← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 73

Sashe 69

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashin su duka biu tayi da kanta tayi musu wanka ta shirya su cikin uniform É—insu na islamiyya daga nan ta fice zuwa kitchen, a canma saida ta tabbatar komai ya tafi daidai an haÉ—a breakfast kafin ta taya maids É—inta suka jere a kan dining lokacin Sulaiman ya gama shiryawa har ya fito, a tare suka zauna sukayi breakfast ana raha ana dariya, dukkansu sun lura da farin cikin dake kan fuskar Arif da islaha dan bakin yaran kaman zai tsage don murmushi.

Da akazo rabuwa ne kuma abinka da ba saban ba ta tsaya tana kallon su ta rasa abinda zatayi musu ko waving ta kasa tana tsaye jikin ƙofa har suka shiga mota suka har gidan,

*******
"Baby love are you alright?" Na sake tambaya ganin tunda muka kusa landing yake ta faman rintse ido yana cisgan numfashi kaman breathing mask É—in da suka saka mishi ya dame shi.

BuÉ—e idanunshi yayi lokaci É—aya har sun sauya kala zuwa ja, ya gyaÉ—a kai tare da faÉ—in
"Yeah babes I'm... I'm alright, kawai my heart is beating so fast kuma inajin raÉ—aÉ—i sosai kaman zai faÉ—o ya fito"

"Hasbunallah! Zuciyan ka ba zata faɗo ba Chona" na faɗa tare da saka hannu na a daidai saitin zuciyan nashi inda ya riƙe, cikin murya mai nuna damuwa nace "u will be fine insha Allah bari na kira nurse ɗin ta sake duba ka"

Girgiza kai yayi tare da matse hannu na a kan ƙirjin nashi yace
"No, just leave it. Hakan ma ya ishe ni har naji kaman ciwon ya tafi da abinda nake marari yaje kusa dashi,
I don't need the nurse bata san maganin ciwo na ba ke kaɗai ne zaki iya sakawa naji sauƙi, just stay here please!"

Bance komai ba na ɗaura kaina a saman kafaɗan shi, hannu na na riƙe a cikin nashi manne a saitin zuciyan shi, inajin yanda yake sauƙe ajiyan zuciya a hankali.

Muna sauƙa muka samu asibitin da zamuje ɗin har sun turo ambulance da zata ɗauke mu airport ɗin, muna shiga suka kwantar dashi suka fara bashi taimakon gaggawa ganin yanayin da yake ciki, hannun shi riƙe da nawa yaƙi sake ni har sanda akaje ɗakin da na'urar da za'a saka shi ciki don ganin ainihin matsalar shi yake kafin suka saka shi dole ya saki hannu na.

Samun wuri nayi na zauna a waiting chair damuwa fall a raina ina roƙon Allah yasa idan aka bincika abinda yake damun shi a zuciyan a samu ba abune mai girma ba, banfi 10 minutes zaune ba wata baturiya tazo ta tsaya a kaina sannan ta kira ni da "Mrs Zoyyad Mohamad?"

Ɗagowa nayi na kalleta tare da jin yanda ta kwaɓulo sunan, amsawa nayi da "yess"

"Oh hi I'm Cynthia, your husband's childhood friend"

Gaisawa mukayi cikin harshen turanci sai yanzu nake tunanin da ace har yanzu naƙi makaranta irin wannan ranar tazo min da bansan yanda zanyi ba don tabbas za'ayi kwaɓa.
Zama tayi tana faɗamin kan cewa babban yaya ne ya turo ta Saboda maganar masauƙin mu da wurin da zan zauna kafin mu isa masauƙin.

Ta buƙaci na bita gidan ta na kwana a can naƙi don yau ba zasu bani dama naga Zayyad ba sai sun gama binciken su, da ƙyar na yarda muka tafi tare mukaje gidanta babban gida da yaranta guda biyu da mijinta suka bani ɗakin kwana sannan suka turo min dinner, ban wani Ci ba dukda bawai abincin da ba zan iya ci bane na taɓa ɗan kaɗan na bari,
Washegari da safe ma ko breakfast banyi ba suk yanda taso zaunar dani na ƙi na kamo hanya na dawo asibiti dan tunjiyan ake ta kirana daga gida ana tambayana jikin Zayyad.

Ina isa har É—akin da suka kwantar dashi suka kaini, da shigana na samu yana shirin fara breakfast.
"I'm sorry babylove banso tafiyaba wallahi Cynthia ce ta matsa sai na bita...." Na faÉ—a cike da damuwa idanu na akan nurse din dake tsaye a gefe da spoon a hannunta sai rarraba idanu takeyi don bata yi tsammanin wannan patient din da budurwan shi yazo ba shine ta matsa wai bayi da lafiya ita zatayi feeding É—inshi.

"Shh...cool down baby, it's ok gwanda da kika je kika huta, nasan ɗawainiyan akwai gajiya, kina ƙoƙari i appreciate it"

"Haba hamma Zayd stop saying that ina wani gajiya a nan, its my duty which I'm not even doing properly"

Bai sake cemin komai ba ya juya wurin nurse É—in dake tsaye tana binmu da idanu
"You can leave Venessa, my wife is here she can help me thank you"
Ba haka dai taso ba ta ajiye mana spoon din sannan ta juya zata fita.
"Babes zo ki ciyar dani da hannun ki masu albarka"
Murmushi nayi na ajiye jaka na sannan na shiga toilet na wanko hannuna na fito na saka a cikin abincin na fara bashi a baki.

