Sashe 8
Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe 2 na rana yasoma shiga cikin garin Jigawa a daidai lokacin Alh namatazu mai jirage ke gaban na’urar computer yana kallon Barr Barraq da yanda yake tukinshi dariya yayi sosai yace”is time lokacin ka yayi Yaro”. Yana cikin tuki yaji karan waya dauka yayi da hannu daya yaji Muzzamil ne yace “kana ina,u know I need yhu ko” murmushi yayi yace “albishirinka gamani masoma shigowa Jigawa… Jin motan dayake tukawa yawani karkace akan titi tayan baya suka fita, take motan yafarayin cikin daji da gudun bala’i birkin dayake takawa ma yaki aiki kum! Motar da bugu dawani dutse Wanda hakan yasa kanshi ya buge glass din gaban motan eyeglasses dinshi suka fita daga idonshi.
Motan yaji yakara komawa baya sanan yayo gaba yacigaba da kutsawa cikin daji motan na bubbuge bishiyoyi wanda hakan yasa ya bugu sosai, tsayawa motar tayi chak sanan tayoyin gaban suka fashe tareda sakin Kara mai karfi “tusss” karan dayasa Rufaida data debo ruwa daga rafi tana tafiya ita kadai a hanya ta saki ihu harda barar da ruwan kanta tulun ya fashe. Tace “na shiga uku bomb”, hango hayaki na tashi tayi daga Chan gaba bata ganin abunda ke hayakin saboda bishiyoyin dasuka kare ahankali take tafiya kaman wani abu na fizgan ta zuwa wurin datake hango hayakin.
Farfadowa yayi daga gajeruwar suman dayayi sakamakon buguwan dayayi,ahankali yake laluben eyeglass dinshi baiji alamun suba, hakan yasa yafara tattaba gefenshi dan gano inda zai danna kofar motan ya bude saboda warin petir dayaji alamun tank yafashe hakan zaisa motan takama da wuta any moment, amma yakasa gano wurin, tari yafara sosai yana bubbuga glass din gefen motan da hannu ya daura kanshi kan glass din,ahankali bakinshi ya furta “ataimakamin, somebody help me” Karasowa wurin Rufaida tayi ta tsaya gaban motan dataga yana hayaki,gashi abu kaman ruwa na zuba takasa, juyawa tayi zata koma saikuma taji kaman ana magana,Kara matsowa jikin motan tayi ta daura kanta a jikin glass din motar ta Kara hannayenta ta gefen fuskanta dan ta hango abunda ke cikin motar, da gudu ta matsa baya tana zare ido, dafe kirjinta tayi tace “mai gilashi!” .
Maman Abd Shakur😘
mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 14 to 16KAINE SIRRI NA 21 to 24 →
KAINE SIRRI NA 17 to 20
Posted on May 2, 2016 by mamanshakur
[5/2, 7:44 AM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌
17
Jikinta na rawa,kirjinta na bugawa da karfi saboda tsoro, juyawa tayi tafara tafiya da sauri duk ta rude tace “wlh ni banda kudin ka,banda kudin dazan biyaka”.
Barr Barraq ya lumshe ido, dan gabaki daya kanshi juyawa yake, jiri yakeji sosai,da kyar yadaga kanshi daga jikin glass din motar ya maida akan kujera.
ahankali yake kukkulle ido harya rufesu ruf.
Kaman ance takara waigowa,tanako waigawa taga hayakin dake tashi daga motar yafi nada ma, girgiza kanta tayi hawaye yadan zubo ahankali ta furta ” wlh bazan iyaba,baida lpy ai,naga jini a goshinshi” da gudu ta fanfala zuwa wurin motar, hannu tasa ta rike mabudar motar taja, sai taga motar yabude, ta tsugunna agaban motar tana kuka tace “kafito mubar nan, motarka na hayaki” sai taga ko motsi baiyiba, hanunta na rawa takai kan cinyarshi tadan girgiza shi tace “kaji, katashi motar ka na hayaki”,Ganin ko motsi batayi yasa tafashe da kuka tana kallon fukarshi,cikin kuka tace “mutuwa kayi?” Kara sautin kukan tayi tana girgiza kai “dan Allah karka mutu, kanada kirki kaji dan Allah”.
