← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 73

Sashe 70

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman yanda na tsammaci wurin zai kasance.... Toh abinda idanuna suke gani mun a yanzu yafi ƙarfin tunani na ma ballantana tsammani na, Maldives yana ɗaya daga cikin jerin farko na ƙasashen duniya da suke da yawan beaches don kuɗin shigan su ma yafi yawa ta wurin saboda yawan baƙi da masu yawon ɓude idanu dake zuwa wurin dan shaƙatawa a beaches ɗin da babu kamar su,
Mata kawai nake gani rututu da bikinis suna yawo kusan tsirara kaman wasu tumaki maza kuma daga su sai shorts, saboda yanayin shigan mu har muka zamo musu abin kallo muna wucewa ana nuna mu da yatsa, don ni flawless gown ne peach color a jikina sai nayi rolling da gyale kaina da farin dankwali, Zayyad kuma normal sweaters ne a jikinshi sai nurse din da aka haÉ—o mu da ita kuma uniform din aikinta ne a jikinta.
Hannu na a cikin nashi muke tafiya da kafafunmu kafin muje inda zamu shiga abun hawa na gaba.
"Babylovee" na kira shi tare da ja na tsaya,
Juyowa yayi yana kallon yanda na haÉ—e rai, yasan wannan fushin akan menene maganar É—aya ne bayi wuce kishi, shi da zai gwada mata kalan nashi kishin nata wasan yara ne.
"Yaya kuma akayi boÉ—É—i?"

"Me yasa kake waigawa kana kallon matan can" na faÉ—a tare da turo baki ina gwada su da yatsa.

Numfashi ya furzar sannan ya É—an juya ya kalli nurse dake biye damu daga ganinta a kugun takure take, na farko tun kafin ta fara niman abinda take so ta rasa shi gashi boÉ—É—i is pissing her off.
"Ni banga matan da kike faɗa ba, banda gine_gine babu abinda nake gani a nan, Please stop being such a baby kina ɓata mana lokaci fa lokacin la'asar ta kusa kurewa"

"Ohh u are politely saying I'm pissing you off? Shikkenan nima bari naje cikin su na zauna maybe a cikin gine-ginen da kake gani zaka gano mai kama dani, I'm off" na faɗa tare da ƙwace hannuna daga cikin nashi na nufi bakin beach ɗin ga idon wasu daga cikin mutanen curr a kanmu suna kallon draman ƙauyawan couples anayi ana sipping cocktail haka na matse nayi kaman bani ganinsu.

Da gudu ya biyo ni a baya ya sunkume ni ya raɓa a kafaɗa kaman wata kaya, sai wuntsila ƙafa nakeyi cikin salon niman magana amman yaƙi kulani, tafiya kawai mukeyi muka je muka shiga wani mota da zai tafi damu a kan ƙasan beach ɗin ba tare da matsala ba ya kaimu reserved area inda mutane da yawa suke siyan gidajen a wurin suna zama.

Gidajen wurin duk kalan su daya ginin anyi da katako a sama da matakalan da ze kaika ciki number ne kawai ya banbanta su sannan ko wanne a kewaye yake.
Daidai ƙofar namu aka ajiye mu tare da nurse ɗin ta taya unpacking muka hallara ciki,
Roses ne tun daga bakin ƙofar madaidaicin parlourn ko ina a rufe wurin yayi duhu sai haske da ƙamshin scented candles da Zayyad yasa ayi arranging, wurin yayi matuƙar ɗaukan hankali na it's so romantic.

Saida ya bari nurse ta shige cikin ɗaya separate room ɗin kafin yazo ta baya na ya saƙalo kanshi ta gefen wuya na yana jin sautin dariya na dake fita a hankali saboda farin ciki,
I hope you liked it, and zaki bada dama ya zamo wurin da zamu ci amarcin mu, just azzume that honeymoon mukazo ba jinya ba, abinda nake so kenan..............🧚🏼‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

52🧝🏻‍♀️ (GRAND FINALE)
"You are not serious" na faɗa cikin fitar da sautin dariya tare da juyawa zan bar wurin, da azama Zayyad ya riƙo waist ɗina ya dawo dani jikinshi yana bina da wani irin kallo mai nuna shauƙi da tsaftacacciyar ƙauna, " then let me show you how unserious I am"
saurin dakatar dashi nayi ganin yana matso da fiskan shi kusa da nawa nace "babylove bamuyi sallan la'asar ba fah! And it's 5 already"

Furzar da numfashi yayi yace "zamu haÉ—u ai bayan sallan la'asar É—in, ina nan tare dake babu inda zanje and our honeymoon is starting today!" Yaja hannu na muka shige bedroom É—inshi wanda ke É—auke da bathroom a ciki mukayi alwala sannan mukayi sallah a tare sai ya sake fita parlourn saboda alluran da nurse zatayi mishi a lokacin.

Wurin akwai sanyi kaÉ—an amman ganin ruwan zafi available a heater yasa banji kyuyan wanka ba, a gaggauce nayi na fito har lokacin Zayyad bai dawo ciki ba.
Jakan kayana wanda su Ruma suka haɗa mana na buɗe ina duba kayan da zan saka, yawanci gowns ne irin na jikina sai atamfofi da laces suma basu fi a ƙirga ba sai jibgin ƙananun kaya.