"Babylove yaya akayi har kasan sunan wancan arniyar?" Na tambaya tare da turo baki cikin shagwaɓa.
"Ohh someone is jealous! Ofcourse she is my nurse, kuma ita ta faÉ—a min sunanta kafin ta fara attending É—ina so babu laifi idan na san sunanta ko?"

"Eh dai dukda haka da kayi addressing dinta as nurse É—inta kawai ya isheta, ni bani son mata suna kalla min kai... And don't you dare to smile again a gaban wata koda kuwa ni ka gani bani son su kallamin dimples dina"

Dariya mai sauti yayi ganin yanda nayi kicin_kicin na ɓata rai
"Tsare gida kenan babes? Kada ki damu ai kin riga kin gama dani tunda har kika kwantar dani a nan wurin"

Murmushin da banyi niyya bane ya suɓuce min ina jin kaina wani a sama, a haka na ƙarasa bashi abincin da muka gama na haɗa shi da su aunty a waya.....

*********
Ba wai ainihin aiki bane ya saka shi zuwa office din, he needs space to think da irin sabuwar rayuwar da ya tsinci kanshi, dole ya yaƙi zuciyar shi ya zamo mai haƙuri sannan ya rage zafin zuciya da fushi uwa uba ya ajiye girman kai idan yana son samun lafiya tsakanin shi da Sadiya,
He have to make their marriage work dole ya saka ma ranshi kaman yau sukayi aure yanzu ne zasu fara shimfiɗa Foundation na rayuwar auren su, haka ya zauna daga shi sai securities a companyn ya taɓa aiki ya taɓa tagumi har yamman tayi kafin ya tattara zai tafi,

Har ya kusan isa gida yaga bai kamata ya koma musu haka hannu na dukan cinya ba, a wani mini store ya tsaya ya saya musu kayan maƙulashe kaɗan sannan ya tafi.

Yana isa da gudu su Arif sukazo suka rungume shi ganin shopping bag a hannun shi yasa dukkan su suka fara kai hannu zasu karɓa,
Jan bag din yayi baya fuskar shi É—auke da fara'a ya ciro chocolate manya daga ciki ya bawa kowa nashi a hannun shi suka shiga cikin gidan da gudu suna murna,

Sadiya dake tsaye a jikin labule tana kallon su ne tayi murmushi tare da miƙo masa hannunta da yasha jan lalle ga bangles dinta sai daukan ido sukeyi.
"Welcome back dadyn Arif, ina nawa tsaraban"

Riƙo hannun yayi ya kai bakin shi yayi kissing, ji tayi kaman an watsa mata abu mai sanyi a zuciyanta daɗin wannan sabon yanayin nashi yana ratsa ta, bata da abinda zatayi yanzu da ya wuce godiya ma Allah, abubuwa lokaci ɗaya sunata gyaruwa.
" Lallen yayi kyau sosai habibty"

"Awnnn thanks Habibi, daman ma kai akayi tunda ka yaba shikkenan ya biya"

"No bai biya ba gaskiya, yanzu dai karɓi tsaraban ki" ya faɗa tare da miƙa mata laidan hannun shi "danzo na bada tukuicin shi daga baya"

********
Kwanan mu 4 a asibiti Zayyad ya É—aga musu hankali saida suka sallame mu don har office din doctorn dake kula dashi yaje ya tada ma bawan allahn nan hankali saida ya rubuta mishi takardan sallama don haka kawai yayi aure ba zasu saka shi yaci gaba da zama a matsayin gwabro ba, he needs to go and rest with his wife.

Nayi_nayi na hana shi ya bari jikin shi ya ƙara kyau tukunna amman yace fyatt shi baisan da wannan zancen ba, harda gwada min ƙarfin iko tunda shine gaba dani dole nabi ra'ayin shi, har iyayen shi saida suka saka baki amman yaƙi sai cewa yayi ai ba barin ƙasar zaiyi ba, yana nan babu yanda zaije kuma zai dinga zuwa checkup amman zama kam ba zaiyi ba.

Babu yanda suka iya haka suka sallame mu, muka shiga taxi da ze kaimu masauƙin mu dake a bakin wani beach.

"Beach?! Seriously?" Na tambaya a firgice tare da ƙwalalo idanu cike da tsananin mamaki,

"Yeah, daga elite hospital yanzu zamu tafi cocoa island beach"

"Kasan me kake faÉ—a kuwa chona? Beach fah! Musulmai damu zamu je beach? Wurin da mutane suka zuwa rabin jikin su tsirara?"

Ware hannayen shi yayi yace "to yaya zamuyi babes a wurin masauƙin mu yake, i have a house there ko inada nawa muhallin kinfi son muje hotel mu kwana? Toh hotels ɗinma suma a bakin Beach suke, we are living in an island everywhere is sorrounded by water please understand"

Turo baki nayi na koma jikinsa na gyara na kwanta ina ƙunƙuni zanga yanda za'ayi yau musulmai suyi rayuwa a beach.
Chapter 69 · 0% Book details