← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 73

Sashe 26

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fita tayi tana faɗin bari naje na kira miki shi yazo har wurin da kike da kanshi sai ki mishi ƙaran,

**********
"Gaskiya yarinyar ta birge ni dadyn Arif a ina Ruma ta samo ta haka? Ƴar gidan waye yarinya mai zafin nama da fara'a gata kyakkyawa masha Allah"

Siririn tsaki yaja don surutun ta ya fara damun sa, shi niman hanyar gyara abinda ya ɓata yake yi yana kokwanton ko yaje ya bata haƙuri ne ko kuma ya bari ta gama fushinta ta sauƙo ne bai sani ba, kada yaje girman shi ya faɗi a wurin yarinya daman gata sakaliya ta daɗa lalacewa

"Ni Ruma ce da zaki na tambaya ta inda ta samo ta?"

"Gani fa nayi tare suka zo ko hala distant relative ne ko kuma ka san daga inda take don naga yawancin mutanen dake mu'amala da Æ´an gida ka san su"

Maida hankalin shi kan system ɗin gaban shi yayi tare da tattaro dukkan nutsuwan shi yana fatan concentrating ko na minti 10 ne saudat ta fita daga tunanin shi ya ƙarasa aikin gaban shi,

"Amman ka san gidan su dadyn Arif? Ko kasan iyayen ta?"

"Ya rabbi!! Amfanin me sanin hakan zaiyi miki? Idan har da gaske muradin samun ta kusa dake kike yi ki kwantar da hankalin ki kwanan nan zata dawo cikin gidan nan da zama sai ma kin gaji da ganin ta"

**********

"Babe's please tell me waye ya taɓa min ke, bani son ganin fushin ki kiyi magana dan Allah"

Rau_rau nayi da idanu ina jin daɗi a raina saboda yanda Zayyad ya nuna min kulawa, sannan cikin shagwaɓa nace,
"Hamma zayd yau zan bar gidan nan wallahi, ba zan iya ci gaba da zama ba"

Gyara tsungunon shi yayi a gaban kujerar da nake zaune ya zuba min idanuwa, we were so close yana ji a ranshi kaman ya haÉ—iye ni saboda yanda ji na a ranshi,

Har wani kalmasa murya yayi yanda zai nuna he really cares yace
"Subhanallah, me yasa Saudat? Ko wani abu ya faru ne ban sani ba?"

"Abin da babban yaya yake min ne bani so, ni ban san abin da ya haÉ—a ni da shi ba amman ya saka ni a gaba babu dalili"

"amman kin tabbata ba wani rashin ji kike masa ba Saudat?"

Girgiza kai nayi Ruma tace "wallahi ya Zayd babu wani rashin ji da take mishi, kaima ka san halin babban yaya idan ya saka mutum a gaba ko baiyi komai ba ma yayi laifi"

"Huhh" ya furzar da numfashi yana kallon ƙasa ya maida idanun shi cikin nawa sai faman cika nake ina batsewa

Shiru yayi yana nazarin kalaman ta don tabbas abin da ta faÉ—a gaskiya ne wani lokaci É—abi'un sulaiman har kamanceniya yake yi da na Nana shi dai ya fita kyakkyawar zuciya amman ba kowa bane ya gane hakan,

"kiyi haƙuri Please, ina baki haƙuri a madadin shi kuma insha Allah zanyi mishi magana amman kema da laifin ki tunda jiya saida nace miki ki tsaya muyi magana dashi kika gudu da hakan bata faru ba"

Turo baki gaba nayi nace "ai banyi tunanin zai sake matsa min bane da na tsaya jiyan ka mishi faÉ—a"

"Hhhh hajiya boÉ—É—i shine sama dani fa! Ta yaya za'ayi na iya mishi faÉ—a? saidai nayi mishi magana na lallashe shi ya daina takura miki"

  *****
Yana dai zaune ne ya zuba musu idanuwa amman abun da suke tattaunawa sam bayi samun isa cikin ƙwaƙwalwar shi, idan ya tsinci magana a sama ne sai ya jefa musu wani umarnin yaci gaba da saƙe_saƙe cikin zuciyan shi,

Sai wuraren la'asar suka kammala duk abubuwan da zasu yi suka tafi shima yabi masallaci daga nan ya samu daman komawa gidan su don ganin yanayin da Saudat take ciki hala har yanzu ma tana fushi dashi, ya ayyana a ranshi bayan ya shige part É—in su Zayyad yana son fara ganin lafiyan É—an uwanshi kafin yayi abinda ya biyo baya,

  *****

"Kaii! Madam rigiman ki da yawa ina dai kin haƙura ba zaki tafi ba?"

Sai wani shan ƙamshi nake ina ɗaɗɗaga kai jin ana roƙo na, "Please! Please! Please! Kiyi haƙuri ki zauna dan Allah"

"To shikkenan naji zan zauna, sai nan da kwana 5 zan tafi,
na faÉ—i haka saboda ban ma san abban Jannat yazo É—auka na É—azu ba dan tunda muka dawo ko part É—in Hajiya ban shiga ba na biyo daÉ—i masoyi,

"Zan iya tafiya yanzu?"

