← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 73

Sashe 61

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Madina kaman kin daina kulawa da lafiyar ɗanki yanzun, ko dan kina taƙama da yanzu babu abinda muke tsoro ne? Amma kada kiyi sake mu koma gidan jiya fah ki guje ma danasani"

Kawar da kanta gefe kawai tayi bata ce komai ba, ya maida duban sa wurin Zayyad yace
"Zo ka zauna"
Babu musu ya ƙarasa ya sami wuri ya zauna,

"Ɗazu munje wurin iyayen Saudat mun tattauna sosai dasu tattaunawa irin ta fahimta, saidai buƙatar da muka je dashi bai ƙarɓu ba, amman ya tabbatar mana idan yarinyar tana son ɗaya daga cikin ku zai bamu saidai ba zai yiwu ku neme ta dukkan ku a lokaci ɗaya ba.
Toh da na dawo na samu zama da mahaifiyarka da ɗan uwanka na samu labarin cewa kai ka haƙura ka bar mishi ita, da gaske ne?" Ya karashe maganar da tambaya.

Da rinannun idanun shi Zayyad ya ɗaga ya kalli Sulaiman kallo mai cike da jin haushi da tsana wanda wannan ne karo na farko da ya taɓa jin haka a zuciyan shi, babban yaya ya kaishi ƙasa da ƙarfi ya raba shi da farin cikin rayuwarshi.
Gyaɗa kanshi yayi a hankali ƙwalla na taruwa a idanun shi yace
"Eh! Na haƙura!!...if...if you will excuse me i will like to go and rest"

"Shikkenan jeka Allah ya baka lafiya, idan kaji sauƙi insha Allah zamu zauna kaima ayi maganar haɗa auren ka da Sulthana, saboda inason ganin kaima kayi settling kana da iyali yanzu right"

What?? Three bombs at a time? Bayan da ƙarfi an raba shi da Saudat an kuma bada ita ma yayanshi yanzu kuma ana son yi masa auren dole da wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyar? Me yasa sai shi? Me yasa ko yaushe shine kawai loser? Bai taɓa winning ko sau ɗaya ba why???

Wani abu mai ɗaci yaji ya tsaya masa a maƙogwaro ga zuciyansa dake zafi kaman ana gasa masa shi,ji yakeyi iskan dake ratsowa ta windown ɗakin da na AC duk ya kasa mishi, kaman an jefa shi ne a wani rami aka rufe, he feels suffocated.
Da azama ya tashi zai bar parlourn saidai bai kai ko bakin ƙofa ba ya faɗi a ƙasa ya fara kwararo amai.

Gaba ɗaya hankalin su tashi yayi sukayo kanshi da gudu, duk sun daburce sun rasa Abinda zasuyi masa ɗaya, yana kan harar da abinda ke cikinsa ne ya samu hawayen da yake ta yaƙin tsaidasu ɗazu suka sauko, yana jin maganganun su a kanshi sama_sama da ihun kiran sunan shi da sukeyi da na neman taimako daga sauran mutanen gidan, a hankali idanunsa yake rufuwa har ya dawo bayi ganin komai sai duhu ya daina jin muryoyin su idanun shi suka rufu ruff......

********

Bayan doctorn ta iso ta duba ta ne tayi mata allura tare da bata pain reliever tasha sai a sannan ta samu barci ya É—auke ta,
Sauƙe ajiyan zuciya Sadiya tayi tana kallon fuskar ƙanwar tata wanda ta haukace a kan soyayyar wanda ya sota a da amman a yanzu bata gaban shi, tasan ƙaramin hukuncin da sulaiman zaiyi mata shine ya saka ta tattara ta bar mishi gida ta koma gidan su aci gaba da kame_kame.

Fita tayi daga ɗakin jin ana kiran sallan isha, taje tayi alwala tayi Sallah sannan ta zaunar da yaranta tana basu abinci da kanta, tana fatan idan yaga hakan ya sassauta fushin sa a kansu, yau ko me yake so yake buƙata zatayi mishi indai zai fasa hukunta Sulthana.

Har zuwa wani lokaci babu shi babu labarin shi, ta kira numbern shi yafi sau a ƙirga bayi picking, hakan ne ya bata daman yin wanka ta sake tsantsara ado cikin ƙananan kaya wanda ya amshi fatar jikinta tayi kyau ba kaɗan ba, sai baza ƙamshi take duk inda ta ratsa amman Sulaiman har yanzu babu labarin shi.

Wuraren 11 ya shigo gidan da dukkan alamu a gajiye yake, tun daga ƙofa ta tsare shi da magana bai saurareta ba yace
"I'm exhausted Sadiya please allow me to rest, sannan idan Sulthana tana gidan nan ki faÉ—a mata na bata zuwa gobe da safe bani son na tashi na sameta a cikin gidan nan"

Da faɗan haka ko sake kallonta baiyi ba ya fice, daɗin haushinta da yake ji na cewa da akayi za'a aura ma ƙanin shi ita, indai yana raye ba zai taɓa bari hakan ya faru ba, da yaa aure Saudat zai fara niman hanyar da zai raba wancan haɗin don samm bata dace da ƙanin shi ba.

**********
Ruma ce zaune a gefen Zayyad dake kwance a gado unconcious an saka mishi drip, fuskarta a kumbure wanda ke nuna irin kukan da ta sha,
Shigowa aunty Amarya tayi bayan ta sallami sauran mutanen da suka cike É—akin da suje É—akunan su su kwanta itama fuskar nata ya hau suntum.

