← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 73

Sashe 59

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

46🧝🏻‍♀️
Girgiza kai baba yayi da murmushi a kan fuskar shi, ba wanda yake nuna yana farinciki ba saidai mai nuna alama ta yana ganin mutuncin su dady amman ko kusa bai taɓa tsammanin mutane masu dattako irinsu zasu yi irin wannan tunanin har suzo su same shi a kan wannan maganar ba.
Haka iyaye suka zamo akan son zuciyan Æ´aÆ´ansu? Ba kunya ba tsoron Allah Kaman ba hausa Fulani ba!.

"Alhaji kiyi haƙuri amman gashkiya bazan amshi buƙatar ku ba badan wai na raina ku ko baku kai ku nemi wani abu a wuri na ba, amman Shaudatu yaro ne mai raunin gashke, a zahirin gaskiya ba zan iya washa da abinda ya shafi farincikin shi ba, don Allah ya bani irin wannan daman daga farko nayi wasa dashi wanda har hakan yayi sanadin zuwanta Wurin ku amman wancan ƙaddara ce, shaidai idan na kushkure na jawo abinda zai sake kawo mishi tsangwama da kyara a ƙarkarar nan to zai zamo sakaci"

"Na fahimce ka malam arɗo nima Saudat kamar ƴa take a wuri na ba zanso ganinta ta shiga wani hali saboda wani na ƙyale ba ballantana kuma a sanadiyya na, amman dan Allah ka ƙara duba lamarin muma ba yana tafiya mana a yanda mukeso bane, ba zamu saka saudat yin Abinda bata so dole ba shiyasa suma na faɗa musu ra'ayinta za'a bi duk wanda tace tana so shi za'a bata sai ɗaya ya janye"

Ƙara faɗaɗa murmushin shi malam arɗo yayi ya juya ya kalli khamis da yayi kicin_kicin ya haɗe rai don fin ƙarfi suka gwada mishi ƙarara amman da kafin azo nan duk ya gama cin ubansu an huta.

"Lalle kunyi min alkhairai da dama kuma zan kashance mai godiya a gareku har ƙarshen rayuwata, amman mutanen wannan ƙauyen bashu raina abinda zai jawo mutum ya zamo abun la'anta a wurin shu, shu gallaza ma rayuwar shi, boɗɗi shi shaida ne a kan hakan domin har rayuwan shi shuka sho ɗauka, bazan bari hakan ya shake faruwa da shi ba dan Allah kuyi haƙuri ku yafe min, amman wannan zancen a barta kawai"

With so much excitement khamis yayi tsugul yace "shikkenan ba za'a basu auren ba kenan? Dukkan su?"

"A'a khamishu, idan nayi haka ko ma kaina bayi adalci ba ballantana ma shaudatu ko su maneman nata, saidai zanso daƴa a cikin shu ta hakura tun yanzu, ko ita babban ta haƙura ta janye ko kuma ƙaramin ta haƙura".

Ya maida hankalin shi wurin dady sannan yaci gaba da cewa
"Alhaji da ace ba jini ɗaya suke ba koda sunfi biyu yawa zan basu duka ikon neman ta saboda bai saɓawa addini ba, amman yaya da ƙani ya saɓa ma al'adun mu, ban taɓa jin yanda akayi irin haka ba dan Allah kayi haƙuri kada a fara kafa tarihi damu, ni nayi alƙawarin wanda shaudatu ya gwada yana so a cikin su zan bashi ita ba tare da wani damuwa ba insha Allah"

Sam hakan baiyi ma khamis daɗi ba don har cikin zuciyansa baiso a bawa ko ɗaya daga cikin su Saudat ba don basu cancanta ba, amman tunda bashi keda hurumin nima mata miji ba zai bita da addu'a kawai yanzu dai ya riga da ya sauƙe nauyin amanar dake kanshi.

"In Allah ya yarda zanje na zaunar dasu mu yanke hukunci a tsakanin mu, nima na aminta da wannan shawaran da ka yanke don future'n Saudat ba abu ne da za'ayi wasa dashi ba, muna godiya da karamci da kuma dattako da kake nuna mana a ko wani lokaci, insha Allah zamu kama hanya yanzu kada dare yayi mana a hanya"

Tashi baba yayi sukayi sallama cikin girmamawa, kafin su fita saida ya kira su ya Aminu da jaÉ—e sukayi musu rakiya har jikin mota saida suka tafi kafin suka koma ciki.

**********
Fitowan Zayyad kenan daga wanka yaci karo da Sulthana zaune a bakin gadon shi wanda yayi a sanadiyyar zazzaɓin da ya sauƙa mishi da yamman nan tsananin tsoron da yakeyi na abinda zaije ya dawo daga wurin baban Saudat.
Saurin komawa ciki yayi ya datse ƙofar saboda towel ƙarami ne kawai ɗaure a ƙugun sa sauran suffa na jikinsa duk a bayyane, daga bayan ƙofar cikin ɗaga murya yanda zata jishi yace.

"What are you doing inside my room Sulthana?"

Lumshe idanunta tayi da jin tambayar shi don ita ta riga da taga abinda ya birgeta ya kore mata duk wani ɓacin rai da tazo dashi, 'Zayyad has a very wonderful figure' ta ayyana a ranta, yana daga cikin abinda yasa kullum take jin yana daɗa shiga ranta saboda shi ɗin mai kyau ne, tana son namiji mai broad chest and her Zayyad have it too.

Leƙowa yayi da yaji shiru a tunanin shi ko ta fita ne amman ya hango ta zaune a wurinda ya barta wannan karon idanunta a rufe,
"Ba magana nake miki ba kikayi min banza? I said what brought you to my room?"

