← Book details Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 43

Sashe 28

Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 60 to 62*KAINE SIRRI NA 65$66 →
KAINE SIRRI NA 63$64
Posted on June 26, 2016 by mamanshakur
[6/26, 11:19] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

63

Nana na hango mai gadi tafada kanshi tana jijjigashi,atorace mai gadi yace “hajiya lpy? Wani laifin namiki yau? ” Nana ta girgiza kai “kodai Kai shiru muje daki kona koreka daga aikin ka”. Da sauri mai gadi yatashi Nana tabi bayanshi tana tafiya aduke, suna shiga tafada jikin mai gadi batare data damu da mugun warin dayake ba, mai gadi yasamu abunda yake nema, yau zai dandana matar birni, hakanan suka fada duniyar nikuma nafito daga dakin. Muzzammil ya dafa kafadarshi “B karka bari maganan Nana ya tsayama arai,trust me Nana bazata iyama komiba sai abunda Allah ya kaddara zai sameka”. ahankali Barraq yace” hakane”Kafin ya Mike suka fito daga warehouse din suna hira kowanne ya shiga motarshi suka tafi. Abakin wani babban super market ya tsaya yasai musu chocolate dayawa different type, da icecream yabiya yafito ya shiga mota. Ganin ana kiran sallan laasar yasa ya tsaya yay sallan sanan yatafi. Parking yay bayan ya gaisa damai gadinsu ya wuce ciki. Hango Auta dayayi a dining sai nadan abinci take tana hangoshi ta taho da gudu tanamai oyoyo yace”me kikeci haka?” Dariya tayi kafin tace “Anty rufaida ce tamin cookies, saikuma tadafamin friedrice mai dadi ,Uncle B harda kidney aciki wlh” tanamai magana Amma hankalinshi baya kanta kallon fallon yake bai hango Rufaida ba, zaiyi magana kenan yaji sassanyar muryar Rufaida mai ratsa jikinshi tace “Auta I need help with dis zip,kizo” da karfi Auta tace”to Anty” tasaki uncle B zata tafi,da sauri uncle B ya riketa” ba abinci kikeci ba?”Auta ta girgiza kai,”oya jeki cinye abincinki, I will help her with d zip” Auta tace to batare da tunanin komiba takoma dining, shikuma yahau sama dakin yabude ya shiga batare da yay sallama ya tsaya yana kallonta. batare data juyoba tace “thank God,kinga nakasa zage zip din”murmushi yayi ya ajiye ledan agefen gado yakaraso inda take tsaye yahada zip din zaija, bayanta ya kalla yaga har yanzu tabon dukan nan basu gama bacewa ba,hawaye yacika idonshi, baisan lokacin dayakai hannu ya shafa tabon ba,Rufaida taji sanyi “Auta ur hands are cold,by d way mekike tabamin baya?kija zip din,and take ur hands off dere” ahankali Barraq ya chigaba da shafa tabon yanamai jin tsanan kanshi daya bari akama Rufaida wanan dukan, Rufaida jin Auta taki dena shafawa yasa hawaye ya ciko idonta ahankali tace “are u looking at d bruises?,grandma dita Duduwa tasa aka zaneni” takarasa maganan muryarta na rawa, ahankali taji an rungume ta sosai an matseta “I luv yhu Rufaida, ina sonki, namiki alkawarin babu wanda zaisake miki wanan dukan, I promise” lumshe ido tayi jin muryan mijinta sun dade ahaka kafin ya dagata ya zage mata zip din tajuya da gudu zata fita yariko hanunta yana murmushi yana kallon riga da siket din jikinta mai ruwan sky blue “kinyi kyau” Ta rufe fuskarta tana murmushi, yana rike da hanunta ya dauko ledan chocolate din yasa mata ahannu “ga tsaraban ki”. Ya saketa ahankali tace “thank yhu” tajuya zatabar dakin yace”Baby” tajuyo kanta akasa “am hungry, plz serve me”kunya taji daya cemata plz komawa kasa tayi tahado mai abinci shi a tray takawo mai ta ajiye, yanata kallonta ta zubamai a plate ta mikamai,karba yayi Amma saida yahada da hanunta ya sumbaci hanun sanan ya saki ya dibi abinci yasa abaki lumshe ido yayi kafin yace “hmmm” da sauri Rufaida ta kalleshi yace”delicious, good cook baby na”dadi taji yanda ya yabi abincin,tashi tayi zata fita yace “ina zaki?” Kallon yatsunta tayi kafin tace “sitting room, wajen Auta”. Yadade yana kallonta kafin yace “ok, but just for today,duk randa nakecin abinci nanne wajen zamanki”,yanuna Mata cinyar shi tafita da sauri,harta fita ta tuna da chocolate din tadawo cikin dakin yabita da kallo,hannu tasa tarufe fuskarta tana murmushi tazo kusa da Shi tadau chocolate din takoma baya da gudu ganin yanason kamota tafita daga dakin,daga murya yayi yace”baby na yhu guys should get ready idan nagama ci abinci zamu tafi”. Maman Abd Shakur.😘
[6/26, 13:42] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

64
Chapter 28 · 0% Book details