← Book details Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 43

Sashe 15

Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

31
Girgiza mai kai tayi tana hawaye “kayakuri bazan karaba”, ya tsareta da ido hakan yasa takara birkice wa “kayakuri dan Allah…” Bude kofar dakin da akayi yasa Barr ya juyoda kanshi Mom ce, da sauri takaraso cikin dakin tana ma Barraq kallon tuhuma cikin harshen turenci tace “maikai ma yarinya na?mesa take kuka?” Barraq yay shiru, zama tayi kan gadon kusa da Rufaida dake Kuka ta dafa kanta cikin harshen hausa dabata kware sosai ba tace”daughter na kin tashi?” Rufaida ta daga mata kai jikinta na rawa tana Satan kallon Barraq da yay folding hannu a kirji yana kallonsu, lura da hakan yasa Mum ta juyo da kai ta kalli Barraq tadan ballamai harara tace “wuce katafi tsoranka take” saida ya kalli fuskar Rufaida dashi take kallo da sauri ta dauke kai sanan yay murmushi yajuya yafita daga dakin.
Mum takara matsowa kusa da ita takama habarta tasa hannu tana sharemata hawayen dasuke gangaro wa tana girgiza kai tace”shin a matsayina na uwa ya dace naga yata na kuka na barta taitayi?” Rufaida tai shiru dan ita bata gane yanda take turenci da sauri sauri. Mum takama hannun Rufaida tarike, da gurbatatchen hausarta tace”daga yau ni ne mamarki kinji” Rufaida hawaye ya zubo daga idonta tana kallon Mum, Mum tadan daure fuska tace “banason na Kara ganin hawaye sun zubo daga idonki,oya tashi muje bayi kiyi brush da wanka sai kici abinci ” da taimakon Mum Rufaida ta mike tsaye suka shiga bayi Mum taimata brush tareda wanke mata fuska da kafa da hannu saboda wanka ayanayin da take bazai yuwu ba. Fitowa sukayi Mum ta Danna wani kararrawa wata maid da kayan aiki a jikinta ta shigo da katon akwati ta ajiye a gaban Mum sanan ta koma gefe ta tsaya. Mum ta kalli Rufaida tace “zabi kayan dazaki sa” Rufaida ta kalli kayan kyawun kayan kadai yasa batasan lokacin data saki murmushi ba,Mum tace”zaba mana kina murmushi” da sauri Rufaida ta chusa kai a cinya tanamai jin son Mum a ranta dan saitaga wani abubuwan ta kaman na marigayiya Umman ta.
Mum da kanta ta zabar mata kaya wani pink Daisy gown anmishi ado da fulawowi baki da pink pant ta ajiye gefen Rufaida tace “ga Wanda nazaba miki daughter” yar aikin ta rufe akwatin sanan tabar dakin. da kyar kunya yabar Rufaida tasa kayan Mum tasa aka kawo mata tea mai kauri tasha da indomie da aka dafa mata dan batajin zata iya cin abincin suba.

Dakinshi ya shiga ya zauna kan sofa karan taba yajawo daga aljihun shi ya kunna yahau sha yana lumlumshe ido. Maisa duk in Rufaida na kuka tana mugun bashi sha’awa? Barinma dazu? Inda ace Mum bata shigo ba maybe hala sai yay wani abu stupid, dafa kanshi yayi tareda fadin “ya Allah don’t let me go astray” yacigaba da Shan tabarshi kafin daga bisani ya jawo wayarshi yafara neman number Muzammil Ango.

