← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 73

Sashe 11

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk ranar da result ya fito nayi failing nakan yi kuka kaman raina zai fita amman ba shi zai saka gobe na maida hankali wajen karatun ba domin bayi cikin list ɗina kwata_kwata, ni so nake yi ma idan za'a ko a hutu na roƙe shi ya barni ina saran hanjin ligidi ina siyarwa ma yaran ajinmu don naga masu siyar musu suna ciniki sosai,

"Meye sunan yarinyar da ta ƙwace miki takardan jarabawan ki?"

Naji muryan Khamis ya katse min lissafin riban hanjin ligidi da nake yi, daram naji ƙirji na ya buga dan banyi wannan tunanin ba tukunna,
"Uhmm.. sunan ta..umm"

ÆŠan matsowa gaba yayi, ya harda yatsun shi yana jefa min wani serous look don ya lura kaman na É—auki abun a matsayin wasa ne,
"Listen to me s.."

"A'a ba lisin bane sunan ta, Rahama ne" na faÉ—a tare da sake fashewa da wani kukan munafurci don bani so ya sake jefo min wani tambayar da bazan iya amsawa ba,

Tsaki yaja a tsawace yace "ki saurare ni nace!! Na É—ago ina girgiza kai hawaye na sintiri kan fuska na,

"Wallahi Saudat idan baki maida hankali ba kudin motan ƙauyen ku ba tsada gareshi ba, wannan shine dama na ƙarshe da zan baki idan har kika zo sama da na 25th position next term a take zan biya kuɗin mota na saka ki a kaiki har ƙofan gidan mai gari ko rakiya ba zan miki ba, dan haka ya rage naki ki dage kiyi karatu ko kuma ki zauna shashanci, tashi ki bani wuri"

Miƙewa nayi ina kuka kaman raina zai fita duk na cika mishi kunne domin a rayuwata ko sunan mutuwa bani ƙinshi kaman yanda naƙi jinin a ambaci sunan mai gari, dole ne kawai na haƙura da burin rayuwa na niman kuɗi na rungumi karatun tunda shi uban gidan na yake so,

Jiki a sanyaye na tashi na shige bedroom ɗin Yusrah don tace idan mun gama nazo na same ta mu ƙarasa gyaran wardrobe ɗin Jannat sannan muyi fitting sabbin kayan da suka siyo na babies a ciki wasu kuma a jera su cikin drawer,

A zaune na sameta saman darduma ta zuba kayan a kan cinyar ta tana naɗewa, dagowa tayi tana kallon yanda nake sharban kuka ta miƙa min hannun ta ɗaya na ƙarasa na zuba a jikin ta har saida ta saki ƙara na buga mata ciki,
"Kada ki ƙarasa ni boɗɗi faɗa min yaya kuka yi dashi?"

Ban ɗago ba na ƙara shigewa cikin jikin ta ina kuka, "aunty Yusrah yace ƙauye zai maida ni gidan su Yarima dan Allah ki bashi haƙuri bani son na koma can"

"To ai laifin ki ne boɗɗi, ya riga ya faɗa miki abinda yake so amman kin kasa maida hankalin ki a kai, kinga shi wannan karatun da kike ƙi mutane da dama suna neman damar da kika samu basu samu ba, yanzu a ƙauyen ku waye kika gani yana karatu?"

Jan hanci nayi na share hawayen fukska na da bayan hannu na sannan na daÉ—a lafewa a jikinta a hankali na furta "Babu"

"to kin gani, wannan karatun shi zai baki ilimin wayewa na zama cikin mutane daban_daban da iya mu'amala da su, ke yanzu kaman wata izina ce ma sauran mutane saboda wahalhalun da kika sha na rayuwa tun baki da wayo har zuwa yanzu, sannan Allah ya kubutar dake ne ba don komai ba sai don ki zamo mai kawo canji a rayuwar mutanen da suke shan wahala irin naki suke azabtuwa a ƙauyen ku,

ke kaɗai ne kike da experience na wahalar da sauran matan ku suke sha dan haka ke kaɗai ce kike da kaman sinadari na kawo ƙarshen wannan wahalan, lallai ƙauyen ku akwai ilimin addinin musulunci amman ba'a amfani dashi, kuna da sani amman kuna danne sanin ku I'm sorry to say amman wani lokacin rayuwar ku kaman na tumaki yake, baku bin hanyar Allah baku bin tafarkin Manzon Allah s.a.w kuna rayuwa ne da son zuciyar ku kawai,

Saidai shi wannan ilimin na boko bawai kawai zai saka ki ƙware a turanci kina yi don ki burge mutane bane A'a, idan kika yishi mai nisa yakan baki wani power ne da zaki iya amfani dashi ki jagoranci al'umma, kuma kinyi min maganar kina son tara kuɗi amman shima wannan karatun bokon idan kika kai wani mataki a cikin shi kika yi Sa'an samun aiki za'a dinga biyan ki albashi ko wani wata,

don ilimi ko wani iri kogi ne bayi ƙarewa idan kika samu dama zaki iya ɗaurawa a kan wancan ɗin sai a ƙara miki matsayi a wurin aikin ki idan kina cikin masu Sa'a ko kuma ki samu wani aikin da ya fishi kuɗin da ake biyan ki sai ya ninka shi, kuma zaki iya haɗa karatu da niman kuɗi kaman yanda nake yi duk da ina da tsohon ciki amman me aka fasa? Kinga ni har uku ma na haɗa ga aure ga raino huɗu ma kenan"

A hankali na ɗago kaɗan tare da leƙa fuskar ta naga itama ni take kallo, ɗaga giran ta duka biyu tayi don ta tabbatar min da zancen tace "yess! Duk abinda na faɗa miki gaskiya ce" sannan taci gaba da cewa

"Rayuwar yanzu da kike gani idan kika ce kwanciya zakiyi to kin ƙulla ƙawance da takaici, ko babu abinda zakiyi da kudin ki neme su ko babu komai kinfi ƙarfin bani_bani, idanma mijinki bai amince miki ki nemi kuɗin ba ya yarda zai dinga baki duk lokacin da kike da buƙata fine! Idan ya amince miki kinyi karatu yace bayi son kiyi aiki fine!!