BuÉ—e idanunta tayi ta É—an haÉ—e rai sannan tace
"Ka fito Ya zayd magana nazo muyi"

"Ok to fita parlourn aunty ki jira ni bari na shirya sai na fito muyi maganar"

Share shi tayi kaman bata ji abinda yace ba ta jawo wayanta taci gaba da dannawa,
Tsaki yaja da ganin haka ya koma cikin bathroom ɗin ya ɗauko T-shirt da ya cire a laundry basket ya mayar da ƙyar ya iya fitowa gabanta a hakan don tunda yake bai taɓa tsayawa a haka gaban wata mace ba, kuma bazai iya yayi wanka ya sake maida kaya mai datti ba.

Dakewa yayi ya tsaya a gaban gadon ɗan nesa da inda take zaune yana mamakin ganinta da yayi yau da hijab har ƙasa, bai sani ba ko izala ta shiga amman da yayi mata murna tunda dai ya sakata nutsuwa.

"Yaya akayi?" Ya tambaya a takaice.

Kashe wayan tayi ta ajiye sannan ta tashi tsaye don ta daidaita tsayin su dukda kuwa ya mata tsawon da har sai ta É—aga kanta sama take kallon fuskar shi.

"I heard that you are preparing to get married to that Saudat girl"

"Yess and so?"

Shagwaɓe fuska tayi kaman zatayi kuka tace "hakama zaka ce, ni kuma fah? Bayan duk alƙawuran da kamin lokaci ɗaya ka zubar dani a kwandon shara without any warning did i really deserve that?"

Ajiyan zuciya ya sauƙe ganin idanunta ya tara ƙolla gashi ya tsani ganin kukan mace haushi yake bashi, cikin lallami yace
"Sulthana! I'm sorry for giving you false hope, da gaske ne daga farko naso auren ki amman daga baya sai na fahimci you and I are not meant for each other, son da nake miki na ƴanuwantaka ne da kuma ɗan shaƙuwa da muka samu a tsakanin mu, Nothing more"

"Seriously? Is it because of Saudat? Me tayi muku ne that you and babban yaya are going crazy over her? Me tayi maka....me ta baka da ka liƙe mata ka manta da wanda tayi zaman jiranka tsawon shekaru har ka samu lafiya? Meye kake buƙata a wurin mace da bani dashi? Ka faɗamin nima zan baka" ta ƙarasa tare da zare hijabin jikinta tayi wurgi dashi.

Filluwa baya Zayyad yayi kaman wanda aka hankaɗa shi har towel ɗin jikin shi na niman faɗuwa saboda mugun ganin da yayi, da sauri ya tattaro shi ya sake gyara mishi ƙulli tare da kawar da kanshi ƙirjin shi na bugun hamsin_hamsin.
"Woooh!!! Meye haka Sulthana? Are you crazy?"

Sake satan kallonta yayi still tana tsaye da bikini yayi saurin É—auke kanshi yana salati sai haki yake kaman wanda yayi tsere don abin yazo masa a bazata, this is the first time da yake kallon mace a haka, that too ba a TV ba zahiril ayni a gaban shi
"Get out of...my room"
Ya faɗa cikin fisgar maganan, amman a maimakon ta fitan kaman yanda ya umarta sai ta fara takowa zuwa inda yake zaune daɓas a ƙasa.

Durƙusawa tayi tana faman karkaɗa jikinta yanda tasan zata daɗa ɗaga mishi hankali, shikuwa sai ƙoƙarin kawar da idanunshi yayi har ta iso shi itama ta tsunguna tare da ɗago hannun shi ta ɗaura a saman ƙirjinta, zatayi magana sai sauƙan mari taji a kumatun ta, kafin tayi wani yunƙuri ya miƙe cikin zafin nama ya fara kutubol da ita a tsakar ɗakin don baiyi zaton ƙasurgumar mahaukaciya bace Sulthana sai yau.
Kaman wanda aljanun sa suka motsa haka yake wujijjigata a tsakar É—akin tun tana iya daurewa har ta fara zunduma ihu.

Jin ihunta yasa Sulaiman da ya nufo ɗakin saurin ƙarasowa ya ɓuɗe ƙofar yayinda yaci karo da Sulthana na gudundule a ƙasa bakinta da goshin ta a fashe Zayyad kuwa sai zuba mata masga yake yi.

Tana ganinshi ta jawo hijab ɗinta cike da munafurci ta fara kuka tana ƙudundune jikinta tare da fara ja da baya yanda Sulaiman ɗin zaiyi tunanin ko wani abun daban Zayyad yayi mata,

wani wawan tsawa ya daka mata da saida ya saka numfashin ta tsayawa cakk na wucin gadi
"Shut your filthy mouth up and get out of this room kafin na baki mamaki Sulthana!!!"

Jikinta na tsuma ta zumbula hijabin kafin ta tashi da sauri da jan ƙafa zata fita, saida tazo wucewa ta gaban shi ya bita da wani disgusting look tare da faɗin
"I will deal with you later"
Hakan ya ƙara kaɗa ruwan cikinta taji ta tsure, duk rashin hankalinta bata wasa da fushin babban yaya.

Bayan ta fita ya maido hankalin shi kan Zayyad da ya dafe bango yana maida numfashi duk jikin shi ya gama mutuwa kaman shi aka daka ba shi yayi duka ba, ƙaramin tsaki yaja yace
"Ka shirya ka fito muna jiran ka a parlour.
And don't waste our time abu mai muhimmanci ne"

Da faɗan haka ya wuce Zayyad ya bishi da kallo, yasan koda na minti ɗaya Sulaiman bai zarge da komai ba da yaga halin da ƙanwar matanshi take a cikin bedroom ɗinshi saboda dukda babban giɓin dake a tsakanin su Sulaiman trusted his little brother so much.
Chapter 59 · 0% Book details