Maman Abd Shakur😘
[5/12, 8:01 AM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

32
Muzammil ya dauka da sauri ganin number Russia dan yasan bazai wuce Barraq ba,”Hey! I Miss yhu B yaushe zaka dawo ne abeg tunda ka kaita?” Barr yay murmushi tareda fadin”look who is talking, u miss me a ina? Bayan amarya ta mantar dakai ni” Muzammil yace” haba man! Kaima kasan u are constant in my heart,hw far ya jikin Rufaida? ” Barr ya sauke ajiyan zuciya “fine, although Dr yace next week zaizo yabude,ina amaryan?” Muzammil yace “I no dey house o,nabarta agida nazo chemist ne zansai pregnancy test nakai mata ta gwada” yabama Barr kunya sosai yadanyi dariya kafin yace”kai man bayau 3 days dayin auren ba,even though I don’t know much about medical stuff but nasan is impossible ciki ya shiga a 3 days har yabada symptoms” Muzzamil yay dariyan shakiyanci yace”sit-down dere, no go marry and know how d system dey work,sai tsufa kake kaki kayi aure kai sai graduate ko” yay maganan cikin sigan zolaya dan yasan yanzu Barr Rufaida yar yarinya yakeso. Barr yadan Sosa kai tareda yin shiru yana murmushi mai sauti,Muzammil yace”answer me now,Ina ra’ayin naka yaje? Anyway na manta nafada ma jiya naje office dauko wasu files nahadu da Nanan ka, she was crying telling me u are d luv of her life,dis,dat,kagane ai bla-bla-bla. Ta tambayen kana ina I have no any other option but to tell her kana Russia… ” “for God sake Muzammil kadena min maganar Nana, I hate her,I hate her generations,banason anamin maganar ta, banason mace Mara kamun kai, ko narasa macen aure bazan aureta ba”, yadan yi tsaki yace “u just ruin my afternoon, talk later” ya katsa wayan yana huci.

Wacece Nana?
Yar Alhaji Asha jiko Babban abokin Dadin Barraq, Nana tai graduating daga American university of Nigeria (AUN) inda ta karanci English, Ta waye iya wayewa,ga rashin kamun kai,tunda ta daura ido kan Barraq ranan da akai hira dashi a AIT taji tana mutuwar son baturen,yaro jinin turawa,jinin yan Nigeria,ga kudi,ga aji,ga kyau. Cikin ikon Allah tagano Ashe dandan abokin baban tane,tama baban ta magana,yay ma Dadin Barraq magana,da murnan Dad yakira Barraq yamai magana Barraq yace shi bayason ta,inlokaci yayi zai nemi matarshi da kanshi hakanan da sanyin guiwa Daddy yabama Alh hakuri. Tundaga lokacin Nana tahana Barraq sukuni har tsiraicinta tana nuna mishi kawai dan ya sadu da ita, amma hakan yaki faruwa Barraq yakibi takanta duk inda yaganta Koran kare yake mata danya lura inya biye mata wataran zai fadama halaka haryay abinda takeso wanan kenan.

Maman Abd Shakur😘
[5/12, 8:25 AM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

33
Kwanan Rufaida 7 a Russia taji sauki sosai likita yazo yabude ciwon ya warke tass har tabon sun bace tasha kuka saboda zafi,Mum na bata kulawa naban mamaki,wani irin shakuwan d’a da mahaifi ya shiga tsakaninta da Mum,Mum naji da ita,tana kokarin chaba mata yar hausan data iya idan taga taimata magana da turenci bata ganeba. Rufaida najin dadin zama da Mum saboda ta lura Mum nada hankali ga yawan kyauta. tundaga ranan Rufaida bata Kara ganin Barraq ba,hakan yasa hankalin ta ya kwanta batada matsala Mum tariga tabata labarin yanda akayi tadawo Russia,aranan ne ta lumshe ido a zuciyarta takira Mai gilashi da Hakika yakasan ce SHINE SIRRIN TA dan yataima keta daga hannun Duduwa yakawota wurin mamarshi mai kirki mai sonta, Mai gilashi-KAINE SIRRI NA!.