Goge Hawayen ta tayi ta kalli gabas,kudu,yamma da arewa kozata ga wani mahalukin dazai tayata fito dashi daga motar, amma bataga ko mutum daya ba, dayake kusan duka yan kauyen da safe suke zuwa rafi diban ruwa,basu zuwa da rana. Kifa kanta tayi akan cinyarshi takara kecewa da sabon kuka,kaman wacce aka tsikara ta tashi da gudu ta fanfala zuwa inda tulun ruwanta yafashe kozata samu ruwa a wurin, cikin ikon Allah taga wani dan bangaren tulun da akwai dan Karamin ruwa akanshi tsugunna wa tayi ta dauka ahankali ta juyo tana tafiya, koda tafito fili saitaga tsabagen hayaki bama ta ganin motar da kyau,hayakin yariga ya rufe motar, sauri takara batai wata wata ba ta shige cikin hayakin ta tsugunna tana laluban bakinshi da hannunta, taba lips dinshi yasa tagane bakinshi ne, tashi tsaye tayi da ruwan ta daga hannunta dake dauke da ruwan ta Kara ajikin lips dinshi tace “kasha dan Allah”,ta juye akan lips dinshi kadan ya shiga bakinshi sauran ruwan ya zuba a kirjinshi hakan yasa yaji sanyi ya saki numfashi tareda bude idonshi kadan “ahhhhhh” kokarin lumshe idonshi yake yasa ta kama fuskarshi da hanunta biyu ta girgiza shi “katashi dan Allah, kaji katashi motar na hayaki, mufita daga ciki”, bude idonshi yay da kyau saidai kash baya iya ganin mai wanan zazzakar muryar,gashi kanshi na masifar juyawa saboda buge kan dayayi sosai, ganin yanda ya tsareta da ido yasa tace “kaji” Hawaye ya gangaro daga idonta ta daura hannayenta akan nashi tace “ga hannuna ka rike mufita”kasa kama hannunta yayi kawai saita cire tsoro takama nashi tace “yauwa to tashi” taja hanunshi, da kyar ya iya tattaro karfinshi ya damke hanunta da karfi yatshi yafito daga motar. yakara rike hannayenta gam tana tafiya da baya da baya shikuma yana binta ahankali kanshi na juyawa jiri na dibarshi sosai.
Sunyi kusan taku ashirin(20) yana layi, adaidai lokacin motar ta kama da wuta, tsabagen tsoro ganin motar yakama da wuta yasa Rufaida tafara sauri tana janshi da sauri,mugun tuntube taci da dutse, dayake dabaya take tafiya tafadi akasa timm, batare dayasan maiya afkuba shima yaci tuntube da dutsen ya fada kanta dan ba ganin gabanshi yakeba.
Ihu tasaki da karfi” wayyo Allah na,ka dagani”.
Maman Abd Shakur😘
[5/2, 8:22 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌
18
Hadadden Hall ne cike da jama’a kowa yaci gayu,kida kawai kateshi kana ganin fuskokin mutanen wurin kasan suna cike da farin ciki banda mutane biyu, Muzzamil dayasha blue shadda ta bugu sai sheki take da Matar dazai aura Beeba. kwata kwata natsuwarshi baya tareda shi karkada kafa yake yana kallon agogon hanunshi. kakkyawan amaryan shi dake gefenshi itama cikin damuwa ta matso da bakinta saitin kunenshi tace “Honey wai har yanzu Uncle B bai isoba? gashifa 4 yayi” cike da damuwa Muzzamil yace “wlh nima ban saniba baby” tace ” to kodai wasa yakema sai gobe zaizo?”
Muzzamil ya girgiza kai”abu daya dana Sani game da abokina shine baya karya,baitaba karyaba, tunda yace yataso yataso dinne” amaryan tace”ok,Allah kawoshi lpy to” Muzzamil ya mike tsaye yace “baby bari naje nakira Dad just na sanar dashi”.
