← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 73

Sashe 53

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki malam arɗo ya tsaya yana kallon Sulaiman kanshi ya kasa fassara mishi abinda yake nufi, ganin mutane sun fara cika a ƙofar gidan ciki harda matan aure suna yafo mayafinsu suzo ganin kalan motoci da mutanen da akace saudat tazo dasu,

Muna zuwa shiga zayyad ya yanki jiki ya faÉ—i amman hakan bai wani dame mu ba saidai a yanzu hankalin Sulaiman ya fara tashi haka suka haÉ—u suka kinkime shi zuwa ciki,

Saida muka shiga ne akayi ma malam arɗo bayani dalla_dalla sulaiman ne ya saka aka gyara musu gidan, shidai baisan mai zaiyi ma wannan ɗan albarkan ba, yana ganin koda goyon shi yayi ba zai isa ba yayi masa alkhairori masu yawa wanda bayi da abinda zai biya shi dashi saidai yayi ta mishi addu'a, ai kuwa ya shata daga bakin kowa a gidan ni kuwa kuka nake kaman anyi mini mutuwa wani ƙima da daraja na sulaiman na daɗuwa a cikin rayina, ya gama min komai a rayuwa da ace ina da abinda zan biya shi dashi definitely zan biya shi,

Hutawa mukayi zuwa ƙarfe 10 sannan muka ɗau haraman ɗaura abinci ga komai da ake buƙata Sulaiman ya tanade shi ya jibge mana a store ɗin gidan, akace hannu da yawa maganin ....miiya cikin abinda bai wuce awanni biyu ba muka gama abincin mu kala guda biyu da wanda kowa zaici da kuma irin wanda ni da su Sulaiman muka saba dashi na yan birni har zuwa lokacin Zayyad na barci bai farka ba, daga nan nayi wanka nayi sallah aka ci abinci na ɗan zauna ƙarin hutu zuwa sallan la'asar saboda nafison sai rana tayi sanyi kafin na fita yanda zan karaɗa ko ina nayi son raina tunda a yanzu ina da goyon baya,

3:47pm
Wani motar ya ƙaraso ƙofar gidan dai_dai inda sauran motocin suke shima yayi parking, da gudu na ƙaraso na ruƙunƙume ta inajin farinciki mara misaltuwa bayan sintirin da na dinga yi a gidan su Ruma yau itama gashi tazo namu gidan kuma ina alfahari da hakan,

Tare suke da Yusrah da mahaifiyar khamis da mahaifiyar ita yusran harda Nasreen amman duk cikin su babu wanda yazo da yara dukda haka dai munyi full house,

Har zamu wuce muryan Fa'iza ya jawo attention ɗinmu, ta fito ta ɗaya ƙofar bayan tana tsaye dare da murfin motan a yatsine take binmu da kallo,
"Hey bush head!! Baku ganin mutane ne da tsiraran kafafunku kaman masilla da ba zaku kulani ba? Dukda dai ke ba laifin ki bane" ta faÉ—a tana gwada ni "kina fama da makanta ba zanga laifin ki ba idan baki gani"

_wato nana ne kawai bata zo ba! Itace kawai bata taya ni murnan dawowa na mahaifata, toh Allah ya huci zuciyarta_

Cikin farinciki muka ƙarasa muka rungumeta dukda sai ihu take wai zamu saka mata bola kasancewar fararen kaya ne a jikinta muka jasu ciki, gaisawa kaɗan aka zauna sake yi sulaiman yayi shirin tafiya zai kuma bi ya haɗa kan ƴan ƙwayan da zai kaisu rehab su tafi tare,

Unknown to us har motan police ya tattari na tafiya sun riga sun tafi su tsohon mai gari ne ake ta faman artabo dashi ya hana a ɗauki ƙanin yarima sun ɓoye shi a wani wurin da ba'a ma san ina bane,

_wannan tsoho mai ran dalma har yanzu yana raye?_🤦🏻‍♀️

*Here i comes again, na zama maman excuse gashi bani iya replying comments😣 like seriously yanzu na dawo sai a hankali a ci gaba da hakuri dani a haka dan Allah ana manage😁 saidai duk da haka ina bin sharhin ku ɗaya bayan ɗaya ina karantawa kuma yana sani farinciki matuƙa na gode na gode💃🥰*

*Ummu excuse ce😂😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

_(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

*Alhamdulillah, bayan tsawon jira gashi na sake dawowa a karo na biyu😃 ina bawa masu karatu haqurin rashin jina kwana biyu da sukayi sakamakon ƙaddara data faɗo min har yayi sanadin rasa sim card ɗina sai kuma na ɗan jinkirta dawowa saboda azumin Ramadan. Amman yanzu zamu kammala littafin nan idan Allah yaso*

43🧝🏻‍♀️
Buge hannun ta nayi ina ƙara sautin kuka na, ta yaya za'a dake ni a hana ni kuka? Ni lokacin da yarima yake cin ubana a gidan ba suna gani suke kyalewa ba? Ko a cikin su akwai wanda ta taɓa yunqurin dakatar dashi? Saidai idan ya gama cin zalina goggo ta rarrashe ni amman duk yawansun nan taron yuyuyu ne babu wanda ya taɓa wani abun azo a gani akan komai dake faruwa a cikin gidan sai yanzu ne da suka ga babu sarki sai Allah wai zasu rusuna su fara roqona gafara?
To ba za'a yi haqurin ba!!

