo ta nan ba"

"Ok inaga ya tafi office ne, nima zan wuce ayi mana addu'a"

Allah ya kiyaye da Allah ya tsare suke masa har ya fita,

*****
"Wannan zuwan na aunty Zaytoona ne ko aunty ummi?" Ruma ta tambayi matar Nafi'u bayan sun shiga É—akin su Batool sun samu matsuguni a armchairs dake É—akin,

Murmushi tayi tace "kema kin sani ai, dole nazo tarban ƙawata guda kusan watanni 5 bamu ganta ba"

"Maybe yanzu ta ƙara haɓaka ta daɗa zama buskuɗa dan naga kaman zaman can ƙasan daɗa hura ta yake yi" ta faɗa tana dariya, don ita ba damuwan ta dawowar da zaytoon zatayi bane burin ta bai wuce taga tana tafiya ko wani ɓari na jikin ta yana girgiza ba tayi ta kwasan dariya

Kafin ummi tayi wani magana suka ji ana shewa da ihu a parlor da sauri suka fita don wannan alama ce dake gwada sauƙar ta cikin gidan, farin ciki murmushi da annashuwan wasu ya dawo da zuwan ta ba zata taba ganin su cikin damuwa ta ƙyale ba,

Kaman yanda Ruma ta faɗa yarinyar lutiya ne amman kallo ɗaya zaka yi wa fuskarta ma gane ba wani shekaru gare ta ba don da kaɗan ta girmi Batool kusan kunika ma suke tsakanin su shekara 1½,

Da murmushi a fuskarta suka gaisawa da kowa yara suka shiga mata da kayyakin ta É—aki Ruma uwar gayya ta fara rabon tsaraba tun kafin zaytoon É—in ta samu wurin zama don kowa da sunan shi a jikin nashi harda su sulthana da Muna kuwa bata manta da su ba,

Bata zauna ba ta wuce part É—in aunty Amarya zata duba Zayyad don sun faÉ—a mata bayi da lafiya,

Tana shiga ta same shi yana sallan walha ta É—auki dessert da aunty ta ajiye mishi ta zauna ta kama ci tana jira ya idar, saida ya kammala sannan cikin nutsuwa ta tako zuwa gaban shi tayi hugging É—inshi tana dariyan jin daÉ—i da murnan haÉ—uwa da jinin ta, shima murmushi yayi yana É—an buga bayanta a hankali cikin zolaya yace

"Kwantar dani kike son sake yi tun ban gama warwarewa ba zaytoon?"

Cikin nutsuwa wanda ita kaÉ—ai take da irin ta a cikin su sai Zayyad É—in da aka saka mishi na dole tace
"Ba zaka mutu ba yaya na sai kwanan ka ya ƙare"

"To yaya hanya yaya kika baro iyayen gidan ki"

"Lfyn su ƙlau hanya kam na kwaso gajiya, yanzu ma barci nake son yi idan na tashi zan zo maka na musamman musha hira" da faɗan haka ta dauki plate ɗin ɗungurungum ta fita dashi

**********
ÆŠagowa yayi ya kalle ni ya sake maida idanun shi kan takardan yana duba duba abin da ya gani a jiki, ni kuwa sai addu'a nake yi a zuciyata Allah yasa kada yace zai maida ni gidan su yarima wannan karon dan ba na É—aya ko na biyu da yace nayi nayin ba,

"Zauna da kyau" ya umarce ni a taƙaice,

Saida hanjin ciki na ya kada jin kaushin muryan sa na gyara na zauna daga tsugunon da nake ina kallin cikin ƙwayar idon shi,

"Yanzu Saudat na 42 biyu kika sake zuwa? A halan ma an cire mutane 3 a ajin naku, da kin fara kaman zakiyi ƙoƙari kin dawo kin faɗi ƙasa warwas?"

Shiru nayi ina ƙifi_ƙifi da ido bansan me zance mishi ba don har yanzu fagen rubutu ko spelling sunana correctly ban iya ba, bani mantawa exams ɗin maths da mukayi, a jikin questions ɗin an mana misalai da oranges wurin addition da subtraction duk zanen orange aka saka, ni kuma da ban gane me za'ayi a wurin ba saboda ban iya karantawa ba dai kawai na ɗauki lemu ɗaya na zana shi ƙatoto a jikin takardan nayi submitting, sauran exams ɗinma shirme na nayi tunda ban iya karatu ba kuma ba karanta mana ake yi ba wasu sai na zauna na kwafe questions ɗin tass nayi submitting, wanda ba zan iya ba kuma sai na bari lokaci ya ciki na basu takardan su yanda suka miƙa min ko suna babu a jiki,

"Kina muradin komawa gidan yarima ko?"

"A'a wallahi" na faÉ—a tare da fashewa da kuka mai sauti, " is me is coming is girl paper do me copy me say no she do tauu me do yayyy"

"Hold it please, ni bance kimin turanci ba bayani nake so kimin da harshen hausa"

Ƙara sautin kuka na nayi ina share hawaye da ƙyar na iya buɗe baki na fara mishi bayani,
"Daman wata yarinya ce a ajinmu na gama jarabawa tace na bata ta kwafa da na hana ta shine ta dake ni nayi ta kuka amman taƙi ta bani yanzu ita an bata maki ni kume ance na faɗi kuma wallahi ƙarya ne, Hamma awada muyal useni.......🤦🏻‍♀️

_Readmores biyar gobe insha Allah😁_

#vote
#share
#comment

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

_Niman maganar ANTIMEE ya ƙare a Kan su FATI cleaner ta AMADULLE😂_
Wannan shafin taku ce tare da
*Aunty Sadiya vice da*
*Haziƙar marubuciyar nan MAIMUNA ABADALLAH (HEROIN)*
_SONKU A CIKIN JININA YAKE❤😘_️

Jiya nayi mistake wurin numbering na saka page 5 instead of page 7, bear with me please 🤦🏻‍♀️

08🧝🏻‍♀️
"Bayan faɗuwar jarabawa hadda ƙarya kika koyo saudat?"

Matso kwalla na daÉ—a yi tare da matsowa kusa da kujerar da yake zaune na saki kuka, duk yana zaune yana kallon ikon Allah baice komi ba don ba yau na fara irin wannan draman ba,
Chapter 10 · 0% Book details