← Book details Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 43

Sashe 11

Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Magananta yaji tace”kaga idan ka mike hanyar nan sambal zata kaika har titi saika shiga mota ka koma gida”,tasa sanda a hanunshi tace “kadinga duba hanya da sandar nan,kayakuri katafi banason ka shiga matsala saboda ni? tunda aka gammu tare sai an daureni an jefeni, katafi kaji insha Allah babu abunda zai sameka,nagode sosai da abunda kamin a rayuwa,Duduwa yau saita kasheni hala, sai anjima” da sauri yace “Rufaida, Rufaida” amma ta falfala da gudu. Ahankali yace”to mena mata arayuwa datakemin godiya?anyway koma wacece ke Alkawari daya zan miki saina fitar dake daga kangin nan dakike ciki” yajuya yana dogara sandar yana tafiya.

Dad polisawa da Muzzamil tsaye agaban motar Barraq daya Kone. Muzzamil yace” Dad jiya tunda nazo bakin titin nan naga tayoyi biyu Dana duba naga tayan motar B ne,hakan yasa na dinga tracing tire tracks cikin Daren nan harnazo nan, and d worse part naga karfen glass dinshi a motar, kenan duk inda yake baya gani baya tareda glass dinshi. Dad kataho da sapayan eyeglass din dana fadama yauda safe?” Dad ya dafa kan Muzzamil yace”eh,son naji,yanzu nida inspectors zamu shiga cikin kauyen nemanshi,kawuce katafi 11 za’ayi daurin auren ka gashi yanzu 10:30″ Muzzamil yace “Dad… Dad ya girgiza kai banason musu just go,today is a special day 4 yhu” yajuya badan ranshi Yasoba kwalla yataru a idonshi yafara tafiya dan karasawa bakin titi ya shiga motarshi daya paka a wurin. Yayinda Dad da yansanda suka shiga cikin mota suka wuce cikin kauyen.

Shiga motarshi yayi ya kifa kanshi a kujera kaman yafashe da kuka haka yakeji, gajeren hawaye daya zubo yadan goge sanan ya Danna key zai tada motar ya dago kanshi yana kallon titi. hango Barr Barraq yayi a tsakiyar titi yana dogara sanda ga motoci sun taho da gudunsu dayake express road ce, da gudu yafito daga motarshi ya fanfala da gudu ya bude muryarshi yace “B stay still,just stay where u are,am coming” yama motocin dasukai layi alamun su wuce duk suka wuce sanan ya shiga cikin titin,kamo hannun Barraq yayi suka tsallako sanan yama Barraq dake fadin Muzzamil kaine muryan ka naji, kakkyawan runguma Muzzamil yabashi tareda fadin is Me,I missed yhu B”.

Maman Abd Shakur😘
[5/4, 9:06 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

23
Suka kankame juna daga baya Muzzamil ya sakeshi yace “bari nakira Dad” ba’afi minti 20 da fadama Dad ba suka zo wurin shida polisawa,Dad yazo inda suke tsaye ya rungume Barraq tareda fadin”Alhamdulillah, Alhamdulillah,my little champion is safe and sound ” Barraq yay murmushi da kyar ya iya furta “Dad am hungry, yunwa nakeji sosai wlh”Dad yace” muje kaci abinci” yajuyo ya sallami poliswan tareda basu kudi mai yawa ya dawo ya shiga motar Muzzamil yajasu sai cikin garin Jigawa state,anguwar GRA suka sauke Dad suka fara saukewa a wajen daurin Auren,Muzzamil yace “Dad musai munje mun shirya zamu zo,nasanma Kawu yariga ya karbi auren”
Dad yace “ok nidazaran angama daurin auren zan tafi inada meeting” yabude jakar dake hanunshi yaciro wani dan karamin akwati yasama Barraq a hannu yace “your eyeglasses son,take good care of yourself” Dad din Muzzamil yakaraso wurin yanamishi magana yayinda Muzzamil yaja motar da sauri dan yasan fada Dad zaimai suka tafi hotel dinsu.