zaune suke ita da Mum a falo,sanye take da Jan doguwan riga a jikinta Gashinta ba dankwali Mum na duba gashin tace”daughter anjima zansa akaiki wurin gyaran gashi cus hair dinki is too dirty” Rufaida tai murmushi tace”to Mummy nagode “suka cigaba da kallon TV dake falon, jin anbude kofa tareda yar karaman sallama ciki ciki yasa Mum batare data juyoba tace” Son yanzu is 11 Am,tun safe kafita jogging maisa kadade?” Karasowa falon yayi ya zauna akan kujeran dake kallon na Mum yadan saci kallon Rufaida wacce tunda taji Mum tace son tarufe ido,dauke kai yayi kafin ya cire headphone din dake kanshi yanadan tabe fuska,Mum tace”bakada lafiya ne akira Dr?” Girgiza kai yayi kafin ya mike tsaye yadau headphone yarike a hannu yana jujjuyawa yadan kalli Mum murya Chan kasa yace”Mummy am hungry, abama wanan breakfast dina takawo min part dina,am going to shower ” yafice daga dakin yana tafiya ahankali tareda rera yar waka.
Mum ta kalli Rufaida tace”Rufaida” ahankali tabude ido ta dago kanta ta kalli Mum tace” naam Mummy ” Mum ta sakan mata murmushi dan har cikin ranta tanajin dadi duk lokacin da Rufaida xata amsata da naam Mummy. Mum tace”kije wajen lidiya(mai musu girki) tana kitchen kice tabaki abincin son ki kaimai dakinshi kinji” Rufaida ta girgiza kai tareda mikewa kaman kwai yafashe mata aciki ta karbo abincin tayi hanyar waje waige-waige take dan batasan dakin ba,hango wani mai kula da fulawowin yasa takarasa wajen ta tambaya ya nuna mata wani hadadden bangaren gidan tayi wajen, tsayawa tayi abakin kofa takasa shiga,takasa kwankwasa wa,takasa magana ta shiru hanun data rike abincin yana rawa.

Mai kula da fulawowin ne yazo watering shukokin wurin ya ganta a tsaye yace”ha’a my lady ai nanne part din my boss,bude kofa ki kaimai abincin kafin ya huce,my boss ya tsani abincin daya huce” yana gama fadin haka yacigaba da aikin daya kawoshi,da kyar tasamu karfin bude kofan ta shiga ta mayar tarufe tana numfashi da sauri. Lumshe ido tayi ta budesu ahankali, kwayoyin idanunta suka sauka akan fuskar mai gilashi dake zaune akan doguwar kujera yana kallonta,da sauri ta juyar da kanta tana kallon wani bangare hawaye na shirin zubo mata.

“Am very much hungry” taji anfada hakan yasa ta juyo da kanta taga ita yake kallo da sauri ta juyar da kai, ta daga kafarta da kyar ta iso gabanshi ta ajiye tray din abincin akan center table din gabanshi kanta na kasa tai shiru, “zubamin Rufaida” taji yakara fada hakan yasa ta mika hannu tadau plate ta bude kullan abincin, hanunta na rawa sosai tadau cokali tafara diban shinkafan duk hanunta na rawa tana zubar da Rabi a table Rabi a plate, bin hanunta da kallo kawai yake zara zaran yatsayen ta na burgeshi gadan karamin Jan abu a duka kunbunan ta dasuka burgeshi(Jan lalle). ganin yanda hanunta da jikinta ke rawa tana zubar da abinci yasa ya mika hanunshi ya rike hanunta dake dauke da cokalin abincin, wani irin rikon hannu yamata, yatsun shi biyu na tsakiya na cikin tafin hanunta ukun yatsayen sun zagaye tsintsiyar hanunta. Idanunshi suna kallon fuskarta dake kallon farin hanunshi daya rike nata,kallon dan zufan dayabi goshinta Wanda hakan yasa dan gashin gaban kan ya kwanta yay lub. jin yaki sakin hanunta yasa tadago kanta ahankali ta kwalalo idonta dake gab da zubar da hawaye ta kalleshi, ita taga yake kallo,Kara kwalalo idon tayi a tsorace hawaye ne ya gangaro daga idonta ya sauka akan kuncinta.

Maman Abd Shakur😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 34 to 37KAINE SIRRI NA 49 →
KAINE SIRRI NA 35 to 48
Posted on May 24, 2016 by mamanshakur
[5/24, 07:58] Fauzee Preety: [5/13, 3:54 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌
Chapter 15 · 0% Book details