Sashe 21
Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maido da mugun kallon yayi gare ta jin tambayar rainin hankalin da take mishi, kafin yace wani abu Sulthana ta rufa mata da
"Maganar me kuke yi da wancan yarinyar darling?"
"A cikin ku akwai mai bina bashi ne da zaku tsare ni da tambayoyi?" Ya faÉ—a haÉ—e ta tamke fuskar shi tamau kaman bashi bane suka shigo suka same shi yana dariya,
Basarwa Sulthana tayi tana ƙaƙalo murmushi ta ɗaura hannun ta saman kafaɗar shi tare da kwantar da kanta a jikin shi
"Ba wannan ba darling, akwai maganar da daman nake son muyi da kai..."
Bata samu damar ƙarasa magana ba ya miƙe shima ya fice don yana tunanin idan yaci gaba da zama dokin zuciya zai iya saka shi ya naɗa ma wannan wawiyar yarinyar duka da bata san mutuncin kanta ba a watan Ramadana ma ba zata shiga hankalinta ba,
moreover zata iya haddasa mishi fitina yana zaman_zaman shi yanzu su ɗago babban yaya ba shiri ya dawo daga tafiyar da yayi yazo ya sauƙe mishi buhun masifa,
shi ya tsani mace mai zubar da kanta shiyasa ko tarayyan ƙannen shi da wa'innan yaran bayi so amman babu yanda ya iya Allah ya riga ya haɗa alaƙar su, idan da shi fitinanne ne duk yanda yasan zaiyi sai ya shiga tsakaninsu kuma ya nesanta ƙaramar mara kunyar nan daga gare shi,
Babu kowa a parlorn su sai tv dake kunne an saka karatun ƙur'ani, zama yayi a kan kujera tare da jinginuwa ya lumshe idanuwan sa don bawa zuciyar sa daman hutawa, ya san saudat ba lallai ne ta zamo matsala ba, yarinyar da yarinta sosai a jikin ta yana ganin shiga zuciyar ta abu mai sauƙi ne sosai duk da ba yanzu ya shirya ma auren ta ba, sai nan da wasu shekaru masu zuwa,
Saidai babban yaya babban matsala ne, ya ma rasa ta ina zai fara tunkarar shi da maganar idan lokaci yazo, ya rasa ta wani siga zai fito mishi da zarar ya dawo daga tafiyar da yayi yayi masa jagora gidan su boÉ—É—i a san dashi don kar wani yayi mishi shigar sauri,
Abu mai sauƙi ne Sulaiman ya tarwatsa duk wani farinciki nashi don samun lafiyar shi, kuma samun Saudat yana cikin abubuwan da idan har yana ɗauke da matsalar shi ba zai taɓa yiwuwa ba,
Fatan shi ɗaya Allah yasa Sulaiman ya fahimce shi kuma ya bashi dama don ya jarraba sa'ar shi ko shima yana da rabon ganin jinin shi a doron ƙasa,
 *****
Banji daÉ—in raba ni da Sitifid da suka shigo sukayi ba, dukda tsokana ta yake yi but I'm enjoying his company, tun yanzu har kewar shi ta fara shigana,
Na san wasu zasu yi tunanin nayi saurin saka shi a raina kwana biyu kawai da haÉ—uwan mu amman kuma mutane irin Sitifid É—aÉ—É—aya ne a cikin gidajen masu kudi,
Mutum ne mai sauƙin kai kuma ga daraja ɗan Adam a duk gidan bayan iyayen su shi da Ruma da boyfriend ɗina junior ne kawai basu nuna min banbanci sai kuma aunty Zaytoon,
Ba wani abun mamaki bane don a zaman kwana biyu na fahimci halin kowa a cikin su, zan iya cewa wahalan rayuwa da nasha a baya da kuma ƙwarewa da na samu a wurin mahaifi na ne ya koyar dani hakan amman kuma duk cikin su ma babu wanda yayi ƙoƙarin ɓoye min halin shi don basu ɗauke ni da muhimmanci ba,
Har ƙarfe 5½ ina kwance sallan la'asar ma da ƙyar na iya daddafawa nayi inajin hanjin ciki na kaman zasu tsinke, a yanzu haka suna ta haɗa abincin shan ruwa amman ba zan iya fita taimakon su ba don idan idanu na sukayi karo da abin in nan akwai matsala, duk bayan mintuna goma sai na kalli agogo,
**********
Fitowa daga É—akin yayi da laidoji a hannun shi ya nufi kitchen yaga ko tana can, turus ya tsaya ganin Yusrah jikin turmi tana daka ga abulkhairi sai zunduma ihu yake yi amman bata da niyyan sauraron shi,
Ajiye laidojin yayi baiyi mata magana ba saboda ganin yadiko a wurin ya ƙarasa ya since yaron shi daga bayan ta ya fita yana rarrashin shi, ganin haka yasa yadiko tace ta sake aikin ta bishi don babu yanda batayi da ita ba ta bari amman ta ƙi,
"Saboda ban je na dawo da saudat ba ko? Shine zaki yi ma É—ana wannan horon, yaron 6 days amman kika shiga kitchen dashi"
"To babu wanda zai taya yadiko aikin ne yayi mata yawa wallahi tun safe take ta ɗawainiya ga namu ga na gida, shiyasa naje na ɗan kama mata wani abun kuma Abul yaƙi barci balle na kwantar dashi a ɗaki"