Dakin Muzzamil suka shiga, sai alokacin yabude akwatin yaciro glass din yasa, ahankali ya furta “Alhamdulillah” Muzzamil dake gefenshi yay murmushi yace”Ala kulli hal”zama Barraq yay akan gado, tashi yayi yace “Men yimin order din abinci,bari nai wanka” yawuce bathroom.

Fitowa yayi daure da towel daure a kwankwaso sai aranan nakare mai kallo,namiji ne kakkaura,fari tass yake jajjir kana ganinshi kasan yahada jini da turawa,yanada yawan gashi ajiki, ga gashin kanshi mai yawa baki sidik,lips dinshi Jane sosai idonunshi manya ne,amma kwayar idon wani irin blue ne, yanada tsayi jikinshi a mummurde.
Zama yayi yadau coffee dake gefen abincin da aka kawo mishi ya shanye tass sanan ya dauko Basmatic rice da aka dafadashi da cactus da green beans, yadanci badayawa ba sanan ya tura gefe Muzzamil yafito daure da towel shima Barraq kalleshi yace”ina kayan dazan sa?” Muzzamil yabude wardrobe ya dauko mai shadda fara iri daya datashi ya bashi Barraq ya kallai yace but… Muzzamil da sauri yatareshi yace”I know nasani,B bayason manyan kaya but kasamana just 4 today kaji” Barr Barraq yay murmushi ya tashi yasa kayan sunmai mugun kyau. Karfe 12:30 suka gama shiryawa,Muzzamil yace” B munyi mugun latti,maybe ma anriga ankai baby na,cos I arrange everything dazaran an daura aure za’a tafi da ita saboda cocktail night dazamuyi a Abj by 8 nadare” yadanyi murmushi “but lemmi call just to confirm”. Yakira Yusuf ya dauka yace”ango hope anga B?mu gamunan a hanya zamu wuce da amarya Abuja” Muzzamil yace”thanks Yusuf, gashinan tareda ni, muma yanzu zamu zamu taho muhadu later just handle everything”, sukai sallama da Yusuf ya katse wayan.

Yan kayayyakinshi na hotel din ya tattara yakai car,sanan yay settling bill yadawo daki yasamu Barraq zaune kan kujera ya lumshe idanu. dafashi dayaji anyi yasa ya bude ido yana kallon Muzzamil, Muzzamil yace”meke damunka,why all d sudden thinking?Tundazu na lura da hakan?”
Lumshe ido yayi ya bude sanan yatashi yajuya ma Muzammil baya ahankali yace “Muzammil kwana daya kacal nayi tareda ita,bansan taba bansan kamanintaba,but all I can tell u is,am in luv with Rufaida, ina sonta,nd is time to save d luv of my life” yana karasa fadin hakan yay sauri yabude kofa yafita,Muzammil ya mike tsaye cikeda mamakin abokin nashi Barraq in luv? Ahankali yace”abun mamaki” da sauri yabishi yatarar dashi a zaune a mota kanshi nakan kujera ya lumshe ido Muzammil ya zagayo ya zauna a mazaunin direba ya kunna motan sanan yakalli Barraq yace “ina mukayi B?” Barr Barraq ya kalli Muzzamil da dan gajeren murmushi yace”kauyen daka daukoni shinake so ka kaini,idan muna kan hanya I will tell yhu everything about her life” sanan yay sauri ya juyar da kanshi ganin Muzzamil na neman mishi dariya. Ya kadakai kawai yatada mota aranshi yace Barraq in luv,hmm wot a surprise!.

