← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 73

Sashe 24

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wayyo daɗi kashe ni!! Ban san lokacin da hannu na ya kai ya share guntun hawayen idanuna ba na gyara zama na saman kujera baki na buɗe na shiga kallo don na ma manta da duk wani baƙinciki da na kwaso da takaicin an kira ni daƙiƙiya kuma Sitifid, heyy dariya nake harda shewa ina tafa hannuwa don abun yana kawo light dake aunty Zaytoon bata da damuwa yasa ko a jikin ta ta gyara zaman earpiece ɗinta taci gaba da danne_dannen waya,

Kaman daga sama na ganshi ƙeƙam a gaba na, hanjin ciki na saida suka kaɗa nayi saurin runtse idanuwana don nayi tunanin yanda naga fuskar shi a bai_bai ɗin nan zabga min mari zaiyi,

Shiruu nayi ƙirji na yana lugude ina jiran naji sauƙan mari amman shiru, sai jin hannun shi nayi ya fisge remote ɗin dake hannu na ya canza channel sannan ya wurge ni dashi,

Bai tsaya a ko ina ba sai a kan goshi na, an gudu ba'a tsira ba kenan, matso ƙwalla na fara yi ina sosa wurin da ya jife ni don ba ƙaramin ƙwaluwa nayi ba na zuba mishi idanu a karo na farko ina ƙare mishi kallo,

Ga kyan siffa sai baƙin hali dukda bai kai ya Zayyad ɗina ba, don wannan yana da ɗan jiki duk da ba sosai ba amman Zayyad matsalar shi kaɗai wanda ke sanya shi rashin lafiya kusan kullum ya isa ya saka shi tsomarewa,

"Ke!! ba zaki bar kallo na ba?!"
Ya faɗa a fili cikin zuciyar shi kuwa kasa jure irin saƙƙonnin da idanu na suke aika mishi yayi, yana jin wani abu mai ƙarfi na tsirguwa har cikin jinin shi amman ba zai iya jurewa ba bayi son girman shi ya faɗi a gaba na da kuma ƙanwar shi,

"Ke ƙwaƙwalwar kifi gare ki ko? Duk abin da ya faru ɗazu bai ishe ki ishara ba shine kika dawo kika ƙara maidar da hankalin ki gaban tv saboda kina son tabbata a daƙiƙanci baki son yin karatu ko?"

Ina jin wannan kalmar ya sake fitowa daga bakin shi na saki kuka, Zaytoon tana kallo na cike da tausayi amman babu abin da zata iya don itama bata fi ƙarfin a haɗa da ita ba,

Bai damu da kukana ba a yanzu hawayen ta sun daina ɓata mishi rai don tunda ta zubar a ranar farko yake da tabbacin zata ci gaba da zubarwa yaci gaba da cewa

"To bari kiji daga yau nayi miki iyaka da kallon TV a gidan nan very soon zaki fara karatu kuma dole ki maida hankali ki san abinda kike yi don ba zan lamunci zaman ki haka ba"

Da faɗan haka ya fice daga gidan gaba ɗaya, haka aunty Zaytoon ta zauna tayi ta lallashi na daga ƙarshe a bedroom ɗinsu na kwana bata bari hajiya taji abun da ya faru ba ko kaɗan, amman ni na saka ma raina da ikon Allah ko kwana ɗaya ba zan ƙara a gidan ba zan koma gidan aunty Yusrah,

18/Ramadan/1442

"Ban yarda ba ban amince ba kaji na faɗa maka, ka san duk yanda zakayi ka ɗauko ƴar mutane ka dawo da ita gida, kai kanka shaida ne na cewa bani barin ta taje ko ina bayan gidan iyayen matar ka, ba don jego ba ko gidan ka ba zan bari tazo ta zauna ba wallahi amman shine zaka ɗauke ta ka kaiwa wasu mutane can da basu san amfanin ta da muhimmancin ta ba? Ka san girman alƙawari kuwa Khamis?"

Sassauta murya yayi yace "ayi haƙuri Mama insha Allah a yau zanje na ɗauko ta, insha Allah ba za'a sake makamancin haka ba ayi haƙuri dan Allah"

"Gaskiya kam, aje a ɗauko min ɗiya ta ta dawo cikin mu dan a yanzu mune dangin ta, matuƙar ina raye ba zan taɓa bari saudat ta wulaƙanta ba"

"Insha Allah mama zan dawo da ita gida a yau É—in nan"

Sallama sukayi ya kashe wayan sannan ya ɗago yana kallon Yusrah da ta sunne kanta ƙasa yace
"Kinji daÉ—i kin haÉ—a ni da mahaifiya ta ko?"

"Baby kayi haƙuri wallahi na gaji da zaman ta a can ɗin ne, kwata_kwata hankali na ya kasa kwanciya I'm feeling like she is not alright"

"Ai Shikkenan hankalin naki sai ya kwanta tunda kin samu cikar baurin ki idan ta dawo magana ta ƙare"

**********
Zaune nake gaban mirror bayan nayi wanka na saka kaya na fara tsara kwalliya wanda nake kowa wurin aunty Fa'iza da kayan kwalliyan Ruma wanda sai ta gama mini wulaƙanci ta zage ni son ranta kafin ta koya min,

Babu laifi na É—an fara koyan wasu abu kaÉ—an daga ciki,

Buɗe ƙofar ɗakin ruma tayi ta shigo tare da sallama da shirin fita ta yafo wadataccen mayafi ta ƙaraso wuri na ta gyara min kuskuren da nayi sannan tace na raka ta,

"Ina zamu je?"