"Rumaisa" ta kira sunanta cikin dakewa,
Juyowa Ruma tayi tare da amsawa aunty taci gaba da cewa
"Kada naji abinda ya faru a wani waje, bani son kowa ya san abinda ya sami Zayyad musamman Saudat da duk wani nata, nasan yanda kuke ƙawance kece kawai kika san da abinda ke tsakanin su so don't tell her he is sick"

"Amman aunty me yasa?" Ta faÉ—a tana shirin ci gaba da kuka

"Bani da wani dalili just do as you are told ok?"

"Ok" ta amsa hawaye na bin kuncinta na tausayin Zayyad da Saudat ɗin, tun yanzu ta fahimci raba su ake son ayi da ƙarfi.

****
Washegarin ranar Fa'iza ta rubuta letter ta tura ma Saudat makaranta a kan halin da Zayyad yake ciki, delay ɗin kwana ɗaya aka samu kafin saƙon ya isa gareta, lokacin da ta buɗe ta karanta abinda ke ciki kuka ta dinga yi wanda har itama ya sauƙar mata da zazzabi mai zafi ta bar cin abinci kullum idan ta zauna bata da aiki sai na kuka abin har ya fara damun staff da masu kula dasu, cikin Sa'a sun gama waec kuma ba'a sa sallamar su harsai sun kammala neco amman saboda akwai ɗan tazara a tsakanin su sai makarantar ta bada dama ta dawo gida tayi jinya.

Zayyad kuwa tunda ya farfaɗo ya daina kula kowa bayi yarda yayi magana da kowa a gidan ciki kuwa harda mahaifanshi, idan aka zauna aka matsa mishi da tambaya kuma sai ya juya ya baka baya har sai ka gaji da zama ka tashi ka tafi, ko sannu akayi masa bayi amsawa ya dawo kurman dole bayi uhmm bayi uhm_uhm. Kullum aunty ne mai kwana tare dashi bata yarda wani ya zauna a wurinsa kada somehow a warware abinda suka ƙulla,
Ko wani dare sai ta kawo mishi maganar yayi haƙuri ya cire Saudat a ranshi sai ya juya mata baya yana zuban hawaye wani lokaci har bacci ya ɗauke shi a haka, wayan shi kanma bai san a duniyar da ya jefar dashi ba, wanda Saudat tana ta faman kira switch off, gashi Yusrah ta hana ta zuwa gidan ta ganshi saboda a yanzu kaman surkuwar gidan take, kuma shima ba budurwar Zayyad ɗin ba na yayanshi.

********
02:07am

A hankali ya buÉ—e idanunshi da sukayi mishi nauyi yana kallon ceiling É—in É—akin da yake ciki, bedroom É—inshi ne ba tantama motsin mutum da yaji a gefen shi ne ya saka shi juyawa ya hangi aunty a saman darduma tana Sallah kaman kullum.

Daddafawa yayi ya tashi ya zauna ya jira har ta idar sannan yace mata zaisha ruwa, jikinta na rawa ta zubo mishi a glass cup ta kawo mishi, hannun shi na hagu ta dunƙule cikin nata biyu tare da ƙura masa idanu yayin da yake shan ruwan shima idanun shi yana kanta, he can see tana cikin damuwa.

Rabi yasha ya miƙa mata cup ɗin ta karɓa ta ajiye, sannan yace
"Aunty dare ya raba tuntuni me yasa baki je kin kwanta ba?"

"You are not fine Zayyad ta ina zan samu kwanciyan hankalin rintsawa?"

"If you care so much about me then why did you do that to me?
Baki tsaya kin saurari bayani na ba kika yanke hukunci? me saudat tayi miki da kika mata irin wannan tsanar? A iya sanina da ita na tsawon shekaru she has been a good girl"

Jinjina kai tayi tace "I'm happy that you finally decided to talk and sort things out.
Ni mahaifiyarka ce Zayyad i know what is best for you, and ban tsani Saudat ba ko kaɗan, idan ban ƙaunaceta da duka zuciyata ba a wurina ta wuce matsayin tsana"

Shiru yayi ya zuba mata ido alaman yana buƙatar ƙarin bayani, taci gaba da cewa

"Tun farkon tasowarka a cikin gidan nan a matsayin mai rauni babu wanda ya nuna maka tsananin ƙauna bayan mu iyayenka kaman Sulaiman.
Yana tare da kai lokacin da kake rarrafe har ka fara tsayuwa kazo ka fara tafiya, lokacin da wannan lalurin ya riske ka ma Sulaiman is always there by your side, a lokacin shima da yarinta sosai a jikin shi amman haka yake taya ni kula da kai, hakan yasa bani da wani addu'ar da ya wuce kada Allah Ya gwada min ranar da kanku zai rabu, ina so ko bayan raina ya zama Sulaiman ne mai kula da kai koda ka kai matakin tsufa kuwa.

Ba sai na tuna maka ba Zayyad kaima kasan adadin sadaukarwar da sulaiman yayi maka masu girma ba zasu ƙirgu ba, me yasa kaima ba zakayi sacrificing wani abu gareshi ba, just once please! Nasan da ciwo sosai amman Sulaiman zaiyi farinciki, he will be happy!"

Sunkuyar da kanshi yayi yana kallon hannun su dake sarƙafe da na juna, he found himself speechless, yana so yayi kaman yanda aunty tace amman yana ji kaman ba zai iyaba
"Da wahala" ya furta cikin raÉ—a.
Chapter 61 · 0% Book details