Hannu na nakai kan wata ƴar ficikar riga armless pink color mai shegen kyau amman ina mamakin yanda za'ayi wannan ɗan abun ya shiga jikin mutum mai girma kama na, sai da na ɗaga naga saman nada faɗi tsayi ne kawai bata dashi sai wani da zaka ƙulle rigan ta ƙasa ya zamo yana showing cibiyan ka.

Saka rigan nayi a jikina na ƙarasa gaban madubi ina kallon yanda ya amshi fatata kaman don ni akayi shi, haka kawai naji ina son in zauna dashi a jikina, na ɗauko leggings golden brown kalan adon dake gaban rigan na saka.
"Woww" shine abinda na furta lokacin da nake kallon kaina sama da ƙasa a mirror, Black scarf nayi ɗauri mai kyau dashi saboda almuru gudun aljanu.
Turare kawai na bulbula na saka takalmi da confidence ɗina na isa bakin ƙofar da zai sada mu da parlour sai kuma naji ruwan ciki na yana kaɗawa na gagara fita.
Zayyad mijina ne, ya kamata ina ado mai ɗaukan hankali don na burge shi amman kuma ban saba ba, ban taɓa yi ba koda a gidan aurena na farko sai inajin wani iri a jiki na.

Sake tattaro dukkan ƙwarin guiwa na nayi na fita parlourn a tunanina zan iya samun su har yanzu a wurin amman shiru babu labarin kowanne daga cikinsu, leƙa ɗakin nurse ɗin nayi itama bata nan sai kawai na koma na ɗauki medicated glasses ɗina da pencil da paper na fita ta ƙofar baya wurinda ke a kewaye babu wani daga waje da zai iya hango wanda ke cikin wurin.

Takalman ƙafana na cire na zauna ɗan nesa da bakin ruwan ina zanen waves, iskan wurin mai ɗan ƙarfi haɗi da niima yana kaɗani har kusan 30 minutes Zayyad bai dawo ba, komawa ciki nayi na ɗauki wayana na kira shi saiga wayan shi na ringing a kujeran parlour hankali na ya kai maƙura wurin tashi, na Farko bayi da lafiya gashi bai faɗa min inda zaije ba kuma magriba ta gabato har yanzu bai dawo ba, ji nayi tsoron gidan ya kama ni gashi yunwa nake ji annan bani da nutsuwan cin abinci haka na koma bakin ruwan naci gaba da zama.

Daga nesa na hangota zaune ta haÉ—a kai da guiwa da É—an ficilar riganta da yabar rabin bayanta a buÉ—e,
Ƙarasawa wurin yayi ya mata sallama saboda bata san da zuwan shi ba kada ta firgita

Ban amsa sallaman ba sai miƙewa nayi a dame ina dube_dube a jikin shi kaman mai son gano wani abu.
"Babylove where have you been? Hankali na ya tashi sosai, da ka sanar dani katin ka fita Pleease! I was really worried"

Ƙaramin murmushi yayi idanun shi na kan ciki na da yake buɗe ya matso daff dani sannan yayi hugging dina ina jin hannunshi a kan bare skin ɗina.
"I'm sorry babes looacin da na fita kina wanka and i forget to take my phone, naje na sanar da management plan din zaman mu ne saboda daily service da kuma ordern abinci. That's all, I'm safe"

GyaÉ—a kai nayi nace "and what about the nurse?"

Wani shaqiyin dariya yayi yace "daman kina tsammanin zan barta ta zauna tare da mu ne? I send her off nazo honeymoon ba zanbari wata aba can tazo ta tare min shan iska ba, i want us to be alone, just me and you"

Jinjina kai nayi na tattari tarkace na "mu tafi ko" na faÉ—a lokacin da na ratsa zan wuce ta gaban shi,
"Kin iya ruwa?" Ya faɗa tare da riƙo hannuna.

"No! Ina da aquaphobia tun ina yarinta, ko a rigan mu ma bani iya shiga rafi,

"Come here" ya faɗa tare da zubar da kayan hannu na, matsawa nayi kusa dashi ya riƙe hannuna duka biyu sannan ya fara jana kusa da ruwan, wani gauron numfashi naja lokacin da naji ƙafafuna sun fara luntsuma cikin ruwa, a take naji jiri ya fara ɗiba na,
"Hamma Zayd bazan iya ba, I'm really scared"

"Tsoron me zakiji bayan ina tare dake? Babu abinda zai same ki as long as I'm here"
Ya faɗa daidai lokacin da ruwan ya haura saman ciki na har yana ɗaga rigan jikina, tsantsi naji ya ɗibe ni da azama na wuntsila jikinshi sai gamu fanjam mun faɗa a cikin ruwa ni a saman shi, saurin miƙewa nayi tare da shiɗewa numfashi na yana niman ɗaukewa, tashi yayi ya rungumo ni a jikin shi yana shafa gashin kaina a hankali ga ɗankwali na da tuntuni ya bi ruwa.
"Are You okay?" Girgiza kai nayi ina daɗa ruƙunƙumeshi a yanzu bani da burin da ya wuce na fita daga cikin ruwan nan ko zan samu nutsuwa a ruhina,

"Let's do it again you will be ok"
Saurin girgiza kai nayi, idan ba wai a wani ɓangare na zuciyan zayyad akwai burin kashe ni bane to halan ƙure muguntan shi yake son yi a kaina,

"A'a hamma Zayd bazan iya ba, mu fita Pleease"
Chapter 70 · 0% Book details