"Yanzu karɓe shi ki shayar dashi" babu musu ta karɓe shi, yace "na faɗa miki zainab zata zo anjima kuma zata zauna har lokacin da Saudat zata dawo gidan nan dan Allah kiyi haƙuri kada mutanen nan suga rashin haƙurin mu, ai abin daɗi ne ma a gwada ana son naka, ba wani cutarwa ne yake samun ta a gidan ba"
**********
"Zaku iya tafiya", ya bada umarni a taƙaice, yana kallon bayan su har suka gama fita aka rufo miki ƙofar room ɗin sannan ya ɗaga wayan shi yana dubawa,
Ajiye wayan kawai yayi ranshi yana daɗa ɓaci tunda ya baro gida ko sau ɗaya iyalinshi bata nime shi ba, bata damu ta san ko ya iso lafiya ko akasin haka ba, ba zata nime shi taji ko yana cikin wani matsala ko damuwa ba, shi babba ne kuma mahaifin wasu amma ba'a girma ma kulawa ko tsoho ma zai buƙaci kulawar iyalin shi ballantana shi mai jini a jika,
Yana da daÉ—i ka gwada kulawa ma abokin rayuwar ka hakan zai sanya ko yaushe ka zama a cikin zuciyar shi, it feels so good kasan kana da muhimmanci a wurin wani koda kuwa wanene idan kayi nisa ko yaya ne a nuna anyi kewar ka, amman Sadiya bata san wa'innan abubuwan ba ta saka wasu damuwa daban a gaban ta,
Yana fatan Saudat ɗinshi ba haka take ba, da kuwa idan ya aure ta tafara bashi kulawar da yake buƙata zai bawa sadiya mamaki, zaiyi mata abinda bata tsammani wanda zai saka ta shiga taitayin ta dole,
tama gode ma Allah shi ba mai bin mata bane amman a yanzu kashi 90 na matan waje dake bin maza sunfi matayen su na cikin gida basu kulawa da tarairaya da kuma iya nuna musu soyayya ba don komai ba sai dan sunfi su sanin darajan mazan,
Ballanta shi mai shiga wurare garuruwa da ƙasashe da dama donyin business ɗinsu, babu kalan matan da bayi gani, kyawawa wanda suka fi matar shi kyau nesa ba kusa ba da kuma wa'inda basu ma kamo ƙafan ta a kyau ba, amman suna ƙoƙarin suga sun samu mazan da zasu basu kulawar ma ya gagara,
ita matar ɗaki tana ganin ai bata da wani sauran damuwa tunda ta riga ta same shi har tana da yara dashi yanda rabuwa da ita zaiyi mishi wahala, amman meyasa ba zata yi ƙoƙarin mamaye zuciyan shi ba tunda tana da daman hakan?? Ba'a taɓa tsufa ma soyayya!!!
*****
A ranar muna cikin shan ruwa babban yaya ya kira video call ta system É—in Batool, ban sani ba ashe dalilin kuran don ya samu gani na ne amman bawan allan nan daga an juyo da screen É—in fuska na don na gaida shi yayi disconnecting É—in kiran,
daman nasan hakan zata faru don na lura kaman yafi Nana tsana ta, shiyasa ni ko inuwa ɗaya dasu bani son zama dan gudun wulaƙanci,
A taƙaice dai yauma kwanan gidan nayi, washe gari ma suka hana ni tafiya duk yanda na matsa saboda shirin sunan babyn aunty Yusrah, ban tashi komawa gidan ba sai washegari da yamma bayan ƴan suna sun gama taruwa muke je nida Ruma,
Bata daÉ—e ba ta koma gida amman tsantsar takuri na Zayyad yasa washegari suka yi list É—in kaya da za'a kai mata harda takalma suka turo dashi ba tare da Hajiya ta san komai a kai ba,
Ai kuwa buƙatar su ya biya, don da aka kawo kayan ni aunty Yusrah ta tura na kai musu daga nan kima suka ci gaba da riƙe ni,
A hankali na fara sabawa da baƙin maganan Nana da Sulthana da kuma zagin Fa'iza wanda babu wanda ya tsallake shi saidai idan bai faɗo ta kanka ba,
Zayyad lokaci ɗaya ya shiga zuciya na yayi min mamaya ba tare da na sani ba, saboda wani mummunan sabo ne ya shiga tsakanin mu a cikin kwanakin da basu fi a ƙirga su da yatsu ba,
Hhh saboda yanayin da na tsinci kaina na cewa na taɓa soyayya da kuma aure na san banyi yarinta ma soyayya ba dukda kuwa su ta nasu fuskan ba haka suke gani ba, amman na san son sitipid ma aikin banza ne don ba zan taɓa samun shi ba, amman ita zuciya bata da ƙashi, sau da yawa tana saka kanta a abunda baka so ta shiga ba wanda zai saka ka zubar da hawaye mara adadi,
Ban sani ba ko idan ma buƙatar nawa ya biya irin na baya za'a yi, yanda na dinga buri da mafarkin zama ta yarima wanda daga baya kuma hakan ya juye ya zamo min baƙin ƙaddara, ina tsoron soyayya ina kuma tsoron aure ciwon da suka ji min a zuciya har yanzu basu goge ba ballanta na ƙara wani a kai,
Ko wace rana ni da Zayyad mukan zauna can cikin garden yanda mutane basu fiye zuwa ba babu wanda zai san muna can, mu taɓa hira sosai hakan sai ya saka duk yunwa da galabaitan azimi da nake ji ya gushe kuma na ƙarasa wunin Ranar cikin farin ciki da annashuwa,
17/Ramadan/1442
A yau aka kai azumi 17, a yau kuma wannan sarkin zafin babban yaya ya dawo,