Zagawa bayan Hall din yayi inda ba kida sosai yaciro wayarshi yay dailing number Daddy Barraq, ringing daya Dad ya dauka,kafin yay magana Muzzamil yace”Daddy na damu wlh har yanzu Barraq bai isoba ” da sauri Dad yarufe newspaper hanunshi yace”Barraq din?,yanzu fa is 4,yaron da tun sassafe yamin salllama yatafi”,Muzzamil yace”Dad inata kiran wayarshi baya shiga,wlh nadamu” Dad yace “don’t worry Muzzamil it might be motarshi tasamu yar matsala a hanya ne, idan yakai har mangariba bai isoba just let me know,mubashi nan da 7’oclock ” Muzzamil ya numfasa yace”to Dad ” ya katse wayan yakoma Hall din badan ranshi yasoba.
*****
Da kyar ya iya Jan jikinshi ahankali ya sauka zuwa gefenta,numfashi ta sauke mai karfi tareda tashi tsaye tana kakkabe jikinta, ganin yana juye juye yasa ta tsayar da kakkabe jikin datakeyi ta kalleshi, kafin ta Ankara taga yafara Kwara amai a kwance ya rike cikinshi, warin petir din daya Shaka ya batamai ciki,tsugunnawa tayi a gefenshi a raunane tace “sannu” ya mugun galabaita daga kanshi yayi kawai dan jikinshi yay zafi, dankwalin kanta ta cire ta mikamai tace “gashi ka share rigan ka” hanunshi ya mika yana laluben abunda take bashi, Rufaida ta kalleshi muryanta na rawa sosai tace “baka ganine?” Kanshi yadaga mata ahankali, kuka yaci karfinta tsugunnawa tayi ta share mai aman daya bata gaban riganshi, sai bayan tagama cikin kuka tace “tashi muje gidanmu nabaka nabaka magani” da kyar ya iya mikewa yadan cije lebe tareda rike kanshi dayakeji kaman zai cire, sannu tace mishi sanan ta mika hanunta yana rawa tarike mai tafin hannu, wani dan yanayi taji ya ajikinta sanan tace “muje” ahankali yake daga kafa hanunshi daya na rike da kanshi, sundanyi tafiya kadan jin zaifadi yasa yace “sister zan huta” akasan wani bishiyan lema ta taimaka mai ya zauna,itama ta zauna kusa dashi jikinshi yay zafi radau, sanan tace “zaka iya tafiya yanzu?” Ya gyada kai sanan suka mike akalla sun bata kusan awa daya kafin sukai gida saboda suna tafiya yana hutawa,zazzabi sosai yakeji da ciwon kai banawasa ba.
Gidan suka shiga, hamdala tayi tadaga Duduwa bata gida bukkarta ta shigar dashi ta zaunar dashi akasa sanan tace “ina zuwa” fita tayi da gudu takoma tsohon dakin mamarta nada, tsofaffin kayan mamanta da labulaye ta kwaso dayawa ta shigo dakin tasame shi harya kwanta akasa shame-shame ya rike kanshi, shinfidasu tayi akasa ta daura wani akan wani saboda yadanji taushi tazo ta tsugunna agabanshi tadan tabashi ya bude idanunshi dasukai jajir tace “taso ka kwanta akan shimfida”,ta rike mishi hannu, tashi tsaye yayi da taimakon ta yadan kwanta akan shimfidar.
Ta Kara tsugunnawa tace”bari naje nasiyo ma magani kaji,kai bacci dan Allah duk Wanda kaji yay magana karka amsa kaji?ko Duduwa tai sallama karka amsa” Bai amsataba,tai fuskan tausayi tace “in sha Allah zaka warke kanada kirki” ta tashi da sauri tadau yar karaman jakan buhu taciro naira Darin da Baba yabata tafita daga dakin da gudu.
Maman Abd Shakur😘
[5/2, 8:37 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