"Yaya jikin naka? Rumaisa tace min baka da lafiya"

"Da sauƙi sosai babe's, nama warke da naga fuskan ki

Bansan lokacin da murmushi ya kuɓuce min ba nace "ok zaka iya tafiya"

"Godiya nake ranki ya daɗe" ya faɗa tare da miƙewa ya gyara zaman rigan shi sannan ya fice ina bin bayan shi da kallo,
Da ace ni budurwa ce kuma na cancanta da nayi fafutuka wurin nemo soyayyar Zayyad don ina ganin har duniya ta naɗe ba zan taɓa samun irinshi ba,

Aunty amarya tana zaune a parlour tana lazimi as always, sulaiman ya shigo ya nemi wurin zama sannan suka shiga gaisawa don yau bai shigo gidan ba gaba ɗaya sai yanzu, suna cikin haka Zayyad yazo wucewa ya dawo da fara'a ganin su zaune shima ya zauna saidai gaba ɗayan su sun shiga Ruɗani mamaki ya kama su matuƙa, shi kuwa kaman ma bai san abinda ya faru ba har saida Aunty Amarya tayi magana

"Zayd! Me ya kaika É—akin Æ´ar uwarka? What's wrong with you? Me yasa zaka je ko iyakan da akayi maka da hakan ne ka manta?"

"Aunty I'm fine, magana kawai naje muka yi ki kalli babu abinda ya same ni" ya faÉ—a tare da nuna jikin shi,

"Me yasa kake min haka ne Zayd? Kullum kafi son gani na cikin damuwa a kanka ƙananun dokoki ma baka iya kiyaye su? Kafi son ganin kanka cikin wahala duk abinda ake faɗa maka baka ji? Saboda kada takurawan yayi yawa yasa fa nake barin ka kana zuwa duk inda kake so a cikin gidan nan amman hakan ma bai ishe ka ba sai ka ƙetare iyakar ka?"

"nifa ba Yaro bane Aunty ba zan taɓa yin abinda zai cutar dani ba ku fahimceni dan Allah"

  ******

"Heyyy dariyan me kike yi ke kaɗai kaman wata taɓaɓɓiya" Ruma ta faɗa yayin da ta zuba a gefe na bayan ta idar da sallah tana leƙa fuska na,

"FaÉ—a min mana boÉ—É—i meye ne ya faranta miki haka lokaci É—aya gashi kaman kin manta fushin babban yaya da kika dawo dashi"

Murmushi nayi ina shafa zanen tafin hannu na cike da kunya nace
"Rumaisa yayan ki is beri nesh (very nice)"

Yamutsa fuska tayi ko kalma É—aya bata gane cikin abinda na faÉ—a ba,
"Nifa nace ki daina min fulatanci idan muna magana kindai san ba ganewa nake yi sosai ba, menene kuma wani bari nesh?! Ko zagin shi kike yi baki son na gane?"

Maman Naxee: "haba niÉ—in banza" na faÉ—a ina dariya "ai ban kai wanda zan zagi hamma Zayyad na zauna lafiya ba bacin shi É—in garkuwa na ne"

"awwwn? Do you love him? Umm.. ki faÉ—a min dan Allah idan kina sonshi wallahi zanyi farin ciki da hakan"

Kallon ta kawai nayi zuciya na yana tsananta bugu, babu abinda ya faɗo min a rai a lokacin sai Yarima!! Wuroɓokki, Inna ta da baba na da kuma ya aminu!
Har inada kwanciyar hankalin sake soyayya bayan da wa'innan a gaba na?"

Saudat!! Muryan ta ya katse min tunani, "ajema a matsayin yanzu baki son yaa Zayd amman da alal misali ace kece matar da zai aura, to ana daff da auren ku sai kika fuskanci yana da wani matsala da zai iya kawo cikas ma rayuwar auren ku, zaki yarda ki aure shi?

Shiru nayi ina kallon ta tare da ƙoƙarin gano inda zancen ta ya dosa,  wannan ne karo na biyu da Ruma tayi zancen matsala kuma ta danganta shi da Zayyad, me hakan yake nufi? Akwai wani ɓoyayyen al'amari a kanshi ne?

"Baki bani amsa ba"

"Rumaisa hamma Zayyad É—in yana da wani matsala ne?"

"Bani son ki É—aura min wani tambaya a kan tambaya ta idan kika bani amsa ta zaki samu amsan ki a cikin ta, zaki yarda ki aure shi a hakan?"

"Ƙwarai kuwa indai ina son shi da gaske zan aure shi saboda ina da tabbacin inda ace ni ke ɗauke da wannan matsalar Zayyad ɗin da na sani ba zai taba gudu na ba"
[1/6, 7:55 PM] Maman Naxee: "kin amince dashi kin yarda dashi sosai bayan haÉ—uwan ku gaba É—aya kwanaki 20 ne, how comes?"

"Ban sani ba Rumaisa domin bani na amince dashi ba zuciyata ce ta amince dashi kuma taƙi sanar dani dalilin hakan, ban san yanda akayi yayan ki ya shiga jiki na haka ba kuma ina fatan kada yayi tasiri gudun ɓacin rai"

******
Saboda yanda ran Zayyad ya ɓaci a yau cacan baki saida ya saka su kaman zasu bugi juna da Sulaiman, shi ba uban shi ba amman matsayin da ya ɗauka cikin rayuwar shi yafi na iyayen shi girma,

hayaniyar su ne ya ɗago mu daga ɗakin Ruma fitowar mu keda wuya muka ci karo da Zayyad ya zube a ƙasa........🤦🏻‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

22🧝🏻‍♀️
Tunda Sulaiman ya faÉ—a ma Sadiya wa'innan kalaman hankalin ta ya kasa kwaciya ta rasa gane abinda yake nufi da Saudat zata dawo zama a gidan su har sai ta gaji da ganin ta kenan auro wannan yarinyar zaiyi??
Chapter 26 · 0% Book details