Sake rarrafowa yadikon yarima tayi tana kuka kaman anyi ma kafiri mutuwa, ta ƙara danƙo kafana daga inda nake zaune tace
"Dan girman Allah boɗɗi kayi mana aikin gafara ka roƙi kaɗɗon nan ta rabu mana da mai gari ƙarami don ya Rashulullahi"

Fisge ƙafana nayi daga riƙon ta na ɗaura daya kan ɗaya ina kuka tana kuka sauran mutan gidan ma suna tsaye suna kallon mu suna taryo duk abubuwan da ya faru dani a baya cikin kwaƙwalen su,

Kwanakin da nayi su mafiya wahala a cikin rayuwana ana treating É—ina kaman wata dabban jeji da bata da uban gida,
Babu wanda ya damu da kuka na, babu wanda ya damu da cina ko shana, azaban da yarima ya bani ko a gidan kaso ba za'ayi min shi ba, he and his family abuses me both physically and mentally.

Zumɓur na miƙe kaman wanda aka razana sannan na dube su dukan su nace
"Yanzu dukkan ku kunyi ma kanku adalci? Bayan cusguna min da kukayi kuka maida ni abu marar ƴanci a baya, yanzu ma kuna son sake rabani da wani ɓari na farin cikin rayuwata?.
Kun manta lokacin da ake hankaÉ—o ni daga wancan É—akin.." na faÉ—a ina nuna dakin da ya kasance nawa da yarima a da.

"... lokacin da ake duka na da sanda kaman jaka, haka zan wuni a kwance a ƙofar ɗakin can cikin jini bayan goggo dakan tallafe ni da abinci ko kallon banza babu wanda wani ko wata daga cikin ku yake jifa na dashi,
Dan Allah bakuji kunyar sake kallon cikin idanuna ba!!! Bakuji kunyar roƙona alfarma ba!!" Na ƙarasa cikin daga murya.

Shiru ne ya ratsa wurin babu wanda yake da bakin ce min komai don fiye ma da abin da na faÉ—a ya faru, Ruma na ganin ba zata iya jurewa ba ta fice daga gidan gaba É—aya tana kuka don ita a zaton ta abinda ya faru dani be kai haka ba,

fa'iza ne ta karaso kusa da inda nake zaune ta daura hannun ta saman kafada na tana lallashi na, cikin tausayawa ta riko hannu na ta dunkule cikin nata tace
"Ba halinki bane Saudat ke É—in mai hakuri ce mai yafiya idan kina tuna baya rayuwar ki ta gaba ba zata yi inganci ba, learn to forgive... please.."

"Aunty fa'iza ganin dangin yarima sun wulakanta kaman yanda suka wulakanta nawa dangin shine kaɗai farinciki na, burina kenan guda ɗaya naga na kawo su ƙasa"

"Amman ba haka kuka yi da yaa Zayyad ba, ba wannan halin da mugun nufin kika gwada mishi ba, idan har kin É—auke mu da daraja ki bar abinda ya wuce ya wuce, kema zaki samu Allah ya yafe miki laifukan da kikayi na rayuwan ki harma da wanda baki sani ba"

Hmm lallai, Fa'iza datayi ɗamara da sunan zata rakoni yin faɗa itace kuma yanzu ta juye take bani haƙuri, ko dayake nima rayuwa ta bani second chance, Ya kamata nima nayi ƙoƙarin bawa mutanen dake cikin rayuwana dama ta biyu

Miƙewa nayi na karkaɗe jiki na sannan na saka bayan hannuna na share hawayen idona, a nutse nake takawa na ƙarasa gaban goggo dake zaune kanta ƙasa, kaman ba zanyi maganana ba na tsaya ina ƙare mata kallo kafin cann nace
"Goggo lami"

ÆŠagowa tayi ta amsa da "na'am saudatu"

Na gode da kulawan da kika nuna min lokacin da nake ƙarƙashin ki, kin sanyanta azaban da ɗanki da jikan ki suke gwadawa a kaina, na gode sosai, saidai ba zanyi miki alqawarin ƙanin yarima zai dawo kwanan nan ba amman nayi miki alqawarin insha Allah zan shiga gaba wajen samawa mai gari lafiyan kafarshi duk abinda ake buƙata zamuyi mishi insha Allah"

Zanin da ta yafa ta rufe kanta dashi ta jawo ta rufe idanunta a kunyace sannan ta saka kuka,

Haka mukayi shiru muna sauraron yanda take rero su cike da nadama, hawaye suna zarya a idanun ta, kafin da ƙyar aka saku aka lallasheta ta bar kukan ta ɗago tana fuskantana cikin kasashshiyar murya tace

"Duk abubuwan da suka faru sakacina ne saudatu saboda kowani mutum dake rayuwa a cikin gidan nan a ƙarƙashi na yake, da naso da na hana cuta da zalunci a tsakanin su, amman na zuba idanu nayi oho da duk abinda yake faruwa har abubuwa suka zo suka fi ƙarfin ikona.
da nasan haka zata faru da tun lokacin baya nayi wani abu a kai, da nasan haka zaki dawo da tun baya ban barki kin wulakanta ba"

Kasalallen murmushi na sake jin abinda zuciyata ke tsumaye, tuntuni abinda nake jiran su ambata kenan don na basu amsan da na tanada wanda ya dace dasu, amman sai yanzu ya samu fitowa.

"Daman shi É—an adam duk yanda ka ganshi kada ka raina matsayin shi ka wulakanta shi don baka san me dai zama a gaba ba,
Tun kafin ku roƙe ni gafara na riga na yafe ma kowanne da ya zslince ni a cikin ku, don ba zan iya ci gaba da ajiye tsatsar ƙiyayya a cikin zuciyata ba,
Sai kuma idan Allah ya sake haÉ—amu a wani wurin, na barku lafiya"
da faÉ—an haka na ja hannun Fa'iza muka juya muka bar musu gidan tsitt har muka fice babu wanda ya sake koda tari.

**********
Chapter 53 · 0% Book details