Sashe 55
Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyada kai nayi da sauri cikin jin daÉ—i, a hankali na furta "eh" don zan iya cewa wannan ne karo na farko da Inna ta fiskance ni akan wani abu da ya shafi rayuwata, harma take niman jin ra'ayina.
Shiru ta sake yi na Æ´an sakanni kafin tace
"Wani shawara kika yanke?"............🧚
_Well... Zaku ga maganar kowa ya dawo daidai a wannan page ɗin🤓 amman bawai hausa ya zauna a bakin fulanin bane saidai accent din ne nada wahalar fahimta ga wanda ba bafulatani ba shiyasa kawai na gyara shi saboda sauƙin ganewa🤠_
*Ina yiwa É—aukacin al'ummar Musulmi barka da Sallah🥳ðŸ’, Allah ya maimaita mana.✨ ya nuna mana na shekaru aru_aru masu zuwa🥰*
(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
ðŸ¤ðŸ’šðŸ¤
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚ðŸ¤ðŸ’š
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsÑ‚ ιмÏσÑтαηт qυαℓιтү α ωÑÎ¹Ñ‚ÎµÑ cαη нαvε, ωε *_ÏÑσғιcιεηт ωÑιтεÑ's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαÑε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
44ðŸ§ðŸ»â€â™€ï¸
"Bani son Sulaiman Inna.... gaskiya ba zan iya auren shi ba"
Daga kallon da tayi mun nasan batayi tsammanin wannan amsar daga gareni ba, harɗe fuskana nayi babu alamun fara'a domin ta daɗa gaskata zancena, haka tayi shiru ta zuba min idanu na tsawon lokacin da bata taɓa yi ba tsawon rayuwarta,
"Kina nufin ba zaki sake aure ba kenan? Ba zaki shiga É—akin ki na sunna ki mutu a can ba?"
"Ba abinda nake nufi ba kenan Inna kawai...." Ban ƙarashe magana ba ta katseni muryarta kaman mai shirin kuka tace
"Mun yarda zamu ɗauki duk wani wulaƙancin da za'ayi mana a sanadin haka, musulunci bai hanaki ƙara aure ba kada kibar al'ada ya hana ki"
Matsowa tayi daff dani sannan ta jawoni jikinta ta rungume
"Kiyu haquri boÉ—É—i kada fushin abinda mukayi miki ya saka ki bari rayuwarki ta tarwatse kiyi sallama da farincikin dake cikin ta.
Tsawon shekaru kusan 6 da kikayi nesa da gida bamu iya mun waiwaye ki ba, bamu sani ba ma ko kina raye ko kin mace, bamu ma san wani irin rayuwa kike yi a wurin masu riƙon ki ba. Munyi buri da fatan sake zuwa gareki amman duk iya qoqarin mu mun gagara.....
Tunda ta fara magana na saka kuka tare da saka hannaye na biyu na qara rungume ta a jiki na ina jin kwatankwacin ciwon da itama take ji a nata zuciyan.
Qarfi da yaji an raba uwa da ƴarta, da ƙarfin cin tuwo aka haramta mata raɓar abinda ta aifa daga cikinta.
"Kiyi haquri dan Allah idan abinda ya ɓata miki rai kenan, ba ko wani namijin bane yake kaman yarima, insha Allah wanda zai aure ki yanzu zai ɗauke ki da daraja kuma ya baki farinciki na duka duniyarnan da miji yake bawa matarsa"
Na gane cewa Inna bata fahimci abinda nake nufi bane amman bashi bane abu mafi a'ala a yanzu ba,
Wannan yanayin da nake ciki yafi min komai muhimmanci, shine abinda nake tsumaye tun yarintana da kuma musamman lokacin da nayi nesa da gida,
A kullum bani da burin da ya wuce ganin ranar da zanyi sharing pain ɗina, farincikina da baƙin ciki na tare da mahaifiyata.
Na faɗa mata damuwowina domin ta taya ni maganinsu dukda kuwa aunty Yusrah da mama suna ƙoƙari ta wannan fannin amman na uwa daban ne.