Duk da haka dai baki ci baya ba sabida zaki amfani yaran ki, sannan Allah ya kiyaye amman akwai mutuwa ko rabuwa idan ɗaya daga cikin su ya faru zaki iya amfani da certificate ɗinki ki dogara da kanki ba sai kin ɗaura nauyi ma iyayen ki ba kuma zaki iya ɗaukan ɗawainyar yaran ki dashi, idan kika samu irin wannan daman ba'a wasa dashi boɗɗi, please don't waste your golden opportunity mu muka amince zamu ɗauki nauyin karatun ki gaba ɗaya har ƙarshe,

Ko baki son ki samu daman komawa wuroɓokki ki gano halin da iyayenki suke ciki ne? Baki so ki shiga ƙauyen ku a lokacin da kima ga dama kuma babu wanda ya isa ya taɓa ki saboda kina da ƙarfin iko?'

"Ina so aunty Yusrah"

"To ilimi shine kaɗai abinda zai baki wannan damar, ki cire ranki ma kallon TV da kike yi babu dare babu rana, yanzu kaf draman hausa babu sunan actor ko actress da baki riƙe ba, ko kallon ma ya kamata kina sirkawa da na turanci ba don komai ba sai dan ki ƙara ƙwarewa,

amman kinfi so ki zauna kawai kina kallon labarin soyayya ace wance matar wane ne wance tana da cikin shege, wance ta aihu wane ya gudu da wance sunje sunyi aure ba tare da sanin iyayen su ba and stuffs,

you are too young for all of this rayuwar ƙauye ba irin ta birni bane, you are just 15 a can matsayin uwa mai shekarun ki take amman a nan har yanzu ma wasu mutanen zasu iya saka ki a sahun yara, kina da sauran lokaci boɗɗi dan Allah kada kiyi wasa dashi"

Gaba É—aya sai naji jiki na yayi sanyi da kalaman ta, duk abinda aunty Yusrah ta faÉ—a gaskiya ne, kamata yayi ma ace a yanzu maganar É—aukar fansa ma yaya na da mahaifi na ne a gaba na,

yanzu ne lokacin da zanyi amfani da dama ta saboda nan gaba na koma na ɗanɗana ma mai gari irin azabtarwan da suka ɗanɗana min na dawo da ya Aminu cikin ƙasar shi ta aihuwa sannan na wanke laifin da aka ɗaura mishi bai jiba bai gani ba,

"Insha Allah aunty Yusrah, me is read book me is no TV"

FaffaÉ—an murmushi ta sake don dukda turancin ba daidai tayi ba amman ta fahimci abinda take faÉ—a wato zata yi karatu kuma zata daina kallon TV,

"Allah yasa ƙanwata, daga yanzu ni da kaina zan dinga miki lesson kullum idan mun gama aiki muna hutawa indai abban Jannat bayi nan ko bayan na aihu ne kizo zan dinga miki lesson sannan zan baɗa auntyn ki Nasreen kuɗi ta siyo miki wasu litattafai don yanzu shiga kasuwa yana nima gagara na"

**********

"Aunty dan Allah har yanzu bai amince ba? Azumi sauran kwana uku ko huɗu kuma idan ya tafi Umrah har ya dawo ba gane mishi zamuyi ba, ki min wani ƙoƙari don Allah"

Ƙara ta sake saboda cizon da yarinyan da take shayarwa ta gantsara mata, ta dangwali goshin yarinya da ƙarfi ta kwala kiran nanyn ta, shigowa tayi ta miƙa mata yarinyar ta fita da ita tana jin yanda take tsala ihu saboda bata ƙoshi ba amman ko a kwalar rigan ta daman ba a son ranta take shayar da yarinya mai shekara ɗaya harda wata biyu ba, Sulaiman ne ya matsa mata dole saboda yarinyar bata da ishashen lafiya tana da yawan laulayi, Arif watan shi 10 a duniya ta yaye shi da ta samu ya fara karban cereal,

Yamutsa fuska tayi tana kallon budurwan dake gaban ta wanda nake tsammanin yayar Sulthana ce dan dukkan su suna É—ibi da Sadiya

"Yaya kike so nayi Muna? Kema da ba a gidan nan kike ba kinsan halin mutumin nan idan yace ba zaiyi abu ba sau ɗaya bayi dawowa ya yarda yayi, tunda nake da Sulaiman bai taɓa dawowa a kan maganar sa ba dan haka tsanantawa ma ɓata lokaci ne,

ki haƙura kawai ki ƙarasa karatun ki a makarantar da ya saka ki tunda ya nace da hakan muci gaba da karɓan kuɗaɗen shi kawai"

Tsaki Muna taja ta tashi tabar mata parlorn, ita duk ba haka tayi tunani ba bata ɗauka ba tare da ita za'a tura ibadan ba don har ta fara faɗa ma ƙawayen ta an cire su a MAUTECH za'a maida su makarantar da ya fishi tsada,

Tana shiga wani bedroom ta zube a kan gadon sannan ta jawo wayarta ta danna kiran Sulthana bugu É—aya ta dauka,
"Ke har yanzu kina gidan baban wulaƙancin nan ne?"
Chapter 11 · 0% Book details