← Book details Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 73

Sashe 62

Ƙaramar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na sani Zayyad but you have to try! Ka saka ma ranka Allah yayi ba saudat bane matarka ita ɗin kawai ƙaddararka ce wanda aka jefo ta cikin rayuwan ka don a jarraba imanin ka, kayi ƙoƙarin cire ta a zuciyan ka kana addu'a Allah ya musanya maka ita da mafi alkhairi and get back to work soon please too many lives depends on you and keeping yourself busy zai rage maka tunani, kwana biyar kenan kana kwance a ɗakin nan baka bani daman magana da kai ba sai yanzu"

*********

Yau baba ya kirani a kan amincewata kan izinin neman auren na da sulaiman yake yi, na amince ko kuma bana so?
Bayan mun gama magana da baba ne na fito parlour na sami Yusrah tana yiwa Jannat assignment,

Zama nayi a gefenta na rafka uban tagumin da ya jawo hankalin yusran tace
"Saudat ke haka zaki ƙare kenan kullum kina cikin damuwa, daga kuka sai tagumi?"

"Uhmm aunty Yusrah ba dole ba, ban tsallake matsala ta farko ba na sake faÉ—awa wani, kinga har yanzu ban samu munyi magana da hamma zayd ba gashi baba ya kira ni a kan maganar kwanaki.
Tun ranar da mukayi magana dashi a school yace zaiyi handling komai har yanzu bai bani feed back ba"

Sauƙe ajiyan zuciya Yusrah tayi tace
"Zan shawarce ki da ki haƙura da batun Zayyad ɗinnan Saudat"

Wani banbaraƙwai naji kalaman nata don basu bada ma'ana ba cikin kwakwalwata ma ni za'a cewa na haƙura da Zayyad ? "Huh... Me yasa zakice haka aunty Yusrah? Ba kece kike faɗa min nabi abinda zuciyana yake so ba? and that's Zayyad!"

"Saudat ki fahimce ni, banyi niyyan ɓoye miki komai ba wallahi amman a cikin yanayin da kika dawo gida bani son sake ɗaga miki hankali shiyasa na bari har sai jikinki yayi kyau na faɗa miki.
Abban Jannat yayi magana da baba kwanaki, kuma shi da bakin sa ya shaida masa cewa Zayyad ya haƙura da auren ki ya janye, yanzu ra'ayin ki da ake son ji kawai a kan boss Sulaiman ne, ko kin amince zaki aure shi idan kuma kinƙi shikkenan sai a bashi haƙuri ke kuma ki jira har zuwa lokacin da Allah zai kawo miki wani mijin ki aura"

Bansan lokacin da hawaye suka gangaro min ba, hannuna na rawa na nuna kirjina tare da faɗin "nice Zayyad yace ya haƙura da ni?.... Ko shine dalilin da yasa ya kashe min waya? Idan na kira ƙannen shi su haɗa ni dashi sai yaƙi magana dani! At least i deserve an explanation, me yasa zaimin haka?"

"Ban sani ba Saudat, kawai kiyi haƙuri Allah zaiyi miki sakayya"

Murmushi mai ciwo nayi nace "hmm daÉ—in abin ba rasa mijin aure nayi ba harda Zayyad dai tozarta ni haka"

Wayana dake ringing na É—ago na duba cikin Sa'a naga matar ya Aminu ce, dukda nasan ta kira ni ne saboda wani dalili daban bayan nayi picking ban tsaya sauraronta ba nace
"Aunty ki cewa Innata ta faɗa ma baba na amince zan auri hamma Sulaiman.............🧚🏼‍♀️

_I tried my best to make this chapter quite emotional 😧 i hope team Zayyad's heart drop a bit😢😩_
😂😂😂😂🤪

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

48🧝🏻‍♀️
08:36am
Ruma ce zaune a main parlour cikin shirinta na zuwa makaranta, atamfa ce red a jikinta ɗinkin riga da skirt ta ɗan yafa madaidaiciyar gyalenta a kafaɗa da wayanta a hannu tana dannawa, tana zaman jiran Zayyad da yayi mata alƙawarin zai sauƙeta a makaranta ya gama shiryawa ya fito.

Knocking ƙofa akayi ta ɗago tana kallon wurin tare da faɗin "come in" da ɗan ƙarfi, a take aka buɗe ƙofar kai gadi ya bayyana a tsaye cikin uniform ɗinshi na aiki hannun shi ɗauke da farin envelope.
Miƙewa Ruma tayi ta ƙarasa wurinda yake tsaye suka gaisa sannan take tambayar takardan hannun shi na menene.
"Saƙo ne aka kawo ma oga Zayyad" ya faɗa tare da miƙa mata tasa hannu ta karɓa sannan tayi mishi godiya ya tafi.