Shiru nayi na langwaɓe a jikinta sai hawaye ne kawai ke sintiri a fuskana amman na gagara faɗa mata matsalata don nasan raba hankalinsu gida biyu kawai zanyi duba da matsayin da sulaiman yake dashi a wurinsu yanzu ace sun tsallake shi sun bawa qanin shi ni? Abin da kamar wuya! Sannan nima nasan ko sama da ƙasa zasu haɗe a yanzu ba zasu min dole ba, shiyasa na ja baki na na saka mishi sakata... Yanzu na jingina komai ga hamma zayd, na yarda dashi ɗari bisa ɗari ba zai taɓa bari soyayyar mu ta lalace ba.
Muna zaune ina zancen zuci har barci ɓarawo ya ɗaukeni da zazzafan ciwon kai, amman ko banza na zubar da rabin ciwon dake cina a zuciya.
Gyara min kwanciya Inna tayi ta rufe ni da bargo dan ana ɗan taɓa sanyi, sannan ta fita ta kintsa ko'ina ta ɗauko indo ta kwantar da ita a tsakiyan mu kana itama ta kwanta, tana kallon fuskokinmu har itama bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari tun safiya na fara shiri amman kafin na fito daga wanka har driver ya iso don haka da na fito a gaggauce na shirya gudun kada na ɓata mishi lokaci kwata_kwata ban gamu da Zayyad ba.
Saida na gama shirina tsaff duka mutanen gidan suka fito zasu min rakiya amman babu shi, dukda kuwa nasan ba iya fitowa yakeyi ko wani lokaci ba amman ya kamata yazo muyi bankwana don bamu san ranar sake haÉ—uwa ba.
Daurewa nayi nayi ta maza na juya wurin baba sannan nace
"Bari na duba jikin mara lafiyan namu baba saboda na samu abin yiwa su aunty amarya albishir idan naje gida, naga tun jiya ma bai leqo waje ba"
Murmushi yayi yace "A'a hajiyata kun daiyi ta saɓani ne dashi amman ya fito, har hira muka taɓa a daren jiya da kukayi barci kuka barni, saidai bani tunanin ya tashi daga barci yanzu, saboda bai daɗe da kwanciya ba"
"Muje kawai tunda bai farka ba kada mu bari rana tayi miki a hanya" cewar matar ya Aminu.
Gyada kai nayi cikin sanyin jiki, ba dan naso ba na fara jan ƙafana zan nufi hanyar fita waje baba ya dakatar dani.
"Ko yana barcin taje ta ganshi dai, kinga hankali sai yafi kwanciya"
Wallahi ji nayi kaman na ruga da gudu na shiga É—akin, amman haka na cije na taka a hankali na shiga É—akin da yake.
A saman gadon shi na hango shi kwance ya bama ƙofa baya sai numfashin sa dake fita a hankali wanda sauƙa da tashin hannun shi dake kan ƙirjin shi ya nuna hakan.
Ƙarasawa kusa nayi na durƙusa a gaban gadon na ƙura ma gashin kanshi ido na tsawon sakwanni 10 kafin a hankali na tashi na zaga ta ɗaya ɓarin ina leƙa fuskar shi.
"Allah ya É—aga kafaÉ—un ka hamma zayd, i will wait for you to come and fight for our love, nayi maka alqawarin duk hukuncin da ka yanke zan baka goyon bayana and i will stay by your side and support you, I LOVE YOU"
Da ace a fili nayi magana nasan babu abinda zai hana shi farkawa saboda na fahimci motsina kaɗai ya dame shi, ni kuwa ba zanso farkawan shi a wannan gaɓan ba don bani son tafiya cikin baƙin ciki.
Addu'a nayi na tofa mishi sannan na sulale na fita daga É—akin.
A waje na samu su baba suna jira na a inda na barsu, daga nan muka É—unguma sukayi min rakiya har jikin mota, na shiga suna kwarara min addu'o'i muka É—auki hanya.
