← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 73

Sashe 22

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune muke da Hajiya a bedroom É—inta ta tasa ni a gaba hannun ta É—auke da kwalin magani ni kuma nawa da takardan tayi na karanto sayi iffet (side effect) dake jikin takardan taji saboda glasses É—inta bayi kusa kuma bata son fara amfani da magani bata san illolin shi ba dukda kuwa doctor ne yayi prescribing,

Ni kuwa sai zufa nake haɗawa na rasa ta ina zan faro, shiyasa nifa ko karambanin turanci bani son yi a gidan nan........🤦🏻‍♀️

#vote
#share
#comment

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

*Mrs Naseer, mrs abdulwahab, mrs S hapsy, mrs usman, mrs bash, and all other MRS's😂 wannan shafin taku ce tare da*
*Ummu hafsat & Hussaina mai jama'a*
Inayin ku sosai dearies, thanks for the love ❤️💙

18🧝🏻‍♀️
Nafi 5 minutes riƙe da takardan na ƙura mishi idanu kafin da ƙyar na haɗa letters ɗin na farko cikin rawar murya nace
"He'a_da_ca_he, (headache)"

Saida nayi shiru tare da jan dogon numfashi na furzar sannan naci gaba da karantowa,
"ji_na'echa_o_masti'a(gynaecomastia) di_arrrr_he'a (diarrhea)
To dai na ƙarshen yayi min kama da nonses (nausea)"

Da ƙarfin guiwana na ɗago bayan na gama karantawa sai ji nayi an kifa min ranƙwashi sau biyu a jere zafin su har ƙwaƙwalwa na, na dago naga wannan zazzaɓin, babban yaya tsaye a kaina yanayin fuskar shi kaɗai ya isa ya nuna maka ɓacin ranshi ni ban ma san lokacin da ya shigo ba dan banji sallamar shi ba,

Hajiya kam, al'ajabi, mamaki, firgici da takaici ne suka hana ta magana, she can't believe mai shekaru irin nawa Æ´ar birni wanda kuma tana da tabbacin ina zuwa makaranta amman ban iya karatu ba,

"Meye wannan kike yi? Baki da hankali ne ko kuma ance miki ilimi abun wasa ne ko kuma ita É—in sa'ar wasan ki ne da zaki saka ta a gaba kina mata wannan shirmen?"

Kasa kallon sulaiman nayi na sunkuyar da kaina hawaye na taruwa a idanuwa na,
"Baki ji ina miki magana ne da ba zaki amsa ni ba? Do you think it's funny?"

"Haba babana kabi mata a hankali mana, meye na fushi a nan ta yuyu bata iya karatun bane, a wani class kike Saudat?" Ta tambaya tana kallo na,

Hawayen da suka gama taruwa min ne suka samu daman ɗigowa a kan hannu na da na ƙudundune shi a tsakanin cinyoyi na, kusan duk haɗuwa na da Sulaiman sai ya saka ni kuka, ina ƙoƙari sosai wajen ganin na kai zuciyata nesa kada na tsane shi amman abu na niman faskara,

Cikin tsawa ya sake tambaya ta sai a sannan na basu amsa da "primary 4"

Zaro idanu yayi cike da mamaki yace "mene? Babba dake kina primary 4!!? What's your problem? ke wace irin daƙiƙiya ce wanda bata gane karatu as big as you are amman ace karanta simple abu baki iya ba?"

Ban san dalili ba amman abu kaɗan yana sosa min zuciya sosai, maganar da ya faɗa min ba ƙaramin taɓa min zuciya yayi ba na saka tafin hannuna na rufe fuska na hawayen dake ambaliya a idanu na suka jiƙa su,

"A wani dalili yasa har yanzu kike primary 4 kuma a wani makaranta kik.."

"Tashi ka fita a É—akin nan Sulaiman"

Yaya zaka saka yarinya a gaba kana tozarta ta? Haka aka ce maka ake yi?"

Tashi yayi ranshi a bace wai yau shine da girman shi za'a yi wa faÉ—a saboda wata har a kore shi a wuri dan yayi scolding É—inta,

Cike da taƙama ya nufi hanyar fita ina jin mummunan kallon da yake bina dashi a jiki na saida yazo daidai fita ɗakin sannan yace "stupid girl" ya fice, ban san lokacin da na fashe da kuka mai sauti ba shima yayi mun babban zagin nan,

Lokaci ɗaya naji tsanar shi ya dabaibaye zuciya ta, wani zafi nake ji a raina wanda banji wannan  zafin ba lokacin da sitipid yayi min irin wannan zagin,

a rayuwa ta bayan yarima da dangin shi ban sake tsanan wani ba kaman sulaiman, ban taɓa ganin mutum mai baƙar zuciya irin shi ba kuma ƙarara yake nuna min tsana da ƙyashi tunda ya tsane ni nima na tsane shi,

Buge min baki Hajiya tayi don kuka na ya fara damun ta, na toshe bakin da hannu na ina daÉ—a matsar kwalla, sai kuma ta janyo ni jikinta ta kwantar da kaina a saman cinyar ta tana lallashi na,

"Kiyi haƙuri kiyi shiru Saudat kinga na kora shi insha Allah ba zai sake takura ki ba kinji?"

Gyaɗa kaina nayi ina daɗa cusuwa a jikin ta, ko dan darajan Hajiya bai kamata na tsani ɗanta ba amman ba abin da zuciyata ya zaɓa min ba kenan

****
Mtsww shi wallahi duk tunanin shi yarinyar nan ta ko ina a haÉ—e take, kaman yanda take da kyan fuska haka take da ilimi da kuma wayewa amman alamu sun nuna yayi kuskuren fahimta,

Yaushe wahala zai ƙare mishi ne a kan mace? Yaushe ƙwaƙwalwar shi zata daina ɗaukan caji saboda sakarcin mata? Wurin Sadiya ba sauƙi wurin saudat ma bai huta ba? When will he get the PERFECT wife? Ya tambayi kanshi,

(but is he a perfect husband to deserve a perfect wife???)