Jujjuya envelope ɗin tayi tana nazari wannan dai baiyi kama da wani official letter ba saboda babu tambarin wani Company ko industry a jiki, tukunna ma yanzu ana turo saƙon takarda ne? Idan mail ne ta email ɗinshi ya kamata a turo idan kuma message ne sai a turo mishi ta waya.
Curiosity ba zai barta ta kai ba tare da tasan abinda ke ciki ba tayuyu ma blackmailing É—inshi ake son yi, hakan yasa kawai ta bude envelope É—in ta zaro takardan ciki ta warware shi ta fara karantawa kamar haka.

```Assalamu alaikum```
```morning greetings to someone i once called mine. I'm sorry for disturbing you once again, ba zan iya daurewa bani na jure rabuwa irin haka ba tare da munyi kyakkyawan sallama ba. Bansan me ya shiga tsakanin mu har ya maida alaƙar dake tsakanin mu ya zamo haka ba, amman koma me yasa nasan tsarin Allah ne kuma hakan shine daidai.```
```well daman na dawo gida ne da na samu labarin cewa baka da lafiya, i was really worried amman an faɗa min yanzu jikin da sauƙi, so alhamdulillah yanzu zan koma naci gaba da karatuna wataƙil kuma wannan ne karo na ƙarshe that i will look at you with affection, I'm getting married now Zayd! wish me luck```
Your's sincerely
Saudat Habib.

Jikin Ruma na rawa ta naÉ—e takardan cikin hanzari ta nufi corridorn da zai kaita É—akin Zayyad batayi nisa ba ta jiyo muryar aunty Amarya a bayanta tana kiran sunan ta,
Dakatawa tayi tare da juyowa riƙe da takardan a hannun ta,
"Meye wannan? And why are you in a rush?" Aunty ta tambaya lokacin da ta saka hannu ta amshi takardan ba tare da wani tunani ba ta buÉ—e don ganin abinda ke ciki.
Ruma dai tana tsaye duk ta gama daburcewa ta kasa cewa komai har saida ta auntyn gama karantawa, ranta a ɓace ta ɗago tana kallon ta
"Duk kashedin da nayi miki saida kika faÉ—a ma Saudat Zayyad yayi rashin lafiya! Kalli Abinda kika jawo, da yanzu takardan ya isa wurin shi mai kike tunanin zai faru?"

Jikinta yana rawa tace "aunty wallahi bani bace, Fa'iza ne tayi mata letter ta tura mata school kuma na faÉ—a mata kin hana"

Jinjina kai tayi tace "i will deal with her, kuma kada ki kuskura ki faɗa masa komai akai kinji ko?" Gyaɗa kai Ruma tayi tace "ɓace min da gani"
Juyawan da zatayi suka hango Zayyad ɗin tsaye a ƙofar ɗakin yana kallon su.

Jikin su duka mutuwa yayi, shikuwa ganin haka yasa ya ƙaraso bai ko kai idon shi kan takardan ba yayi ma aunty sallama kan zai wuce office ya bama Rumaisa briefcase ɗinshi ta riƙe suka fita.

***
Driving yake yi da hannu É—aya É—ayan kuma ya É—aura elbown shi a jikin window ya dafe kanshi dashi, rabin kallo ma kaÉ—ai ya isa ya ganar da kai yana cikin damuwa.
Kallon shi Ruma tayi tace "Ya Zayd ba zaka tambayi lettern nan daga wurin wa yazo ba?"
Shiru yayi kaman bai jita ba yaci gaba da driving É—inshi, tace "daga wurin Saudat ne"
GyaÉ—a kai kawai yayi tare da shan kwana suka hau kan wani titin da tsirarun abun hawa ne suke bi don yayi bayan gari da yawa.

Ci gaba tayi da cewa "ba zaka so ka san abinda ke ciki ba?"

Girgiza mata kai kawai yayi, ta ƙura ma fuskar shi idanu tana karanta expression ɗinshi, he is hurt deep inside amman an tilasta mishi ɓoyewa.
"Amman kasan da taji baka da lafiya ta bar makaranta ta dawo gida saboda kai?"

Saurin juyowa yayi ya kalleta cike da mamaki don shi ko labari baiji ba,
"Yes itama tayi rashin lafiya sosai a lokacin aunty ne ta hana mu faÉ—a maka, but i cannot hold it any longer"
Tana jin sautin songon numfashin da yaja haryanzu dai bece komai ba.
"Sannan a cikin takardan ta rubutu cewa...." Sai kuma tayi shiru tana kallon shi don tasan abinda zata faÉ—a mishi yanzu zai iya tarwatsa mishi zuciya
"Cewa zatayi aure" ta ƙarasa murya can ƙasa kaman mai raɗa.

Bata rufe bakinta ba hawaye mai ɗaci ya gangaro da gudu daga idanun shi ɗaya ɗayan kuma na bushe ƙarau, irin wannan kukan ne mai cin zuciya, a cikinta babu wani sauti.

"Don't hold it in ya Zayd zai cutar da kai, cry out loud if that's what's going to make ur heart ease all the pressure"

Parkin yayi a gefen hanya ya kifa kanshi a cikin tafin hannun shi yana kuka jikin shi sai wani irin shaking yake yi, sunfi 20 minutes suna tsaye a wurin kanshi a kife yana zubar da hawaye masu tarin yawa. Patting É—inshi a baya Ruma ta farayi tana rarrashinsa da kalamai masu kwantar da hankali ganin kukan ya fara yawan da zai iya saka mishi ciwon kai, saida ya nitsar da kanshi kafin suka É—auki hanya

**********

Sulaiman na samun labarin an bashi dama babu ɓata lokaci ya sake ɗaga su dady a Ranar suka kai goro da sadaki aka saka aure sati biyar lokacin Saudat ta gama neco da sati guda kenan, lokacin da ake can ana tattaunawa shi kuma ya saka ta haɗa kayanta a kan cewa yau da kanshi zai maidata makaranta don su samu daman zantawa.

****

Saida Zayyad ya ajiye Rumaisa a school kafin ya É—au hanyar office.
Da shigan shi yasha mamakin ganin table ɗinshi almost empty, yayi tunanin fashin kwanakin da yayi zai dawo ya samu files sun cika table ɗin har suna zuba saboda yawa amman Sulaiman duk yasa an tattara su don dama da mugunta yake tara masa aiki, file guda biyu ne kacal wanda suke zaman jiran shi su ɗinma don tilas shi ake buƙatar ya duba ya saka hannu ne amman da ba zai samu wani aiki ba idan yazo.
Chapter 62 · 0% Book details