Ta san idan tace min gidan babban yaya ne ba zan je ba shiyasa kawai tace "gidan wata auntyn mu ne zan kai mata wani aika zaki raka ni ina?"

Da sauri na gyaɗa kai tare da miƙewa na zari hijabi na bita a baya na ma manta da zancen komawa na gida a yau wanda nayi alƙawarin sai na tada hankalin hajiya ta saka an maida ni muka fita ina mararin shiga haɗaɗɗiyar mota,

Muna fita muka ci karo da Sitifid wanda shima fitowar shi kenan zai shiga ya same ni, yayi kyau sosai cikin ƙananun kaya,

Cikin girmamawa da ɓoyayyar soyayya wanda ke madaƙe cikin zuciyata na gaida shi ya amsa feeling the same, sannan ya tambaye mu wurin da zamu je da sanyin safiya,

Ruma bata ɓoye mishi ba tace mishi gidan aunty Sadiya shi dake ya gane waye sai yace ba zamu je ba dukda kuwa ya san babban yaya bayi gida amman bayi son na sake shiga ɓacin rai yau ma,

Amman ni dake sahibar yawo ne haka nayi biris da zancen shi na ishe shi da mita da magiya da yasa bai so ba ya barmu muka tafi tare da mana addu'an Allah ya dawo damu lafiya............🤦🏻‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

*Idan ba zaka iya amfanar mutum ba kayi ƙoƙari kada ka cutar dashi*💡

20🧝🏻‍♀️
Shatin karan hanci na saida ya fito a jikin glass ɗin windown motar saboda yanda na manna kaina a jiki ina kallon gari unguwannin mutanen nan kawai abun kallo ne, so silent and peaceful babu kowa a waje bayan masu tsaron mutanen cikin gidajen, wannan idan a ƙafa kake tafiya sai a sace ka babu wanda ya sani,

Bamuyi tafiya mai nisa sosai ba muka ƙaraso gate ɗin gidan driver ya kutsa kan motar mu ciki, yana parking wani yaro yazo da gudu ya buɗe side ɗin da Ruma take yayi hugging ɗinta,

Jan cheeks É—inshi tayi yana dariya

"aunty wacece wancan?" Ya faÉ—a tare da gwada ni da yatsa,

"Sunan ta Aunty Saudat ka gaida ta"

Babu gardama yaron ya miƙo min gaisuwa nikam tunani na ne ya ɓace yayin da na hango kamar zazzaɓi (Sulaiman) ƙarara a fuskar shi, saida muka fita daga motar na tambayi Ruma yaron waye tace min ai ɗan babban yaya ne kuma gidan shi muka zo,

Saida na saki iska ban sani ba wallahi saboda tsoro cikin zuciyata ina jero addu'oi,
Ni Saudatu nayi shirin barin gidan su sitifid ne saboda zazzaɓi gashi kuma na kawo kaina har cikin gidan shi, hala ma dalilin da yasa Hamma Zayyad ya hana ni zuwa kenan naƙi ji,

A daidai entrance na main door naja na tsaya tsoro ya gama shiga na, na riƙo hannun Ruma da hannu na ɗaya wanda yake faman karkarwa saboda tsoro
"Gaskiya nikam mu koma ba zan iya shiga gidan nan ba"

"A kan me? Saboda babban yaya wai?"

GyaÉ—a mata kai nayi "Allah a tsorace nake Ruma ba zan iya sake haÉ—a ido dashi ba"

"Habawa boÉ—É—i yayan nawa sai kace dodo? To kwantar da hankalin ki bayi nan wurin matar shi muka zo ba wurin shi ba"

Sauƙe ajiyan zuciya nayi nabi bayan ta muka shiga hannun ta riƙe da na Arif,

A hakince muka sami matar tasha lace ƴar ubansu jewelries ɗinta na gold sai sheƙi suke taci kwalliya tana baza wani ƙamshi mai daɗi harta ƙafarta hill shoe ne 4inchs kai kace wani wurin zata, amman ba daga nan ba Sadiya akwai iya ado da ɗaukar wanka saidai tana fama da wauta da ballagazanci gashi Allah ya haɗa ta da miji ɗan duniya,

"Sannu da hutawa aunty halima"

Murmushi tayi tare da faɗin "yauwa Rumaisa sannun ku da zuwa, lallai kam kin cika alƙawari kinyi sammako, ke da ƙawar ki ne?"

"Eh aunty itama zata taya mu ne"

"Very good na gode sosai, yaya sunan ki Æ´ammata?"

"Sunana saudat" na faɗa cike da jin haushin Ruma, ita da tace nazo na rakata ta kawo aika yanzu kuma naji ana maganar tayi kalan zazzaɓi ya dawo ya same mu?

"To muje ko?" Ta miƙe tare da jan hannu na, bani da wani zaɓin da ya wuce nima na bitan ba don raina ya so ba muka shiga bedroom ɗinta muka fiddo da kayan dake jakar da muka zo dashi, ashe ba aika bane kaya ne da zamu saka muci aiki gashi nifa tun yanzu na fara jin azumin nan,

A kitchen muka riski Sulthana da Muna, ta gama zaman banzan ta cikin gidan su sitifid bata samu komai ba shine ta haƙura ta dawo, yanzu haka sunyi rakace_rakace a kitchen ana ta hidiman haɗa abinci kala_kala saboda da rana Sulaiman zai tarbi wasu clients ɗinsu arna da zasu zo gida su tattauna hidiman business shine fa yace Sadiya ta shirya musu abinci abun harda gayya, bayan ƙannen ta biyu da kuma maids ɗinta,
Chapter 24 · 0% Book details