ÆŠaga wayan shi yayi ya kira wani number bugu É—aya aka É—auka, bai tsaya amsa gaisuwan mutumin ba yace

"Ina son ka samo min admission na best school dake garin yola na baka zuwa gobe da safe" kitt ya katse wayan, sannan ya zuba a kujerar tare da cire hulan kanshi yana huci, dole ya canza rayuwar Saudat gaba É—aya don ba zai iya zama da bagidajiya ba,

**********
Me ya kawo ta nan wurin a cikin daren nan? Ya tambayi kanshi lokacin da ya hango ni zaune a kan farin ceramic bench da kullum muke zama a kanshi cikin garden,

Juyawa yayi ya kalli Ruma ganin yanda na kifa kaina ina kuka, yace "sis mai ya same ta ne?"

"Wallahi ban sani ba ya Zayd shiyasa ma kaga na kira ka na tambaye ta yafi sau a ƙirga taƙi cemun komai, tun da aka idar da asham ta fito daga ɗakin hajiya take kuka"

Cikin nutsuwa ya ƙaraso wurin wanda ya wadatu da farin haske ya zauna a kujeran dake kallon nawa tare da ƙura min ido, zafin sheshsheqar kukana har cikin zuciyar shi yake jin yana ƙona shi,

Handkerchief ya zaro daga aljihun shi ya miƙa min sannan ya kira suna na cikin wani murya mai taushi,
Bansan Zayyad yazo wurin ba hakan ya saka ni É—agowa da sauri na zuba mishi rinannun idanuwa na ga hawayen dake faman sintiri saman fuska na,

Da yana da dama da zai haramta min zubar da hawaye gaba É—aya don bai dace dani ba, a yanzu haka ji yake yi kaman ya rungume ni tsam a jikin sa don bani damar fitar da ciwon dake zuciya ta,

da ace na halatta mishi da zaiyi min irin rarrashin da zai mantar dani duk wani sauran damuwa na, yana da burin dasa farinciki mai É—orewa a cikin rayuwa ta ba zai so wani abu ya ruguza wannan burin ba,

Karban handkerchief ɗin nayi na share hawaye na sannan na miƙa mishi amman bai karɓa ba cikin nutsuwa ya sake kiran sunana a karo na biyu,

" zaki iya faÉ—amin abin da ya same ki har yayi sanadin zubar hawayen ki?"

"Babu komai ya Zayd"

"Babu komai kike kuka? Ko an taɓa kuka babu dalili?

Ƙura ma jikin bench ɗin da yake zaune idanu nayi don ba zan iya jure kallon cikin idanun shi ba,

"Ya Zayyad da gaske ni daƙiƙiya ce?"

Waro idanun shi yayi tare da faÉ—in "what?! Who the h**l told you that?"

"Ko da yake ma ai gaskiya ce tunda bani gane karatun boko ban iya turanci ba, amman ina da haddan alƙur'ani na san abubuwa da yawa game da addini na kuma nayi karatu mai zurfi a kansu saidai na lura a wurin mutanen birni wanda baiyi karatun boko ba shine daƙiƙi"

"Could you stop beating around the bush and tell me waye ya faÉ—a miki wannan kalman?"

Auu ashe É—azun ma tambaya na wanda ya faÉ—amun yayi da turanci?

"Zaki faɗa min ne ko sai ranki ya ɓaci?" Ya faɗa cikin ɗan ɗaga murya jin nayi shiru "Wa ya bada daman wani ko wata ta faɗa miki wannan mummunan kalman a cikin gidan nan, a kan wani dalili?

ta yaya ma za'ayi na faɗa ma sitifid abin da yayan shi yayi min? Wani tunani shi ɗin zaiyi a kaina? Ko dama ace zai yarda dani bai kamata daga zuwa na cikin gidan in kawo saɓani a tsakanin su ba dan na tabbata yanda na hango ɓacin rai a idon sa ba zai bar wanda ya ɓata min rai haka nan ba,

"Ni na haƙura na yafe, ka barshi kawai ba kowa"

"To ni ban haƙura ba, ban kuma yafe ba duk wanda ya zage ki ko waye shi a gidan nan tabbas sai ya fiskanci hukunci"

**********
A firgice ya fito daga bedroom ɗin ganin bayi ciki, cikkn tashin hankali yaje yana buga ƙofar aunty Amarya bugun da ya saka ta yanke Sallah babu shiri ta fito a kiɗime don idan taji irin haka tabbas Zayyad ne,

Fitowan ta ke da wuya taci karo da sulaiman tsaye sai zazzare idanu yake yana tambayan ta inda Zayyad yake sai dafe ƙirji tayi tana salati cikin zuciyan ta tana maimata 'an kuma, Allah yasa ba sake shiga cikin wani matsalan yayi ba, kuma Allah ya kare mata shi a duk inda yake'

Ganin haka yasa ya fita da gudu yana kwala masa kira har ta part É—in Hajiya sai da ya duba amma wayam babu shi babu labarin shi, haka ya koma bakin gate don sake tabbatar da bai fita ba duk da an faÉ—a mishi hakan kafin ya shigo,

  *****
"Ba zaki faÉ—a min ba ko?" Ya sake tambaya ta,
Chapter 22 · 0% Book details