Maman Abd Shakur😘
[5/4, 9:24 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

24
Ganin boyewan datayi akan bishiya bashi zaisa yau afasa jefeta ba yasa ta sauko daga kan bishiyar mangoron tana kuka na fitan hankali da tulunta a hannu, tafiya take kowa na kauyen ana nunata ana cewa “ga wacce za’a jefe a kofar gidan mai gari anjima,ankamata da namiji suna lalata,namijin ma bature fa” ko kallon mazan da suke magana batayi ba saidai ma takara fashewa da kuka tawuce gida shiga gidan tayi da sallaman ta takarasa tsakar gida ganin Duduwa dawasu kattan maza su uku,Duduwa na zaune akasa suko suna tsaye bakake dasu hakan yasa tasaki tulun akasa,batasan lokacin da wani zazzafan fitsari ya tsiyayo yabi cinyar ta zuwa kasa ba.

Duduwa ta taso tazo gabanta tace “aikuwa gaskiyar su laminde,gako rigar maza nan ajikin ta, wlh yau saikin kusa mutuwa saboda azaba Rufaida” taja hanunta Rufaida tafara tittirjewa tana ihu dan “Allah Duduwa karki kaini gurinsu, mezasu min?” tana ihu haka Duduwa tadinga janta akasa ta kukkuje,Duduwa ta jefata tsakiyar mazan tace”Mujittafa gatanan ka daketa,kaimata bulala dari, kadaki bashin gyadar ka data batar, sanan kushiga daki dukanku kuyi duk abunda kukaga dama da ita,dama ai tadawo karuwa inkunga damama dukanku Ku ukun Ku afka mata a lokaci daya ba matsala ta bace”. Mujittafa yasa hannu yadaga Rufaida tsaye dake kuka sosai yana karemata kallo sama da kasa da wararran bakin nan nashi da ba hakoran gaba yace”ahh Duduwa ai wlh bama saina daketa ba,kawai afka mata kadai idan nayi nabar miki bashin gyadar ” Duduwa da sauri ta mike kaman mahaukaciya tace”ninace kuyi mata bulala dari,maza takebi” da sauri ta shiga daki taciro sharbebiyan dorunar ta mai baki 4 da wayan wuta tahadesu ta nannade tana mikama Mujittafa tace “gashi kacimin ubanta yanda bazata Kara neman mazaba” Rufaida tafasa ihu ta kankame jikinta tana kuka.
Mujittafa yace”haba Duduwa saikace ba jikarki ba zakice azaneta da wanan doruna haka”Duduwa ta nuna kirjinta” Ni Ni nace kadaketa da ita,kuma Rufaida ba jikata bace ban hada jini da itaba,yar tsuntuwace, asiri nake rufamata danama bari ta zauna Dani ina bata abinci,Ku cimin ubanta kuma kasheta Ni banda asara, kumata bulala dari sanan Ku wurgata bukka Ku afakama bunsurar” Mujittafa yakara washe jajayen hakoran yace “kwantar da hankalin ki Duduwa dole mu ladaptar da shegiyar da duka,sanan dukanku mu afka mata mu yagata,yanda bazata Kara marmarin bin mazaba”, Duduwa takara gyara daurin zani tace “yauwa haka nakeso” ta nuna sauran mazan tace “Ku dagata kujumai ita yamata dari abaya”.

Rufaida na ihu, kururuwa, kuka,shesheka, haka suka dauketa, daya ya rike hannuwanta dayan kuma kafafunta suka juyata, Duduwa tasama Mujittafa dorinar a hannu tace “yauwa cimin ubanta”. Mujittafa iya karfinshi ya zaula mata daya abaya, ihu Rufaida tasaki tawani bankare kaman zata fadi akasa saboda azaba, Duduwa tace” kuriketa da kyau yar yarinyar nan tafi karfin kune?,kaikuma Mujittafa haka ake dukan mazinaciya budurwa yimata da karfi”. Mujittafa yakara daddagewa yakara zubama Rufaida abaya Wanda saida rigan Barr Barraq ya barke ta baya, masu karatu Ni kaina kasa daurewa nayi nafito daga gidan dan duba wai har yanzu su Barraq basu isobane???.
Chapter 11 · 0% Book details