*********
Riƙe baki nafi'u yayi cikin tsananin mamaki yana kallon Sulaiman, shikuwa yayi kutun_kutun ya haɗe rai kada ma yayi tunanin ko yana da niyyan fasa abinda yayi niyya ne.
"Amman wallahi bakayi ma kanka adalci ba babban yaya,.....bakayi ma Saudat adalci ba hakama Zayyad.
Ta yaya za'ayi ka shiga ma yarinyar nan ta sama bayan kasan ba kai take so ba?"
"Kunyi magana da ita É—inne tace maka bata sona?" Ya tambaya cikin tuhuma tare da daÉ—a tsuke fuska yana tura ma Nafi'u mummunan kallo.
"Allah ya huci ranka yaya, bani na kar zomon ba rataya aka bani.
Amman ka sani ba sai an faÉ—a ba, Saudat Zayyad take so"
Kallon shi sama da ƙasa yayi a yatsine sannan yace "na fahimci yanzu kuma taya shi yaƙi kakeyi, ka zaɓi half brothern ka akan wanda kuka fito ciki ɗaya"
"It's not the issue of him being my half brother and you being my complete brother or whatsoever, dukkannin ku Æ´an uwana ne kuma abinda kake shirin yi ba daidai bane that's my point! nima fa kake yi a kan niman É—an uwanka, haba dan Allah!"
Ya buɗe baki zaiyi magana wayar shi ya ɗau ruri, ganin sunan hajiya yasa babu ɓata lokaci ya ɗauka.
Magana sukayi wanda bai wuce minti 1 ba yace mata yana zuwa sannan ya katse kiran.
Miƙewa yayi yana gyara zaman hulan kanshi yace
"Inaga ka manta wani abu ne amman bari na tuna maka, matar da kake aure a yanzu ba a son ranta ta aureka ba, tana da wani masoyin wanda yake sonta take sonshi amman kayi amfani da iko da dukiya ka shiga mata ta wurin iyayenta ka raba su,
To nima irin naka zanyi da abubuwan da kayi amfani nima zan raba tsakanin saudat da Zayyad"
Zuwa yanzu jikin Nafi'u ya fara sanyi da kalaman Sulaiman, ya rasa yaushe halayyan shi ya dawo haka, mutumin da yake maida damuwan wasu damuwan shi yanzu shine yake shirin saka masoyin shi a damuwa,
A sanyaye yace
"Babban yaya he is your brother, case É—ina da naka ba iri É—aya bane, Zayyad is your blood!"
"Blood my foot!!! Shi É—an uwan nawa ma ai namiji ne, ya gwada mazantaka mana!
Anyway bari na tafi kada na saka mahaifiyata jira.
Kuma duk abinda zai faru ba zan janye ba, amman shi rabin ran naka zai iya shiga takara idan yaga dama sai muga ni dashi wa zaiyi nasara nidai na riga na fara jefa tawa ƙuri'ar"
**********
"Sulaiman haka aka ce maka ake aure a yanzu ba zaka shawarci yarinya kaji ko tana son ka ko bata son ka ba kawai zaka tura a nema maka auren ta?"
Fuskar nan dai a haɗe kaman ko yaushe ko uwar tashi ma ba sararawa, cikin maganar shi da yafi kama da na umarni yace
"Hajiya a gani na hakan shine dai_dai saboda wannan yarinyar bata yi hankalin da har za'a nemi yardan ta ba kafin a yanke hukunci a kanta, ni naji ina son auren ta zan iya zama da ita saboda tana da nutsuwa sosai ba zan samu matsala wurin shawo kanta ba"
"Naji kaman yanda kace `Saudat batayi hankalin da za'a nemi yardarta kafin a nemi aurenta ba, nima bani da hankalin da za'a shawarce ni ne? Ko har kayi girman da baka buƙatan concern ɗina a cikin al'amarin rayuwarka?"
"Haba hajiya, kada kice haka dan Allah!"